
Maryam ta bude baki cikin mamaki “Lah kema ciki gareki Rahima? Labarin da zan fada miki kenan Nima, shikenan za mu yiwa Umma tagwaye sunan da take kiranmu.”
Suka rungume juna suna adduar Allah ta inganta musu ya Kuma saukesu lfy idan lokacin yayi.”
Bai Kara ko minti guda ba, awa dayan na cika suka ji horn din motarsa suka kalli juna, Rahima ta mike ta dau Jakarta ta gyara mayafinta tace "Mu zamu tafi sai kinzo kenan?"
Tace Insha Allah, uhhmm did he know about the pregnancy?"
Tace “No but yau zan sanar dashi tunda na tabbatar”
Suna fita Maryam ta riko hannunta ta mika masa tace "Rabiu manya, to ga matarka, ban cinyeta ba balle in gutsuri namanta "
Ya sosa keya “Ba haka bane Aunty…
Ta katsesa “Kwarai na fahimta to Allah ya bamu alkhairi, sai nazo.”
A wannan ranar wani sabon nishadi ya rufesu suka jima suna hirar soyayya kasancewar a ranar suka shekara daya cif da aurensu, sunyi nafilfili da adduoin godiya ga Allah SWT kana suka kwanta.
Bata yi hanazarim shaida masa batun cikin ba Saida dare ya tsala ta tashesa daga barci, ya tashi ya kunna fitila ga zatonsa ita a bata da lfy yace “Lafiya?
Ta kura masa idanu tana nazarinsa, duk da cewan barci ya farka yai Mata wani irin kwarjini, fuskarsa sai sheki, ya Kara kiba da haske, tayi ajiyar zuciyar, Rabi’u yarone matshi amma girman jikinsa kansa ayi kuskuren shekarunsa, suna mugun kama da Hayatu sai dai ya darashi tsayi da jiki, Hayatu farine mi yar doguwar fuska,mutum ne Mai fara’a da son mutane ga ban dariya, kusan ko yaushe ka gansa hakoran nan bude suke Yana dariya, da wuya ayi masa Abu ya bata masa rai har yai fushi, wadannan kyawawan halayen nasa yasa yake da jama’a da abokai babu iyaka.
Ya kagu da kallon da take masa ya girgizata “Wai shin lfy.
Tayi “yar dariya “Hakan nan kawai kwana nan sai inji kana matukar burgeni ko kallonka nayi sai inji wani dadi a zuciyata.”.
Ya zumburi baki cikin wasa “Kawai kika tasheni barci don ki kalleni kinji sanyi a ranki ne?”
“To me zanyi maka da dare Nan, kishi ko yunwa?”
Ya janye matashin da take rungume dashi a cinyarta ya maida kansa ya kwanta a wurin Yana mai sakin kyakkawar ajiyar zuciya yace “Ni kuwa ni’ima nike ji duk lokacin dana kalleki, shin Rahima kinsan irin mutuwar son da nike miki kuwa?
Ta rufe bakinsa “Rayayyen so dai mijina idan kace mutuwa ai ba zance kenan, na yarda da so da kaunarka, nima hakan yake a zuciyata, domin Ubangiji ya karfafa mana dankon soyayyarmu ne ya bamu wannan.” Ta kamo hannunsa ta dafa cikinta.
Da farko bai fahimci inda zancen ya dosa ba, daya dago ya zabura ya cakumota ya riketa gam ya fara tsalle Yana sumbatarta “Da gaske cikine dake Rahima alhamdulillah.”
Tace “Da gaske Ina dauje da bebinka Rabiu amma idan baka daina juyi dani haka a tsakar daki ba zamu ita rasawa don likita ya shaida mun saina rinka kukawa in bi a hankali mahaifata Bata da kwari.
Nan da Nan ya ajiyeta a hankali yace “Are you ok?”
Tace “Banda wata matsala sai adduar Allah ya rabamu lfy.”
Murna ta rufesa ba sauran barci kenan, ya zauna ya fara plan din tarbon jaririn da sauran kusan watanni bakwai kwarara kafin ya fito duniya.
Alla- alla yake ya kare sallar asuba, ya shuga gaida Hajiya yai Mata albishir, saboda tsabar farin ciki ranar tuni tayi Bata ci komi ba, farin ciki ya kosar da it’s, can gidansu Rahimar ma abinda iyayenta suka kashe suka tsare kenan, jiran ranar haihuwar ‘ya’yansu biyu, Maryam da Rahima.
04/09/2020, 13:45 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
10
Lokacin tafiya bautar kasarsu yazo, Rabi’u ya shiga ya fita aka barsu a garin Kano, inda shi yake Bank Rahima Kuma ke koyarwa a makarantar kurame.
Watanni bakwai da ‘yan kwanaki Rahima ta kamu da zazzabin malaria, Rabi’u ya rikice musamman da yaji likita ya gaya masa ba a son mai ciki ta kamu da zazzabin saboda yana iya haddasa miscarriage ko yaiwa uwar lahani.
Kowa ya dukufa adduar Allah ya bata lafiya ya kareta da abinda ke cikin, kwana biyu kamar taji sauki ana uku zazzabin ya dawo wannan karon hade da ciwon baya da mara. Likitoci sunyi kokarinsu amma kafin awa guda nakuda ta taso haihuwa ce gadan-gadan, da taimakon Allah ta haihu lafiya ta sami danta bakwaini. Iyaye da ‘yanuwa da abokan arziki suka cika asibiti sai dai kash da kyar aka barsu suka ga jaririn a hannun nurse aka wuce dashi aka saka shi cikin incubator sabida bai gama yun kwari ba ga rashin lafiyar jundice da akan haifi wasu jariran dashi.
