RAYUWAR MACE 4

“Menene wannan haka?” Ya fad’a muryar sa a dan tunzure, ta masa banza kamar bata ji ba, ta gwammace ya kashe ta idan ma kashe ta zai amma ba zata tanka masa ba, sake magana yayi da dan karfi, ta dago a tsorace taga yana wa hannun ta da kafarta kallon tsana.
“Bana son wannan abun da kika je akayi miki, karki kuskura kizo min gida dashi wallahi, ki san yadda za’a yi ki goge shi.”
A wani irin yanayi take kallon sa, mamaki na neman kashe ta, lallen yake nufin be sani ba, ko kuma me? Bata gama dawowa daga tunani ba, taji ya wurgo mata leda akan fuskar ta, tsinin takalmin dake cikin ledar ya buge ta, sosai taji zafi.
“Kayan da zaki saka ne a dinner din da friends dina suka shirya gobe, saura ki zubar min da girma na da aji na da kauyancin ki, ki tabbatar kuma kinje an goge wannan bakin abun na hannun ki, ina laifin ma ki saka nail polish ko kiyi fixing nail din ma , amma kiyi wannan abun irin na yan kauye, bana son shi bana son ganin shi kuma.”
Saroro tayi tana kallon sa mamakin sa na neman kashe ta, tashi tayi daga zaman da tayi, ta dire masa kayan a gabansa tace
“Bana bukatar kayan nan saboda ba zan je wajen ba, sai ka dauka ka kaiwa wadda take da wayewa daidai da taka, wadda ba zata baka kunya da kauyancin ta ba. Lalle kuma ba zan goge ba, tunda ba dan kai nayi ba, kuma hannu na ne da kafata ba ta wani ba, abinda naga dama shi zanyi.”. Ta murguda masa baki ta juya da sauri ta fice dan tasan tsaf zai iya gaura mata mari yadda taga yana huci. Kasa motsawa yayi daga wajen kamar wanda aka bigewa kafa, ya kalli kayan da ya kashe kudi masu yawa wajen siyansu amma ta watsar masa a wajen, sannan ya gaggaya masa magana yana tsaya har ta fita be fisgota ya nuna mata shi ba sa’an ta bane. Ransa ya kai kololuwa a baci, huci ya dinga yi kamar wani dan karamin zaki, sai ga Abbati ya shigo da yaga fitar Asma’un, kallon kayan dake kasa yayi ya kuma kalli fuskar Adam din, sai ya juya zai fita.
“Tsaya pls, wannan kayan ta manta su ka kai mata, ni zan wuce.”
“Owk.” Yace ya dawo ya dauki ledar suka fito a tare ya tafi shi kuma ya shiga ciki ya samu Rauda tana waya a tsakar gidan ya bata ya tafi.
***Daren gaba daya bata iya runtsawa ba, bata kara tabbatar da banzar al’adar Adam din ba sai a jiya, hakan ya tsaya mata a rai matuka har ta rasa irin tunanin da zatayi akai, tana jin yar hayaniyar wadanda basuyi bacci ba a tsakar gida suna aikin abinci har ta daina jin su kwata kwata, sai daf da asubah sannan bacci ya dauke ta cikin yanayin da ba zata iya misaltawa ba. Wajejen bakwai aka hau tashin ta kasancewar ranar ce daurin aure, ta tashi idon ta duk sun kumbura saboda rashin isasshen bacci. Shiryawa ya Hadiza tasa ta ta hau yi, babu um babu a’a ta hau shirya war, tana jin sanda su Abba da jama’ar da zasu tafj daurin auren suka tafi saboda a garin su Abban za’a daura Sumaila, ji tayi jikinta ya kara sanyi sosai. Ta zauna rik’e da kanta dake sara mata sosai, ko da aka kawo breakfast din sai ta kasa shi, jiya ma ashe dan ba taga anzo tafiya daurin auren bane har ta samu sukunin ci sosai. Babu yadda su Rauda basuyi da ita ba amma bata da nutsuwar da zata iya saka wani abu a cikin ta, lokaci kad’an sai ta duba agogon wayarta har sha daya tayi, jikinta ya kara saki sosai ta saddakar shikenan, shikenan ta shiga rayuwar da bata da yakinin samun kwanciyar hankalin ta.
Wajen karfe daya da rabi suka soma shigowa, kowanne su cike da farin ciki, farin cikin da yake daidai da bakin cikin ta, tana jin sanda wani kawun ta kanin umma yake fadawa matan tsakar gidan an daura, wata daga cikin su ta saki guda me karfi. A take taji kanta na wani irin juyawa, taga dakin na neman fado mata akai, bata san sanda ta fashe da wani irin kuka ba, su Rauda dake gefenta suka hau tayata dan dama karfin Hali kawai suke da kuma bin umarnin umma!