
Tace "A takaice ma baka San kowacce irin cuta ke damunka ba."
Yace “Sun Fadi Amma ban wani rike ba na manta.”
Ta sassauto “Hhmmm to Allah ya saukaka ya baka lfy, Amma don Allah ka kula da kanka, we do need you.”
Yayi murmushi “I need you too my love.”
Gari ya waye, bayan sun kammala ibadarsu da yin kalacin safe suka fara Shirin fita wajen aikinsu, Rahima na duke tana shirya Abdul taji wata irin kara mai firgitarwa, ta saki Dan ta nufo Rabi’u dake kwance dafe da cikinsa tabbacin karar daga makoshinsa ta fito, a rude tazo ta dafa shi tayi kokarin dagasa ta kasa, ta kira sunansa ya amsa da kyar yana numfarfashi yace “Cikina Rahima….
“Sannu, bari in Kai Abdul wajen Hjy mu tafi asibiti…
Ta sungumi Dan ta sauka kasa a guje ta isko Hjyr na azkar ko gaisheta bata tsaya yi ba ta mika Mata Abdul tana fadin “Hajiya babansa babu lafiya asibiti zamu tafi.”
Ganin yadda take a rude itama ta goya Abdul ta bi bayanta suka hau saman tare a ranar bata ji wuyar data kance yana mata ba .
Taga halinda yake ciki, har kamaninsa sun canza, ta sake fitowa tayi waje neman makwabta suzo a taimaka musu a fito dashi. Kafin kiftarwa ido maza sun taru an daukoshi an saka a mota suka nufi asibiti, Rahima da aka hana binsu kuwa gidansu ta nufa tana kuka, suna jin abinda ke Nan, Alh Mamman da kansa ya daukota da Ummansu suka nufo gidan Hajiyar inda suka taras ta kira Yayyinsa tana fada musu su wuce asibiti suma gasu nan tafe.
Asibitin Murtala aka kaisa inda da shigarsu ba bata lokaci manyan likitoci su kayi caa a kansa, nan da nan babban likita yace aje ayi hoton cikin don sanin matakin dauka da gaggawa.
Dr Haseeb da Hayatu suka isa hankali a tashe, suna ganin halinda yake ciki suka dimauta.
Anje anyi hoton, likita ya duba ya fara rubuce-rubucen magungunan da za a fara bashi kafin su gama bincike Rabiu ya bude ido da kyar ya hango dushi-dushin Haseeb, ya dago hannu a galabaice ya miko masa, Haseeb ya fahimci magana yake sonyi don haka ya duka daf da bakinsa…
Cikin rada maganar ta fito “Ga amanar Rahima da Abdul….
Yace “Na karba Rabiu Allah zai baka lafiya…
Haseeb bai gama rufe bakinsa ba Rabiu yai kalimatu-shahada ya cika.. Nan aka yita .
Dagowan da bai ita yi da kansa ba kenan Saida aka kamashi yana salati .Innalillahi wa Inna ilahirrajiun.
Mutuwa kenan, daci Mai kore Zaki, Mai raba da da mahaifi, Mai raba Mata da miji, Mai raba danuwa da danuwa, Mai raba masoyi da masoyi, Allah yasa mu cika da imani.
Duk da cewa Ubangiji yace bai halicci wani don wani ba, a ko yaushe muka yi rashin daya daga cikinmu al’amarin Kan zama sabo, bamu iya dauriya dole muyi juyayin rashi da tausayin kanmu tare da fargaba da tunanin cewan muma fa komin dadewa wata rana sai mun tafi lahira. Allah yasa mu cika da imani
Maganar halinda yanuwa da abokan arzikin marigayi Rabi’u suka kasance bata ko taso ba balle matarsa Rahima, Hajiyarsu kawai Allah ya saukarwa dauriyya ta dake ita ke baiwa jamaa hakuri
Bayan kwana bakwai kowa ya watse sai wasu daga cikin dangin uban Rabiu da kanun Hjy Kaltume Mata biyu don suci gaba da debe musu kewa. Hayatu ma Kan kawo matansa su yini. Wani ikon Allah rasuwar Rabiu ne ko shiriyar Ubangiji ne yasa yasa su natsuwa da kama kansu har jamaa na mamakinsu oho. Shima Haseeb matarsa na zuwa ta koma da laasar, Maryam ma na tafe duk bayan kwana biyu, jamaa kowa nata kokarin ganin an debe mata kewa.
Ita kuwa sai kallonsu take, hawaye sunki kafewa a idanunta musamman idan ta dauki Abdul tana bashi nono. To tun hawayen na zuba har sun kafe ta fara kukan zucci. Idan ta tuno rayuwar da suka yi, watau haka Allah ya kaddari rabon Abdul ne yasa akayi aurensu a gaggauce, rabuwar ma Allah ya kawo kwatankwacin hakan. Oh Allah ka jikan Rabiu ka sanyaya masa, hakika sunyi rayuwar auren daya dace, rayuwa mai cike da nishadi da farin ciki abin shaawa fa kowa, da karshen tazo Allah yasa shakuwa tsakaninsu bayan so da kaunarsa da suka fara tasiri a zuciyarta, Ashe Wai ba za akai ko Ina ba, Ashe rayuwar tazo karshe…. Hawaye masu zafin gaske suka gangaro zuwa kumatunta suka diga kirjin Abdul, ya saka kuka, ta lallasheshi, ita tama manta Yana bisa cinyarta, da Hjy Kaltume ta lura ta shiga yi Mata fada, ta dawo tayi nasiha taci gaba da lallashi, maimakon tayi shuru hawaye sai Kara fitowa suke Saida ita kanta Hajiyar da sauran mutane suka koka.
