Rayuwar Mace

RAYUWAR MACE 3

RAYUWAR MACE
Hafsat Rano
Free Page (3)

Tun da suka dauki hanya suke masa shakiyance be ce dasu uffan ba, ya riga ya san dole suyi yadda ya dinga kuranta musu ita, ba karamin bata masa rai tayi ba ta kuma maida level dinsa baya a cikin abokan sa, ba dan ya kwallafa rai akanta ba babu abinda zai sa ya aureta dan shi baya son mace me duhun kai. Tsaki ya dinga ja har suka zo in da zasu rabu, ya sauke su ya fizgi motar kamar zai tashi sama sai gida.
   A falo ya tarar da Hajiyar da tarin akwatunan lefe tare da sisters dinsa su uku da suka je hado kayan, suna zaune suna dubawa ya shigo ransa a bace zai wuce Nadiya ta dakatar dashi

“Boy baka gammu bane?”

“Na ganku mana.” Yace yayi wucewar sa ya haye sama ya barsu da wagaggen baki.

“Ina ga dai an batawa boy rai, yadda yake zumudin auren nan ai ya tsaya ya ga komai.”

” Gaskiya dai, abun ya motsa.”

Fadila tace tana dariya

” Bari naje naji ko menene ya faru.” Nabeela ta mike Hajiya ta dakatar da ita

“Ku rabu dashi kila shi da abokan sa ne, zai sauko anjima kadan idan ya watsa ruwa.”

Komawa tayi ta zauna suka cigaba da maganar auren suna hada kayan da lissafin abubuwan da za’a siya kuma, Hajiyar na jin su tana amsa waya akai-akai Adam din ya sauko ya zauna a kusa da Nadeeya ya tankwashe kafar sa yana kallon kayan.

“Have a look, kayan wife din ka ne.”

Dan wara idon sa yayi akan kayan sai kuma ya dauke kai yana kallon Hajiyar

“Mah ba zai yiwu a dawo da bikin nan next week ba?”

“Next week kuma? Ai kamar yau ne upper week din Adam, hakuri zakayi a samu ayi shirye shiryen komai a nutse.”

Shiru yayi be sake cewa komai ba, ya ja baya ya jingina da kujera ya ciro wayar sa ya shiga chatting da yan matan sa, hakan ya saka shi manta abinda ya faru, har ya sake suka shiga hira da su kafin su tattara su tafi akan zasu dawo gobe saboda wasu kayan da basu gama siya ba.

***Tsaye Ya Hadiza take a kanta tunda ta shigo take kuka ta ki fad’a mata abinda ya faru, ita kanta ji take kamar tayi kukan dan ta san yanayin da Asma’un take ciki wanda ta taba shiga kusan irin sa Allah ya kiyaye Abba ya sakko aka daidaita, shiyasa take matukar tausayin ta dan mutum irin Adam ace shine mijinka ba karamin tashin hankali bane.

“Ki fad’a min abinda ya faru dan Allah, hankali na ba zai kwanta ba kuma wannan kukan sai ya saka miki ciwo.”

Bayan hannun ta, tasa ta share hawayen sannan ta hau ciro hijab din jikinta saboda zafi da hucin da jikin ta ke fitarwa. Duk Ya Hadizan na tsaye akanta har ta cire ta ninke sannan ta hau kokarin kakalo murmushi ta dora a saman jar fuskar ta.

” Wani abu yace miki?”

Da ka ta amsa mata tana jin wasu hawayen na neman zubowa.

” Karki yarda ki biye wa maganganun sa dan irin Adam xasu iya karar miki da hawayen ki tas babu abinda ya dame su. He’s not worth your tears, ki nutsu ki shiga kai wa Allah kukan ki, sai kiga komai yazo da sauki ta inda bamu zata ba.”

” In sha Allah.” Tace tana kwanciya.

     Fita Ya Hadizan tayi bayan ta kara bata baki, ta barta tana sakawa da warwarewa, ta riga ta san rayuwar ta tazo karshe, dan tana jin komai zai iya faruwa a zaman ta da mutum kamar Adam, bata san yadda zata kasance ba amma tana da yakinin zaman ba zai taba dadi ba.

