
Tunda ta fara bayaninta ba tace komi ba Saida ta numfasa tace “Umma kema kina sauraren gulmar matan gidan buki ko?”
Tace “Ba gulma bace, wafannan batutuwa da kika ji ba karya ba za’ida, Ni nasa aka binciko min don dole insan halayyar mutanen sa zan Kai Diyata cikinsu, ko nayi kuskure.
Rahima ta kada Kai “Uhmmm Uhmm Ymma, Ni zani in kwanta.”.
Ta kalli kudin tace Dauka ki ajiye a jakarki ba zaki rasa amfani dasu ba bai kamata in kashe kyautar sarakuwarki ba ta karike tana dariya.
Cikin shagwaba tace “Umma abin ya koma zolaya Kuma, Saida safe.
03/09/2020, 22:19 – Anty saliha: …RAHIMA…doc by jami
8
Suka ci gaba da shirin buki har zuwa ranar daurin auren, Yayan ango ya biya sadakin Rahima lakadan, an daura aure lafiya an tashi lafiya, shagali ya rage na mata inda suma suka ci gaba da saukar qur’ani mai girma aka dora da wa’azi da nasihohi yayin walimar don taya ma’auratan murna da fatar alkhairi.
Iyayen amarya sunyi rawar gani wajen gyarewa diyarsu dakunanta ras, sai wanda ya gani, sun kuma nuna bajinta wajen kawowa ango garan buhunnan abinci da su Mai da sauran tarkace harda kudin cefane a sama, a yayinda dangin angon suja karbi sabuwar ‘yaruwar tasu hannu bibbyu.
Sati guda suka dauka sua amarci sannan suka koma school don ci gaba da neman ilmi. Kafin nan Saida Rabiu ya zagaya da amarya gidajen ‘yanuwansa kaf da abokan arziki don you musu ban gajiya su Kuma san juna, gidan Ya Haseeb ne farkon ziyarta inda suka yi karo dashi zai fita cikin hanzari domin ana nemansa a asibiti, sama-sama suka gaisa don Rahima ma ba zata tantance kalarsa ba, saurin da yake bai bashi damar tsayawa ba balle suyi masa godiya.
Washegari Ya Hasseb ya Kira kanin nasa bayan ya bashi hakurin rashin tsayawa su gaisa a jiya ya mika masa key din mota “focus” a matsayin gift dinsa na aurensu tareda taya su murna da adduoi. Murna a wajensu bai faduwa, Hjy Kaltume kuwa harda hawayen dadi Saida ta fitar tana ci gaba da sanyawa Haseeb albarka.
Wani weekend Rabi’u da amarya suka shiga kanti suka cikowa yaran Hasseb kayan kwalam suka nufi Galadanci misalin karfe sha daya na safe. Tuni yaran da mahaifiyarsu sun tashi sunata Kara kaina a kicin, Rabi’u ya sallama Rahima na biye dashi a baya dauke da ledan tsaraba. A guje yaran suks rugo suka nufo shi “Uncle oyo-yo. Ya duka ya dauki karamin mai suna Junaid suna kiransa Khalifa sabida sunan mahaifin maigidan kenan, shekarunsa biyu harda rabi, ya rike hannun babban Mai suna Mohammad suna kiransa Abba shima kasancewar sunan shakikin Haseeb ne Wanda ya taimaka masa kwarai a rayuwa kana shine surukinsa mahaifin matarsa Zuwaira, shekarunsa hudu.
Zuwaira ta daina abinda take yi ta juyo garesu cikin murna ta rungume Rahima “Maraba lale da amare da ango, Rabiu ba kace min aure kake so daman tuni, kaga kibar da kayi kuwa, ko zan San sirrin?”
Yayi wani irin juyi a tsakiyar kicin yace “Wasa Ni da kyau Auntyna amma kash sirrin tsakaninmu ne Rahima ko in Fadi?”
Cike da kunya tace “Kyaleshi don Allah Aunty har akwai wani sirrin da ya wuce shagwabamun da kuke kullum.”
Zuwaira tayi dariya "Laifin Dakta kenan na fada masa ya rage Kar nan da shekara guda muga Rabiu ya aje tozo."
Kusan awa biyu suka kwashe suna hira saboda ance Yayan nasu bai tashi daga barci ba.
Rahima ta zauna gefe ta zuba tagumi tana kallon yadda Rabi’u ya kwanta su Khalifa nata dumurmusarsa,ya daga wannan ya aje, yaiwa gudan cakulkuli, su fada a jikinsa dukansu suna dariya, gefe guda ga kayan wasansu da suka watsar sunyi kaca-kaca, shaawarsu ya cikata Nan take tayi shaawar samun nasu babyn harta fara imagining yadda babansu zai rinka wasa dashi kamar yanzun, gaskiya Rabi’u mutum ne Mai son Yara..
Bata ankara ba taji yana gaida Ya Hasseb, tayi saurin gyara mayafinta ta zamo daga kujera ta durkusa gwiwa bibbyu ta gaida wan mijin nata cikin ladabi da biyayya.
Ya amsa cikin yanayin da bata iya fassarawa don babu sakin fuska a tareda shi sam.
