RANA DAYA BOOOK 2 CHAPTER 13

Ta ce Ai da yake ma gashin naki ba shi da zuciya, ko an yi banza da shi sai yayi ta hauka
Salma ta ce Shi ko Yaya ma da na ce ina son “
kitso sai ya ce ya fi son gashin a haka, sai dai in ina son a gyara min in mishi magana Hadiza
“To shi kenan, kin ko fara zuwa
Makaranta?” Salma ta ce,
“Nasan ya na sane shi
yasa bana mishi zancan
Da za ta tafi, Salma ta ce “Gashi bani da kudi
sai dari biyun Yaya da ya ce in aje masa, bari dai
in debo miki biskit su Amira sa ke zuwa
Makaranta da shi.
Hadiza tace
“‘In kuma yazo yaga an diba fa?”
Salma ta ce, “Nawa ne ya sai min har da alawa, shi
baya cin irin su.
” Hadiza tayi dariya tar da fadin
“Yar gata
Ta saka hijabi da nufin raka Hadiza har bakin
titi. Hadiza ta ce “A’a babu ruwana, kin taba yin
rakiya ne?” Salma ta ce,
“Ban taba fita ko wajen
Gate ba, Allah ina son in fita
Suna cikin jayayya sai ga wata bakar mota.
Shatima ya fito wani abokin aikinsa ya kawo shi.
Ya fadada fara’arsa.
“Sannu da zuwa,
” Ta ce,
“Yauwa Alhaji.
Suka
gaisa. Ya ce
“Ba dai za ki tafi ba?”
Tace
“Wallahi zan tafi ne tun safe nazo.
” Ya ciro kudi a
aljihun wandonshi ya mika mata.
“Ga shi ki hau mota.
” Ta ce,
“Da ka bar shi.”
Yace
“A’a ki amsa, ni na ba ki.” Ta amsa tare da
godiya. Salma ta kalle shi, “Yaya zan dan rakata
titi.”
Ba tare da ya kalleta ba ya ce,
“A’a, ki koma
daga nan.
Ta tsaya cak! Ta mika ma Hadiza ledar
hannunta. Ta ce, “Ki ce ina gaida Inna, ki bata dari
biyar cikin kudin da ya ba ki.
.” Hadiza ta ce, “Ko
ba ki ce ba zan bata.
Ta koma daki ta same shi a cikin dakin bacci,
yana rataye suit din shi a jikin madubinta. Ya ce,
“Wato za ki fita ba izini ko?” Ta ce,
“Ban zaci
zaka yi fada ba. Yace
“To ko waye ya zo ban amince kiyi
rakiya gaba da Gate ba.
Ta ce,
“To Yaya, insha
Allahu.
” Nan ma ta dauko littafin rubutunta, shima
ta rubuta, har ya kalleta ya fito bandaki.
“Me ki ke yi da littafin?”
Ta ce, “Ina yin ‘yan
rubuce-rubucena ne yace
“Yana da kyau haka.
To me ki ka ba Hadiza din?”
•Ta kalle shi “Ai bani
da ko sisi, sai kudin ka dari biyun ka da ka ce in
aje maka.
Yace
“Kuma a dakin ba ki da abin bata?” Ta
girgiza kai tareda dan tabe baki,
“Me gare ni Yaya, na dai ba; Yaranta biskit dina, tunda shi ai
ka ce nawa ne ko?”,
Ya cc, “Eh.” Tace
“Ka ji abin da Ya Hadiza tace?” Ya tattaro hankalinga garè ta da tambayar.
“Me ta ce?”
Ta ce, “Wai in Rage siyan nama da
yawa sai in tara kudin, wai in sai kamar ,na dari uku nace sai na tambayeka in ka yarda
Yace to sauran kudin ayi me dasu? Wai in adana sai a siya min abinda bani dashi
Yace to ai ta baki shawara ne ni bani da matsala da haka in kina ra,ayin rage cin nama kina iya yin hakan tace na gode yaya•Yayi murmushi,
“Sarkin
godiya. Gobe za a kawo form na Makarantar, ki.
Ba ta san lokacin da ta buga tsalle ba har ta kai
inda ya ke ta kuma rungume shi, tana fadin
“Na
gode Yaya.
Yayi dariya,
“Ki samu nutsuwa in
fada miki.”
Ta durkusa a gabanshi,
“To Yaya na nutsu.”
Ya ce Makarantar a nan Unguwar take kusa da
titi, sannan maza ne da mata, in kin shiga ki kama
kanki bana son kiyi abota da wadanda ba za ki
karu ba, ki sa kai kiyi abin da ya kai ki.”
Salma ta ce Insha Allahu zan kiyaye.” Ya ce
“Ban ce musu ke matar aure ba ce, kin ga ke za ki