NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Ba tantama Hajiyarsa aka yiwa namesake “Ummulkurthum.

Ana sauran kwanaki kadan su cika arba’in aka wayi gari babu Alh. Muhammad mahaifin Zuwaira. Wannan babban rashi ya girgiza Haseeb fiye da kowa, Zuwaira taci kuka har ta gode Allah, ta rame ta fige tayi baki duk ta lalace, mijinta da ‘yaruwar zamanta suka rinka bata magans tareda nasihohi har ta dangana taci gaba da yiwa Allah godiya da ya nufeta da shiriya ta rokesa gafara ya yafe mata kullum yana sanya mata albarka kafin Allah ya amshi rayuwarsa.

Gaba dayansu suka nufi aikin Hajj da shekara ta zagayo, inda Rahima ta sauke farali, Haseeb da Zuwaira kuwa sun taba zuwa.

Tana yaye Muhibba ta nemi iznin komawa B.U.K yin masters, ya amince saboda sanin muhimmancin ilmi bai tauye ta ba taci gaba da karatu.
Tana cikin shekara ta biyu a makarantar ta sake haihuwar mai sunan Ummanta Habibatu suna kiranta Ummi.

An haifeta ba jimawa Zuwaira ta samu nata rabon itama ta haifi Ummul Salama.
Allah mai jin rokon bayinsa kenan, Haseeb ya roka an amsa, ya bashi ‘yan mata uku reras sai fatar Allah ya raya masa ya shiryasu hanya madaidaiciya.

Tunda Zuwaira ta daina fita fita zuwa Dubai da Saudiyya yawon saro kaya suka sake hada gwiwa da suna ba Hayatu yana dauko musu kayayyakin da ake bukata tunda shima ya zama business man, sosai suke samun nasibi baya ga business dinsu da Maryam Kuma, sun Kara da saro designers perfumes, shoes and bags latest designs.

Rahima ta biyawa Umma da Baffa kujerar Hajj, ranar Umma Saida ta zuba ruwa a kasa tasha domin murna tare da godiyar Allah da ya rayasu ya shirya musu zuriyyar ya daukaka su har an fara dawainiyya dasu da wasu ma duk ana cin gajiyarsu.

Ka’idane duk shekara Haseeb na fitar da zakka ya rabawa marasu galihu, ya kuma biyawa wadanda Allah ya tsaga rabonsu zuwa sauke farali ko Umrah, wannan karon kuri’ar kan Lauratu goggon Rahima, Malaminsa Mal. Nuhu da amintaccen maigadinsa Mal Hassan ta fada..
Rahima tace itama zata biyawa Uwale da fatar Allah ya kai ladar kabarin mahaifiyarta da Rabi’u

Duk karshen wata suke haduwa family ana sauke qur’ani a gidan Daktan, in an kare ayi adduoi ga dukkan mamata da masu rayuwar, iyaye, ‘ya’ya, ‘yanuwa da abokan arziki, jiharsu da kasarsu baki daya. Duk ranar jumma’a za a dafa abinci a rinka rabawa mabukata sadaka duk don neman yardar Ubangiji da neman karin yalwarsa cikin dukkan al’amurran ratuwarsu.

Aikin Dr Haseeb sai dada bunkasa yake, sunansa na dada yaduwa yayinda yaci gaba da bude rassuna jiha-jiha Yana samo kwararrun likitoci Yana zubawa

Gwamnatin tarayya ta yaba da kwazonea kwarai suka bashi mukamin Minister for health Yace bai so hidimomi sunyi masa yawa…
Mata da ‘yanuwa suka yi masa ca! Bai amince ba saida Hajiyarsa tasa baki tace “Ya Allah zai maka daukaka ka butulce? Hidimomi ba Allah ke taimakonka tafiyar da komi ba ko da karfinka kake?”
Ya amsa da zuciya guda ya fara aiki.
Kamar ba za a sake haihuwa gidan ministan ba domin Saida Ummi ta shekara uku aka samar mata kani, wannan karon sai ga kyakkyawar yaro, ga tsawo ga kiba, babansa zahiri..
Ranar suna Saida kowa yai kwalla da yaji sunansa Rabiu
Nauyi kam ya karu kan Daktan, ga na iyalinsa, ga na Mahaifiyarsa, ‘yanuwa dana yanuwan Zuwaira ga na jama’an Annabi da suke cin arzikinsa banda na aikinsa, ya zama bai da lokacin kansa.
A ka zo batun komawa Abuja Zuwaira tace sai dai Rahima ta tafi domin ta sakankance ita dince ce star din Haseeb, ta kuma hakura da haka duk da cewa ba nuna banbanci yake tsakaninsu a zahiri ba, Rahimar taki yarda da shawarar Aunyn ta domin tsakaninta da ita girmamawa ce.

