
Kafin su fara karatu gadan garan ne suka shirya suka nufi Gumel gano kakanta da sauran dangin mahaifiyarta, duk sati zasu ziyarci gidajen ‘yanuwa ba inda ta tsani zuwa sai gidan Hayatu sabida rashin zaman lafiyar da matansa keyi, ta tsani tashin hankali.
Ba zata manta ba ranat da suka fara zuwa gidan ta riga Rabi’u shiga ciki tayi sallama aka amsa ta durkusa don gaida matar data gani zaune bakin famfo tana wanke-wanke, ta dago Kai ta Mike tsaye tana fadin “Lalle yau nayi farin gani, amarya Ina angon naki?”
Kafin ta amsa Rabiu ya sallama yace “Aunty amarya gamu mun taho me kuka aje mana?”
Sai nan Rahima ta gane wannan ce amaryar Yaya Hayatu sunanta Haulatu…
Haulatu tayi dariya” Me kuka kawo mana goron amarci dai, ku shiga dafa ciki ka barta a tsakar guda tsaye.”
Yai musu jagora zuwa dakin uwargidan suka sallama bata amsa ba sai da ya daga labulen dakin suka ganta zaune abinta, Rabiu ya shiga ciki Rahima ta bishi syka zauna suka gaisheta ta amsa a ciki, suka zauna shiru-shiru na mintoci bata Kara ce musu kanzil ba, ya kada Kai ya umurci matarsa ta tashi su tafi, suka sake mara sallama ta share, suna fitowa suka shiga dakin Haulatu don su sake gaisawa itama su bata hakkinta, ita Kam tayi ta jansu da wasa har ruwa ta kawo musu da lemu tace su tsaya suci abinci kuma..
To ai kuwa zaman nan da suka yi dakin amaryarta ya tunzura Jamila, ta fito tsakar gida ta shiga masifa tana sakin habaici “Ahayye ayyririru, yau Ni za a gwadawa gulma da makirci irinta dangin miji, dadin abin kafin a auro wata Ni aka fara gani da sani dole a zauna dani komin kiyayya, magulmatan banza munafukan wofi.”..
Ba Wanda ya futo balle ya tanka mata, ana haka Allah ya dawo da Hayatu gida daga wajen aiki, malamine a makarantar Shekara. Yana shiga gidan nasa yai katarin surutan da Jamila ke Fadi, Rabiu na jin muryarsa danuwansa ya fito Rahima ta biyo shi suja gaishe shi
Yana amsa yace “Lafiya meke faruwa Rabiu?”
Ya shafawa idonsa toka yace bai sani ba ya tambayi matarsa. Jamila tayi farat ta amsa “Dole kace baka sani ba mana algungumi, ka dauko wannan kekasasgahiyar matar taka Kun haddasa fitina, ta juya Kan mijin wallahi kayi mishi kashedi, hawainiyarsa ta kiyayi ramata….
Hayatu yaji zata zake ya buga Mata tsawa “Ke ar wallahi ko ki min shuru ko ranki ya baci sai in tattakaki yanzun nan inga me za ayi mutumiyar banza, ni kenan bani da ikon fita in dawo in tadda gidana lafiya, kaina farau aje mata biyu? To wallahi kinyi kadan, duk iskancin da za kuyi ku tsaya kaina Kar shegiyar data shiga sabgar ‘yanuwana, sakararu marasa tunanin abinda zaije ya komo.”
Kafin ayi haka Haulatu ta banko labule ta fito a fusace ” Ah ah Hayatu wasa yai wasa banda tsikarin uwar miji da tabarya, mene nawa a ciki Ni da na tarbesu nace su jira abinci, tambayesu kaji data fito tana masifarta wa ta bi ta kanta balle ya tanka, gaskiya ni ba shegiya ba ce da ubana kafi kowa shaidawa tinda Saida ka Kai masa sadakina ya baka aurena, shegun sakararru na inda suke.”
Tana rufe baki Jamila ta zabura sai tau! saukar mari, Haulatu ta rike kuncinta tace “Kika mare Ni? Wallahi baki isa ba sai na rama, itama ta zaburo tana jiran a dabance, Hayatu yai saurin riketa “Kyaleta Haulatu itace babbar kwabo ta yada girmanta.”.
Su ma bakin suka bata hakuri, da kyar aka ciwo kanta ta hakura suka iza keyarta ta shiga daki.
Maimakon jamilan tayi shuru sai cewa tayi “Ai da Kun Kyaleta tazo ta rama din yau in gwada muku yadsa ake kirba mutum in lallasata in mata dukan da uwarta bata taba yi mata tunda ta fito duniya.