04/09/2020, 17:24 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
11
Kafin ta gama takaba ‘yanuwa, iyayenta da dangin mijinta kaf sun nuna mata gata Kuma ita wata ce a gare su don Haseeb ma ba a batun dawainiyar da yake musu ita da danta Abdul karami, tun bai saba da wan uban nasa ba har yai sabo dashi kwarai saboda yawan dauka da fita dashi yawo da yake in baida aiki sosai a asibiti…
Kwanci tashi ba wuya Rahima ta gama takaba, ta Kara sati guda da kyar kana ta tattara kayanta tace gidansu zata koma. Wani sabon tashin hankalin, ranar Abu ya koma sabo to amman barin gida ya zama dole don ci gaba da harkokin rayuwa.
Bisa yarjejeniyar ba zasu amshi Abdul ba sai ta sami wani mijin ta goya danta suka koma inda tafi wayo, gidan Alh. Mamman.
Makarantar da take koyarwa basu saketa ba ko bayan gama bautar kasarta nan suka dauketa aiki taci gaba da koyarwanta.
Gama takabarta keda wuya masoya suka ce sallamu alaikum, harda wani abokin Rabiu da suka kare school tare, wani ikon Allah saurayine shi ko auren fari bai yi ba, ya kasa dumfararta da kansa sai letter ya tura mata Wai Yana jin nauyi, yadda bata saurare shi ba haka taki sauraren kowa cikin zawarawan dake mata Kara kaina tun daga wajen aiki har gida, da ma wani abokin Alh Abbas mijin Maryam Wanda uwargidansa ce ta rasu ta bar diya biyu, Yana son suyi aure ya rike Mata da ta rike masa nashi, shima bata cewa Abbas din tana yi ko ah ah ba, kusan duk Wanda ya nemi kusanci sai tace a bata lokaci tayi shawara, a zahiri kuwa ra’ayin sake auren ne bashi a zuciyarta, a nata tunanin ma da za a barta haka zata yi zamanta din tasan zata iya tsare mutuncin kanta dana iyayenta tunda Allah bai halicceta kharija ba, wai don a matsa mata da batun auren ne taki yaye Abdul da ya Kai kusan shekaru biyu. Umman tayi-tayi ta gaji tasa mata ido, gara bata son bacin ran Rahima daidai da kwayar zarra, suka ci gaba da lelen Dan da yake gudu koina, wani burgewa ma sai ya gama yawonsa ya dawo ya zauna yace ‘Mami zan Sha mama’
Irin sangarcewar da yayi Maryam ta taho ta gani ta fara masifa, Umma ta fara kakkare Rahima, ita din ma tace Umma karki kula surkulenta, shin don ta yaye Walida sai tace sai na yaye Abdul?”
Umma tace “itama ba yayen Allah tayi ba ciki ya sa akayi saurin hanata nonon.”.
Rahima tayi dariya “Ah to gane min hanya Umma na makaho da yaso tsegumi. Kin ganni ni ba miji ba, Ni ba wani kwakwkwaran bazawari ba mene nawa na hanzarin cire yaro a bakin nono, Maryam ko tausayin Abdul ma ba kya ji.”
Taja tsaki “Ke da Umma ke ban tausayi sabida ga gaskiya kiri-kiru Kun take, shun Umma kin kalli diyar taki da kyau Kinga yadda ta kode tana kanjamewa?”
Cikin damuwa tace “Na lura sosai, nima ramar nata har tsoro take bani, yarinya taki sakin ranta ta hakura, wallahi kullum fadar da nike mata safe da yamma kan ta fauwalawa Allah rashin da muka yi shi Kuma Allah yasa yana cikin rahamar Ubangiji.’
Maryam ta gyara zama daman gangara take nema tace “Umma ban tari numfashinki ba, ya za ayi ta samu natsuwar hankali tana zaune muku haka kawai. Ni a ganina duk halinda data shiga laifinku ne, baku matsa mata ta samu miji tayi aure? Kawai Kun Kyaleta sai biye mata kuke, har kin yayen nan don kar a sami kafar mata batun aurene.”
Rahima ta harari Maryam “Umma ki daina saurarenta kinsan halinta da zuga.”
Umma ta nisa “Wannan karon Kam gaskiya take Fadi na Kuma gano kamshinta bari Baffanku ya dawo.”
Ta sunkuyar da Kai ta dafa Umma “Don Allah karki hadani da Baffa Umma nayi alkawarin yayesa cikin satin nan.”.
Maryam tayi Mata gwalo tukunna kafin taci gaba “Ai ba yayen ba ta fitar da miji shine batu, tayi alkawarin zata amince ba zata kara kin sauraren wani abu har Allah ya zaba mata mijin.”