
Rahima tace” Watau mu Mata problems din mu yawa ne dasu, haka kawai mace ta daukowa kanta rigimar da zata dameta ta rasa nayi, rayuwar duniya? Kan mazan yanzun ma da basu da tabbas Allah dai ganar damu yai Mana jagoranci.
Zuwaira ta kare abincinta mai rai da lafiya ta zubo suka hadu suka ci banda Rahima da ta kasa cin komi tana kwance, sannan suka tafi bayan sunyi sallar la’asar.
22/09/2020, 18:19 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
52
Bayan tafiyar bakinta ta kwanta ta dafa kanta ta karanto suratul fatiha *7 hade da ayoyin shifaa, nan da nan ta sami saukin ciwon kai da ya dameta, ta juya ta dauki remote ta canza channel din dish tana kallon labarai, nan barc ya dauketa..
Ya shigo ya ganta a haka bai tasheta ba, ya karbi remote din dake hannunta ya rage sautin tv kadan ya fita zuwa sashen Zuwaira.
Ta fada mishi Rahima bata jin dadi, ya gyada Kai ya wuce dubo yara da sukayi barci, ya tofa musu addua ya dawo yai ma Zuwaira saida safe ya koma sashensa, yaci abinci kana yayi wanka ya kimtsa kana ya sake komawa sashenta.
Still bata farka ba, ya zauna shiru yana nazarinta kafin ya mike ya nufi bedroom dinsa ya kwanta.
Can cikin dare ta farka ta ganta bisa settee, a takaice Ya Haseeb bai dawo ba kenan, da ya shigo ba zai barta ta ci gaba da kwanciyar haka ba, can ta shaki kamshin turarensa ta bude ido sosai, this isn’t her imagination lalle ya shigo ya fita abinsa tunda har yanzun fushi yake da ita.
Ita ma ta kai kul saboda bata ga dalilin da zai sa ya dau batun da zafi ba bayan ta riga ta bashi hakuri ta nemi afwar laifinta.
Yes tasan tayi kuskure domin komi kunyarsa da take ji ba zai hanata mishi albishir din rabon da Allah ya basu ba, Wanda idan ba Ubangiji ba wa ya isa yai wannan ikon? Ya tsaga rabon haihuwa tsakaninta da wa da kani?
Fushinta na wofi ne maras tushe tunda ta riga ta amshi Haseeb a matsayin mijin da Allah yai mata zabi, ta amince wani hanin ga Allah baiwa ce meye problem dinta kuma tunda ta dade da tsunduma cikin kogin soyayya mai zurfi da fadi, ta kurbi ruwan kogin da ya kunshi dandanon zuma, gishiri da madaci, tasan dandanon zakin zuman soyayya, ta shaidi gardinta ta hadiye tsaf har da neman kari, wajen dandanon ruwan gishirin ma ta hadiye rabi ta watsar da sauran, ya rage sauran ruwan madacin data guntsa cikin baki yana kokarin shigewa cikin makoshi tana kokarin fiddo shi don ko alama wadannan ruwan ba ruwan sha ne a gareta in dai domin soyayyarta da Haseeb ne.
Tayi ajiyar zuciya, so in har tana so ta amayo wadannan ruwan madaci da suka riga suka gauraye bakinta ya zama dole ta warware problem din dake tsakaninta da mijinta.
Ta tashi ta nufi bedroom dinsa tayi knocking ta tura kofar a hankali.
Kwance yake ringingine ya dora dukkan hannyensa ya dafe goshinsa, dim light din dake dakin bai hana ta ganin yanayin dake yake ciki ba, ta matsa ta zauna gefen da yake kwance, sanyin air condition da kamshin turaren Emotion da qira’ar sheikh Abdurrahman Sudais suka da yake saurare cikin suratul Rahman suka sanya mara wani irin natsuwa cikin ranta.
Bai nuna alamun yaga shigowarta ba ma balle ta tanka, hhmmm tasan halin gogan nata, miskili kafi mahaukaci ban haushi but ko shi ana janyo ra’ayinsa da rarashi da dabara, idan haka dole ita ta ajiye nara miskillancin a gefe… Ta Kira Ya Haseeb can kasa so very softly….
Cikin muryar data sakar mata kasala yace “Lafiya ba kiyi barci ba har yanzun?”
Ta Kara sassauta murya "Abinda ya hanaka barci shi ya hana min.".
Ba tareda ya motsa ba yace “In har akwai problem dake damuna kin sani, so nagode kije ki kwanta.”
Tsawon minti biyar ta rasa yadda zata bullo ya saurareta abu ya faskara saboda bai yi niyya ba..