    Shirye shirye ya kankama sosai a baangarorin biyu, ita Umma dai tana yin komai ne domin ya zama dole amma ba wai don son auren ba, sai dai bata da damar nunawa saboda Asma’un da Abba dan ba zata yarda ta bata kofar da zata bijire wa mahaifin ta ba. Satin ta guda ta dawo gida a lokacin ne aka shiga yi mata yan gyararrakin mata na al’adah duk da ba wani zafafawa akayi ba amma kuma dole dai zaka yi auren ‘yarka ka dan tabuka wani abu ko yaya.
    Komai baya mata dadi duk abinda ake mata kawai tana bi ne don babu yadda zata yi, saukin ta ma tun da yazo gidan Ya Hadiza be sake dawowa ba, sai magana da yayi mata a whatspp akan abinda take bukata tace babu, sai missed video calls dinsa da ta gani sau biyu bata bi ba, shikenan shima be sake bin kanta ba dama Nadeeya ce tace masa ana tambaya shiyasa ma ya tambaye ta, abinda tayi masa ranar yayi masifar bata masa rai shiyasa ya tattara ya watsar da ita ya cigaba da shirye shiryen sa dan babu fashi a auren dan yadda yake ji idan be aure ta ba akwai matsala.
 
Saura sati daya bikin suka kawo lefe, akwatuna goma cif masu kyau da tsada, tun daga nan hankalin ta ya kara tashi sosai, ta yarda da gaske dai auren babu fashi, babu abu daya da ya burgeta a kayan dan bata son duk wani abu da ya danganci Adam din, sosai take jin tsanar sa. Bayan an karbi lefen kowa ya watse su Ya Hadiza suka zauna zaman yi mata nasiha dan idan aka shiga satin bikin babu me sukunin zama yayi mata, jin su kawai take dan duk abinda suke fad’a bata jin zata iya yin guda daya, ita dai kawai ta riga ta san zatayi aure ne dan biyayya ga mahaifin ta.
    Da daddare kafin duk su watse sai gashi ya zo, gabanta ne ya fadi da taji Areef yace yazo, duk suka zuba mata ido tayi saurin zamewa daga zaunen da take ta kwanta kuka na taso mata.

“Tashi zakiyi kije, kiyi hakuri.” Ya Hadiza tayi maganar tana mikewa, tashi tayi daga kwanciyar, ta ja hijab dinta dage gefe zata saka ta girgiza mata kai

” Musulunci ma ya halatta mishi ganin wani abu sashe na daga gareki, ki saka mayafi dan Allah, sai ki dauki Hibba kuje.”

Bata yi mata musu ba, ta ajiye Hijab din ta karbi mayafin dake jikin kanwarta Rauda ta yafa, ta rik’e hannun hibba din suka fita, already ya shigo yana falon Abba shi da Abbaty da Yaya Ibrahim. Da sallama ta shigo duk suka juyo suna kallon ta, sannan suka amsa, murmushi yayi mata tayi kamar bata gani ba, ta samu gefe chan ta zauna sai suka tashi suka fita ya zama daga ita sai shi sai Hibba da ta makale a kusa da ita dan tana da kiwa. Tsam ya taso daga wajen zaman sa ya dawo kusa da ita, har tana jin kanshin turaren sa sosai, bata dago ba ta gaishe shi ya amsa yana bin ta da mayen kallon sa, riga da skirt ne a jikinta simple dinki amma tayi kyau sosai, fuskar ta fayau babu hoda sai yar rama da tayi akan ranar da ya ganta a kitchen.

“Fine baby, ya sunan ki?” Ya mika ma Hibba hannu ta noke yayi murmushi

“Madam ya gida?”

“Madam?” Tace a ranta

“Lafiya lou.” Ta amsa tana mummuraza yan yatsun hannun ta. Kallon hannun yayi, ya kai nasa hannun ya kama tayi saurin janye wa a tsorace ta kalle shi, a lokacin ta lura da shaddar dake jikin sa an masa karamin dinki iya guiwa kansa babu hula ya rage gashin sa sosai.

“Menene haka? Kamar kin ga wani dodo.” Ya tambaya cike da mamakin ta

“Ka daina taba ni.” Tace kai tsaye tana kokarin tashi daga kujerar yayi saurin fizgo mayafinta yana zaro mata idon sa.

“Me kike nufi? Aure fa zamuyi? Me yasa kike behaving kamar baki san yadda rayuwar ta zama bane, bana fa son kauyanci.”

Kallon sa tayi cike da mamakin sa, ta lura akan rayuwar da yake so yake ganin daidai ce nan da nan zaka ga fushin sa, ita kuwa ta gwammace duk abinda zai fad’a ya fad’a fushin sa ba komai bane akan fushin ubangiji. Tana jin sa ya cigba da gaggasa mata magana san ransa, tayi biris kamar ba da ita yake ba, tana da yakinin zafin zuciya ce dashi, kuma bakin sa bashi da control wejan gasa magana. Sai da ya gaji don kansa yayi shiru yana jan tsaki. Ya zaro wayar sa ya hau kira yana cigaba da huci akan kawai ta hanashi taba jikinta.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button