NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Bayan an gama shagalin da wata guda, kura ta lafa, Zuwaira ce da Rahima ke zaune a main parlour suna hira, sai kallon Rahimar take cike da sha’awa tana yaba yadda take tafiyar da al’amurran rayuwarta ta yau da kullum, me zata ce da wannan baiwar Allah? Gaskiya sai godiya da adduar Allah ya saka mata da khairan domin a dalilinta ita kanta da ‘ya’yanta sun samu nagartacciyar rayuwa, ta sami kan maigidanta yanzun girmamata yake sabanin da can inda aka fito…..
Karar waya ta dawo da ita daga duniyar tunani, tayi firgigit daidai Rahima ta dauka ta sallama, can taji ta rafka salati ta kalli Zuwaira, ita Kuma a firgice tace “Me ya faru wa Kuma muka rasa?”

Rahima tace “Allah yaiwa Husaina rasuwa sanadiyyar accident…..Zuwaira tayi kasake tsoron Allah ya Kara kamata, duniyar kenan mai halin dan mangwaro, sai ta bari ka saki jiki kana tsotso kana jin zakinta ta subuce maka. Ita yaushe rabonta da ita tun ranar da ta taho gidanta shekarun baya suka rabu baran-baran amma tana da labarin sheke ayar da take abinta har Allah ya amshi ran ta.
Ta nisa oh Allsh na gode maka da ka taro Ni ka dawo dani Kan hanya madaidaiciya, tun lokacin tuba bai kure mata ba.

Basu Kara firguta da al’amarin Ubangiji ba Saida suka ji labarin ya baza gari cewa kasa taking amsar gawar Husaina, duk inda aka tona ko a ga maciji ko kunamu har jamaa suka gaji da watangaririya da gawarta, bata samu hutun da gawar mutum ke matukar bukata ba sai dare da malamai suka taru suka rinka adduar neman gafara da rahamar Ubangiji.
Ya Allah ka shiryemu, ka shirya gaba da bayanmu dama da hauni, kasa mu fi karfin zuciyarmu kar ka kawata mana kyalkyalin duniya, abinda ya faru da Husaina ya zama izna/ishara ga yawancin matan zamani da suka maida aure abin wulakantawa, Allah ya yafe mana dimbin zunubanmu.

Wata rana Rahima na kishingide bisa doguwar kujera cikin shiryayyu falon sabon gidan da suka koma, maigida ya Kira wayarya cewan yana son ganinta.
Ta mike da hanzari ta gyara rigar da ta saka ta wata bugaggiyar shadda coffee and orange colour, anyi mata dinkin boubou da aka gewaye da cord lace gwanin sha’awa, kayan da launin kayan sun amshi jikinta sosai, ta fito dagwas-dagwas take takawa zuwa falonsa, ta sallama ya amsa ta shiga ta zauna.
Tunda ta bullo ya kura mata ido har ta iso ta zauna kusa dashi bai dai na kallonta ba, hakika kwalliyar ta burge wansa aka yita dominsa ko da bai furta ba ta fahimci cikin kwarar idanunsa,ta matsa kusa kamshin man shafarwata (avon) soft musk suka daki hancinsa, ya rumtse ido ya bude, tayi kasa da nata idanun saboda kunya tace”Gani, Daktan yana bukatar wani abu ne?”
Ya amsa “Uhhmm uhhmm. Kuma yaci gaba da kallonta dai.
Nan take ta urunce ta fara kaduwa, zuciyarta ta fara harbawa tasa hannu ta danne saitin wajen, cikin makyarkyatar murya tace “Dakta your gaze is so intense, it makes me nervous, don Allah me kake so?”

Kafin ya bata amsarsa ya rungumota cikin sarkakkiyar murya yace “What I want in my life is your love forever, can you give me that much?”

Ta kwantar da kanta a kirjinsa tace *Na dade da mika maka zuciyata cikin so da kaunarka ba don komi ba sai domin ka sanya min nishadi cikin rayuwata tunda ka amince na zama daya bangaren jikinka, ka fahimci bukata ta, ka zama babban aminina, Ya Haseeb na sadaukar da kaina da soyayyata gareka da fatar zamu kasance a haka har abada.”

Dakta Haseeb yai murmushinsa mai Kara sakata cikin shaukin kaunarsa yace “Na gode sosai my dear. Nayi murna da farin cikin jin kalamanki, Ina Kara godewa Allah SWT da Kara salati ga Manzon Tsira wanda ya luras damu sai abu hudu sun hadu sannan mutum ke da azikin rayuwar duniya. Na farko mace Saliha ta gari, na biyu makwabci nagartacce, na uku abin hawa lafiyayye sai ma hudu gida mai fadi. Kinga duk Ubangiji sarkin sarauta ya hore min dukkan wadannan, fatana yanzun Allah tasa mu gama da sauran tsoffinmu lafiya, ya bamu ikon ci gaba da sauke hakkokinsu dana iyalina, sannan yai mana kyakkyawar cikawa idan lokacinmu yayi.

Rahima ta amsa “Ameen ya Zuljalali wal ikram, Dakta.”

Wadannan dattjai biyu sunci gaba da tafiyar da rayuwarsu cikin so da kaunar juna duk da sun fara manyanta an kai ga fara ajiye jikoki, kullum soyayyarsu Kara tofo take tamkar ana mata ban ruwa daman ance so bai tsufa sai dai masoya su tsufa.

A ko yaushe Rahima ta Kan zauna ta rinka kwatanta Haseeb da taurarin littafin Anti Saliha. A miskillancin sa za su zo daya da Faruk, a tsabar kwarjininsa sai dai ta hadashi da Abdul Nasir, wajen sadaukar da Kai wajen aikinsa shi da Tahir suna mata kama, to wajen son zumunci da kaunar ‘yanuwansa fa dole ta hada shi da Sagir.
A fagen matan kuwa ta rasa wacce zata kwatanta kanta da it’s saboda tun daga Surayyar, Kausar, Laila da Sa’adatun kowaccensu sarauniyya ce Kuma tauraruwar dake haska zuciyar masoyinta don haka data hada ta tace ta tankade ta rairaye bata samu abun zubarwa ba daga mazan har matan domin kowanne naji da abokin rayuwarsa tamkar yadda suke ji da rayukansu.
Sai dai duk a je a komo abubuwan da take ganin sune jigon rayuwar wadannan ma’aurata in ka debe tsantsar so da kaunar juna sune aminci, hakuri, yarda, mutunci, kyautatawa da barin wa Wanda ya hadasu dukkan al’amurransu, baya ga sanya shi a gaba da bayansu tare da yin kyawawan adduoi da kaurara godiyarsu gareshi gwani sarkin Sarakuna.

Har yanzun a iya tunaninta ta rasa shin idan ta kwatanta rayuwar aurenta da nasu, ita dun wace lamba za a bata?

Da yake bai dace ta baiwa kanta amsa ba gudun son kai, ta hakura ta barwa jama’a suyi mata alkalancin.

  *SUBHANALLAH WALHAMDULILLAH WA LA ILAHA ILLALAH WAL LAHU AKBAR

WA LAHAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYIL AZEEM.*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button