Bai zauna ba ya koma falonsa Kaninsa ya bishi can ita kuma suja ci gaba da hira da Zuwaira inda ba a dau dogon lokaci ba ta lakanci halin Antyn tasu tas
Zuwaira macece Mai harka,tafi mijinta sakin fuska nesa ba kusa a, tana da son mutane da saurin sabo saidai fa akwaita da surutu don cikin awanni kalilan ta fayyace mata labarinta kaf , na iyayenta da ‘yanuwanta da na shi kansa maigidan nata, ta fada mata irin zaman da suke da irin matukar son da take masa.
Wani Abu da ta lakanta Aunty Zuwaira irin matan Nan ne masu son rayuwar jin dadi kota halin kaka, masu son kashe kudi da neman kudin kota wacce irin hanya Kuma..
Da alamun ilmin addini bai gama ratsata ba, abinda tafi sani shine ta daura zani komin tsadarsa, ta saka latest takalmi ta rataya jika cike da dimbin naira ba tareda tunanin komi ba, tana da son cin dadi daoilin hakane yasa ko ta dafa nama a tukunyarta ka’ida ne duk daren duniya a sawo mata gasashshiyar kaza, ‘yan shila, tsire ko balango taci ta kwanta.
Babban abinda ya bata mamaki babu wani kusanci Mai karfi tsakaninta da mijin da take ikrari tana masifar son, kowa harkar gabansa yake…..
Saida ta tabu kafadarta ta dawo daga duniyar tunani..
“Duk tunanin angon ya barki ne haka? Tafdijan da kece matar Dakta ya za kiyi?”
Rahima ta share maganar tace “Aunty lokacin dora abincin rana yayi ko?”
Ta zabura “Tabbas Ni bana manta inada baki cikin gidana ba, taso mu shiga kicin yau muci girkin amare.”
Suna aikin Zuwaira naci gaba da yi mata bayani nau’in sanaar sa take yi, Dubai take ziwa saro manyan bedsheets harda zinari, a cewarta ba zata iya wahalar karatu ko wani aikin gwamnati ba.
“Me kike karantawa ne a school? Ta tambayi Rahima.
Ta amsa “Special Education ne, tunda shi accountancy yake yi.”
Tace “Me ya kaiki karatun wani special education?”
Tayi ‘yar dariya “Wallahi Aunty Zuwaira Ina matukar tausayin yara makafi, gura gu da bebaye da kurame, da ma wadanda ake haihuwarsu da karamar kwakwalwa, a ganina hanyar da Zan iya taimaka musu kadai kenan.”
“Kice kawai kina son wahalar da kanki da rai da lafiyarki baki koyar a normal school ba sai makarantar kurame, ah ah wahala dai kike shaawa.”
Ta girgiza Kai “Banyi tunanin wata wahala ba gaskiya, abinda na sani shine kowanne aiki na zabawa kaina dole in zama Mai dauriya da hakurin jure kowacce irin wahala ke tattare da aikin, na zabi wannan fannin ne don bada tawa gudumuwar.”
Zuwaira ta gyasa Kai “Daukarwa rai dai Allah ya taimaka ai kin kusa karewa ko?”
” Da ikon Allah karshen shekara nan zamu gama
Basu tafi ba sai bayan laasar, zuwa lokacin maigidan ya fita tuni kafin ya fita ya ba Zuwaira kudi a baiwa sarakuwarsa. Da kyar ta amsa, a ganinta dawainyyar tayi yawa ta isa yanzun su ya rage su nemi nasu na kansu su ci gaba da kwatanta alkhairin da ake musu don shege kawai ke mance alkhairi Dan halas bai mantawa komin kankantarsa.
Watanni takwas kacak suka rage su kare digirinsu na farko, cikin watannin ne Rahima ta Kara shakuwa da mijinta, kaunarsa ta fara zurfi da tasiri cikin zuciyarta har abin na daure mata Kai. Yanuwa da abikan arzikinsu sai shaawar zaman nasu suke musamman yanayin tafiyar da rayuwar auren nasu
Tunda akayi auren sai Kara ji da juna suke, suna samun natsuwa da kwanciyar hankali irin wadanda ake samu muddin aka yi katari da dacen abokin zama, ba abinda yafi musu dadi illa Kara fahimtar juna da suke ko yaushe.
Rahima bata da damuwar data wuce taga ta kare karatunta lfy, bayan so da kaunar mijinta tayi dace da sarakuwar da take ji tamkar ita ta tsugunna ta haifeta itama, koda wasa Hjy Kaltume Bata son ganin bacin ran Rahima ko na dakika gudane, duk abinda ta samu indai naci ne sai taba Rahima taci kafin takai bakinta, idan kudine ko yaushe tana tattalin ta bata su Wai karta zauna baby na kashewa, dangane da abubuwan hidimomin yau da kullum kuwa kamar su man shafawa sabulu wanka dana wanki duk wata zata kebe kudu a sayo ta kirata ta damkasu a hannunta, kayan lashe-lashe da tande-tande ba a maganarsu, ita dai Kar Rahima ta nemi komi ta rasa.
Ita Kuma bata zubar sa tarbiyyar da akai mata tun a gida ba, daraja na gaba ko a Ina ne musamman tsoho, to ta mutunta wadanda bata San inda suka fito ba a titi ballanta uwar mijinta Mai kaunarta tamkar ta lasheta. Sai ya zama cikin surukanta babu kamar Rahima ba don ta kasance matar Dan autanta ba ah ah kima da girmamatan da take yi tun zuwanta gidan ya haifar da hakan.