Ba a sallamesu ba sai ana gobe suna tare da gargadin Kar a bari a rinka daukar yaron gudun jagwalgwalo
Hajiya Kaltume ta Kira Rabiu don su shawarata sunan da za a sanyawa jaririn yace "Hajiya na riga nayi masa huduba tun ranar da aka haifesa kinsan addini ya koyar daamu da zaran an haihu mu yiwa yaranmu huduba,bayan munyi musu Kiran sallah da kalimatu-shahada a kunnuwansu ba sai an jira sai wani ranar suna ba. Koyar Manzon Tsira ne."
Tace “Naji ustaz, wane suna ka saka masa Ina fatan ba irin na zamanin nan masu wuyan Fadi ba.”
“Ko daya, wannan ko sau nawa zaki iya fadi cikin mintu guda kacal.”
“Wai zaka fada min ko sai ka gama ja min rai Rabi’u?”
Yayi dariya “Sunan Ya Haseeb yaci, Abdul Haseeb karami ne Hajiya.”
Ta gintse dariyarta tasha mur “Maimakon ka sa sunan mahaifinku da Allah yaiwa rasuwa, mene naka na saka sunan wanda yake raye?”
Rabi’u yace “Ina Sunusin Ya Hayatu sunan baban yaci Hajiya, tunda yasa ba lale nima sai na saka ba, bukata a samu magaji an samu ai, ba Kuma sai mutum ta mutu ake saka sunansa ba, Hjy Ya Haseeb ya cancanci wannan adalcin daga garemu din da taimakonsa Allah ya hadamu aure, don haka kiyi fatar alkhairi kawai.”.
Daman ba Wai bata ji dadi bane, ah ah ta yaba da kaifin hankali da tunaninsa kwarai, ta gyara zama tace “To Rabiu Allah ya raya mana shi yasa dadin musulmi ne yasa ya gaji mai sunan.”
“Yauwa yanzun ki Kai magana, Ameen Hajiyata.”
Anyi suna an ci an sude, Hasseb babba yana can wani aiki a babbar asibitin dake kasar Morocco, sai labarin haihuwar yaji da labarin anyi masa takwara. Da zai dawo sayayyan musamman ya yiwa uwa da namesake dinsa din nuna jin dadin karamcin da aka yi masa, yazo har gida yaga jaririn da ake fadin yafi kama dashi a bisa mahaifinsa.
Cikin watanni biyu Abdul Haseeb ya murje yayi ‘yar kiba har ya fara wayon gane iyayensa da kakarsa da yake yini can wajenta.
Suna gab da kare bautar kasa wata rana, Rahima ta gama shiryawa maigidan abincin rana ta girka masa tuwon shinkafa miyar alayyaho abincin da yafi so kenan, sai gashi ya dawo ya hayo sama dauke da Abdul a kafadarsa yana rike da jakar aikinsa a hannu daya. Ta tarbesu ta amshi jikar tana masa sannu, ya amsa Yana ci gaba da yiwa dansa wasa, ta tsaya ta zuba tagumi tana kallonsu tace “Kana bani mamaki, yanzun daga shigowarka kaje ka dauko yaron nan ko kunyar Hajiya baka ji, haba ana son kawaici don Allah.”
Ya kyalkyace sa dariya “Ita Hjyr bata damu ba, ki tuna tun safe yake wajenta sun yini tare, Ni kuwa sai yanzun na Sami damar wasa dashi.”
Ta kalli Abdul “Hhmmm ko baka koya masa kimi ya koyi kyuya, duba yadda ya kura maka ido Yana kallonka.”
Rabiyu ya zaunar da Abdul bisa cinyarsa yace “Da Kuma fa gaskiyarsa gashi ba nine babansa ba.”
Ta bude baki cikin mamaki “Ba kaine ba to waye ubansa?”
Ya amsa “Maida wukar, nina haifi abina mana Amma Ya Haseeb ne babansa.”
Ta hararesa cikin wasa “Tunda aka haifi yaron nan kake wannan furucin, kowa yasan a mtsayinsa na yayanka dole a kirasa baban Abdul ka taba ganin an raba anta da jini?”
Yace “Inda Mai iyawa ai sai a basa ya gwada mu gani.”
Ta gyara zama “Hhhh Ni dai kawo sa kaci abinci.”
Ta karbesa ta goya, ta jera masa abincin ta zuba masa suna hira, yana cin abincin yana dan tsayawa , can ya ture plate gefe yace “Na koshi.”
Ta kallesa cikin damuwa” Abinda na lura kwanannan baka son cin abinci ka koshi har ka fara rama, wani Abu na damunka ne?”
Ya girgiza Kai “Ba wani abu bane, just cikina ne ya cushe ko naso cin abincin sai inji na koshi dole nakan hakura.”
Tace “To muje asibiti mana, mutym ya zauna sa cuta a gida?”
Ya taso ya dafa kafadarta “Karki damu kanki da yawa, dazun da ya taso min a office Nan da Nan na ziyarci clinic dinmu suka ban magani nasha naji dadi wallahi sai anjima karfe tara na dare zan Kara sha.”
Fuskarta ta canza “Rabi’u baka da lafiya ka boye min?”
Ya rungumota “Afwaan Rahima ba wani sabon Abu bane da baki sani ba, kinsan na kanyi ciwon ciki muna school amma after 3-4 days nakan sami sauki inci gaba da harkokina, a gaskiya na dade ma banji ya tashi ba that’s nima ban koma asibiti ba amma insha Allah gobe sai mu tafi.”