Da kansa takobin dagan ya raba gardama cewan kowacce zata rinka zuwa wata uku ta dawo dayan ta tafi Kuma, wace lokacin hutu ya shigo cikin turn dinta ta tafi da yara.

Zuwaira ta sake samun ‘yar bebinta ‘yar caraf kyakkyawa, da ganinta tace wannan ai Rahima ce,kamar yana jiran ta furta, ministan ya rada mata suna Rahima suna kiranta Amira.
Zuwaira na murna ita kuwa wace akayi dominta ta korafin me yasa ba a fara sanya sunan Zuwaira ba?
Ya kalleta yace “Banyi gwaninta ba kenan?”

Ta amsa “Wallahi kayi sosai na kuma ji dadi nagode amma kayi min alkawarin idan muddin na haifi mace Zuwaira ce.”
Yace “Allah ya kawo cikin, shin ko har an samu?”
To Allah yayi an haihun amma namiji aka samu sai yaya kenan? Ya rada masa suna Habibullah.

Shekaru sun mika kwarai, tuni Dr Abdul Haseeb Junaid ya ajiye aikin gwamnati bayan shekaru takkwas yana bautawa kasarsa a matsayin ministan lafiya.

‘Ya’yansu maza sun kare univertsity. Junaid (Khalifa) Engineer ne, Mohammad(Abba) Architect, Abdul Haseeb karami ya bi sahun babansa ya zama likitan kwakwalwa, yana kasar Bulgeria karo ilmi.

‘Yan matan Kuma Muhibba ta dage saita zama irin Dr Kausar ta cikin littafin Anti Saliha Zumuncin Zamani, ita din Gynaecologist ce, Ummul Salama Lawyer ce don ita Bartister Tahir ne gwaninta(Son Zuciya) Ummi Habiba sha’awar Boutique din Sufab ya tunzuro ta da yadda ita kanta Surayuar ke tafiyar da business dinta da son taimakon iyayenta yasa ta karanta Business Administration yayinda Amira Rahima ke son zama cikakkiyar malamar makatanta mai zaman kanta irin na Sa’adatun Sagir haka dan autan gidan Daktan yace shi malamin lissafi zai zama, so Habibullah mathematician ne.

Wata rana Daktan ta tara manyan ‘ya’yansa lokacin Abdul karami ya kare karatunsa yace lokaci yayi da kowannansu zai fitar da abokiyar rayuwarsa.
Ba bata lokaci Junaid ya nuna Walida diyar Maryam yake so wace ke zuwa hutu wajen Innarta Rahima, Muhammad yace Nabila diyar Uncle Hayatu. Wadannan ‘yan Mata duk karatu suke a B.U.K. ne, Walida na karanta Mass Communications tunda a rayuwarta Laila Tahir Mutallib ce role model dinta, Nabils na karanta Economics.
Idan ta bi daga-daga na kurya kan Sha Kashi, Abdul Haseeb junior yayi shiru bai ce komi ba, to shima miskilin ne irin uwarsa da wan uban, to Barewa tayi gudu ne danta yai rarrafe? Baban nasa yaxe ya rubuto sunan wace yake so tunda ba zai furta ba, ya rubuta ya ajiye, yana fita ya dauki takardar ya warware, abinda ya gani yai matukar faranta ransa, ba domin namiji yake ba da yai guda Amma yayi abinda yafi dacewa yayi a irin yanayin, ya daga hannuwansa sama yace “Tsarki ya tabbata gareka ya Allah Ubangijin Al’Arshi mai girma!!!

Ya sake duban takardar da Abdul ya rubuta Daddy Rahima Amira ce mata ta Insha Allahu
Ya juya takardar yana mamakin ko ya aka yi yaran suka yi tunanin hada auren zumunci gaba dayansu oho?
23/09/2020, 12:31 – Anty saliha: …RAHIMA…doc by jami

54

 Iyaye, 'yanuwa da kakanni kama da abokan arziki da sauran jama'ar da suka ji labarin hada wadannan igiyoyin aure sai sha'awa da murna suke.

Kasa-kasa ba inda Daktan bai aika da katin gayyata ba, duk wasu masu hulda da asibitocinsa, abokai da tawagar shugaban kasa da kusoshin gwamnatocin jihohin Arewa sun halarci wannan gayarumin dauren aurarraki.

Da yake al’amarun tuwona Mai na ne shi kansa Daktan ya rasa inda zai fi maida hankali a sha’anin, to kusan shine uban angwaye da amaren baki daya, haka ya wakilta kanninsa da abokan arziki aka taru aka yi komi cikin tsari gwanin sha’awa.
A wajen bukin ne su Ummul Salama suka hadu da masoyansu ita ta hadu da abokin Khalifa, Muhibba dan abokin babanta balarabe nan na Riyadh ke sonta, har sun amincewa juna, sai adduar Allah ya nunawa iyaye lokacin nasu bukin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button