Ta mike tsam, a zatonsa ficewa zata yi… Zuciya ta kule shi ya rumtse ido, tabbas Rahima kan dole take zaune dashi…
Ta matsa daf dashi ta duka ta riko hannunsa na dama ta dora bisa cikinta tace “Da ni da abinda ke ciki muna matukar bukatar kulawarka, idan ka juya mana baya yanzun zamu zama abin tausayi, kaine bargon dake lullubemu da so da kaunarka, yanzun ji nike tamkar wace aka sabule fatar jikina na zama exposed to sanyi, rana, iska da kowace irin cuta domin rashin kyakyawan kariyarka. Please do forgive me, Ya Haseeb baka san irin nauyinka da nike ji ba, kwarjini da muhibbanka na cika min ido har yasa komin rashin kunyata ba zan iya tunkararka da wani zancen Kai tsaye ba, Allah yai maka wannan baiwar, still Iam so sorry I didn’t mean to hurt you.”
Kalamanta suka rinka ratsa shi suna shigarsa ya rinka jin wani ni’imtaccen sanyi cikin zuciyarsa da kokon ransa. Farin ciki ya taso ya shafe radadin dake kewaye da ruhinsa.
Cikin hanzari ya bude idanunsa ya ganta tsugunne a gabansa, ya yunkuro ya tashi jiki na kyarma ya rungumota, suka sauke wani gwauron numfashi tare da sumbatar juna..
Ya sassauta rikonta ya lakace mata hanci yace “I have only one weakness my dear…and that weakness is you please don’t take advantage of it to hurt me.”
Rahima ta Kara makale mijinta tace “You’re my love, my life and my everything Ya Haseeb.”
Duk da cewan sun taba zuwa Maiduguri wannan karon tafiyar ta musamman ce domin sunan diyar aminiyarta Hjy Fatima suka tafi, sai dai kash Yayan nata yai mata na ‘yan duniya,suna isa garin ya shafawa idonsa toka yaki yarda ta sauka gidan aminiyarta dai Lake Chad Hotel inda yai musu booking V.I P Suit
Bayan suna da kwana da biyu suka shiga ciiin birnin na El-Kanemi.
Tun zuwanta na farko Rahima ta yaba da birnin sosai musamman karamcin da ‘yanuwan Hjy Fatima da mijinta Alh Ahmad Sheriff suka nuna Mata, basu manta da alkhairin Dr Haseeb da matarsa suka yo musu a Kanon Dabo ba. Daman ai shege kadai ke manta alkhairi.
Kwanansu uku suka sallemesu da dimbin alkhairi, kyautar turarukan wuta da humra da lapayoyi saida ta kasa godiya.
Daga can Bauchin Yakubu suka yiwa tsinke wai zai kaita ta gani abokansa da suka yi makaranta tare suka Kuma dade basu ga juna ba.
Suna shiga garin, Rahima taji wani irin natsuwa ta musamman na shigarta, hakika Allah ya albarkaci jihar da wani irin kwanciyar hankali mai shigar baki irin yadda taji a ranta.
Da ganin yadda jama’ar garin ke Kai kawo cikin sukuni bisa titi kasan jihar na daya daga cikin jihohin Arewa da Allah ya karesu daga hargitsi da tashin hankali. Kai tsaye gidan abokinsa dake cikin gidajen jamiar Abubakar Tafawa Balewa suka wuce inda suka sami kyakkyawar tarbo daga iyalin shahin malamin.
Nan aka barta da muhawara da zuciyarta kan cewan tsakanin mutanen Bornu da Bauchi su wa suka fi karrama bako?
Gaba dayansu suka fita gari din ba ido abincinsa, cikin University suka fara shiga, suka nufi fadar Mai martaba Sarkin Bauchi Allah yaja zamaninsa, daga can sai Yankari Reserved, Zaranda Hotel nan ma zasu gaisa da abokinsa, matarsa da Rahima suka wuce kasuwar Wunti domin sayayyar tsaraba
Tsarin garin ya burgeta, ta rinka kwatanta wajen yawon bude na Kyarimi park dake Maiduguri da Yankari Game Reserved, duka jihohi biyun sun bata sha’awa, wajen alkhairinsu kuwa tsakaninta da jama’ar garuruwan sai adduar da fatan Allah yai musu sakayya, ta Kuma gode da kauna.
22/09/2020, 22:36 – Anty saliha: ..RAHIMA..doc by jami
53
Kwanci tashi cikin Rahima ya isa haihuwa, Ubangiji ya kawo nakuda da haihuwar cikin sauki saboda tsananta adduoi da suke tayi, ta haihu a gida tareda taimakon kawarta nurse Shafa'atu da Auntyn ta Zuwaira, ta haifo diyarta mace sak kamanin Dakta.
Murna da farin cikin ‘yanuwa da abokan arziki bai faduwa, Uban kuwa dawowa gida kawai yayi ya tadda mai jego da diyarta, yayi kamar zai lashe su, gashi Allah ya jarabce shi da son diya mata.