Takaici ya kama Hayatu ya harzuka ya dumfareta yace “Bari ni in karairayaki kafin ki lallasata, tana ganin ta dau faskaren icce ya dumfareta ta sheka daki ta danne kofa gudun kar a sabauta ta.
Suka bar su Rahima tsirma-tsirma a tsakar gida, yana basu hakuri, suka dawo gida su basu ci abinci ba su hankali bai kwanta ba..
Tun a lokacin bata sake marmarin zuwa ba, gidan Ya Haseeb Kuma iya yin Aunty Zuwaira ke damunta
04/09/2020, 00:24 – Anty saliha: …RAHIMA…doc by Jami
9
Sauran watanni uku kacal su zana jarabaea akayi bukin Maryam ta auri Alh Abbas dinta, matarsa guda da yara shidda maza da mata suna zaune a sabon fegi. Da alamun Maryam ma Bata dace da Uwargida ba sai abinda Allah yayi kenan domin ita ma ba baya ba wajen kishi da rashin hakuri sam bata yarda a takata ko a wulakanta ta.
An dai yi buki an kare lfy babu wani gagarumin tashin hankali sai ‘yan kunji -kunji ko Kuma don Alhaji Abbas namiji ne daya iya rike gidansa ba kamar Hayatu ba da ya zama shakulatin bangaro, yayi sake iyalinsa suka fi karfinsa.
A kwana a tashi Rabiu da Rahima sun kare jarabawarsu sai adduar Allah yasa ayi nasara.
Bayan sun huta na sati biyu ta rokeshi ya kaita gidan ‘yaruwarta, ya amince ya dauketa suka tafi. Sun shade awa uku suna hira amma Rabiu bai sa niyyar tashi ba, Maryam tace “Ni fa ban gane ba shin ba tafiya zaka yi ka bar min ita anjima ka dawo daukarta ba?”
Ya kwashe da dariya “Kina nufin in koma gida Ni kadai? Gaskiya ba zan iya ba, kafarta kafata.”
Maryam ta kalli Rahima “Say something kinji Wai ba zai barmu muyi hirar zumunci ba.”
Ta danyi dariya “To shin din bare ne?”
Yace “Kyaleta kawai ta nuna min ‘yan ubanci alhalin an zama daya Ni da Rahima.
Maryam ta daga Kai “Ai ga alama nan na gani tun zuwanku, Ina ruwan Romeo & Juliet.
Yayi dariya “Kuma ba a hanaku ba.”
“Ah ah Wannan irin soyayyar sai ku yara, Ni mijina tsohone bayan haka ina yaga wani lokacin soyayya Yana can yana neman mana na sakawa a bakin salati.”
Rahima ta jinjina “Ke din yadda kike?”
“To naji na amince Amma don Allah Rabi’u ka tsahirta mana kona rabin awa ne, magana Nike son yi da ita, zancen na Mata ne Kasan akwai sirri.”
Ya kalli matarsa “Kin amince in tai in dawo Nan da awa guda?”
Rahima tayi masa irin kallon soyayyar nan tace “Is okay, nagode.”
Ya mike ya sumbaci gefen kumatunta “Sai na dawo kenan.”.
Yana fita Maryam ta juyo gareta “You surprised me, I was impressed Kar dai ince kun kamu?”
Ta kishingide ta amsa “Ina zaton hakan Nima, a hankali so da kaunar mijina suka rinka shigata saboda duk da kasancewar sa yaro matashi ya iya tafiyar da al’amarin rayuwar aure yadda yakamata, ko ya fahimci feelings dina ne ya bi duk hanyoyin da suka dace ya mallaki zuciyata, idan kinga irin kishina da yake sai kin rike Baki, ya fara fadin Wai anya zai barni inyi aiki kuwa, ga kulle, idan kuwa ya bari na fita to ki tabbatar da tare zamu fita, ke al’amarin nasa tun Yana ba Hajiya shaawa ta fara nuna damuwa tace tun kafin aje ko Ina zai bullo da sabon al’amari? Ni kuwa maimakon ya dameni ko inji haushi sai dadi nike ji, Ina Kuma ji a zuciyata muddin ya tsaya kan va zanyi aikin ba zan amince don ko kusa ban son abinda zai batawa masoyina rai.”
Maryam ta kura Mata idi sosai tace “Tabbas kina kaunarsa amma har yanzun da sauranki baki shiga matakin da Zaki ji amsarki ba, akwai sauran lokaci tukunna.”
Rahima tace “Haba dai duk nike ji dinnan da saurana?”.
“Kwarai kuwa idan lokaci yayi zaki fada min da kanki, yanzun kashi talatin kike dashi cikin dari kina awo aiki ko rabi baki Kai ba.”
Ta nisa “Ashe in Kara zage damtse tun kafin bakon dake tafe ta/ ko ya kutso kai ana hanamu shakatawa.”