SARAN BOYE 76

No. 76
………….Gaba ɗaya gidan ya hargitse. Su Naser dai sunbi motar data ɗauki Yoohan a mota, sai dai babu tabbacin zasu iya cimmasu, musamman daya kasance dare ne.
Afrah da yake tazo wajen sunan ce tai azamar kiran Jay ta sanar masa, shima kansa hankalin nasa ya tashi matuƙa, amma sai ya shiga kwantar mata da hankali akan karta damu, indai da waya a jikin Yoohan gano inda ya ke abune mai sauƙi, ya kuma tabbatar a duk inda za’a kai Yoohan Deen na wajen insha ALLAH.
Suna yanke wayar yay kiran su Aliyu ya sanar musu. Tare da tura musu Number Yoohan dan yana son a bibiyesu da sauri kafin suyi tunanin yadda wayar a wani waje ko wani abu daban. Haka kawai a ransa ya kejin wannan aikin papa ne.
Lallai hikimar Afrah na saurin kiran Jay ya taimaka ainun. Dan cikin amicin ALLAH kuwa ta hanyar bibiyar wayar Yoohan ɗin da ke a jikinsa suka samu nasarar sanin inda aka kaisa.
_★
A ɓangaren Yoohan kuwa an shammacesa ne. Dan yana tsaka da firgicin jin cewa ba’aga Deen ba, da cewar Nu’aymah ta suma juwa ta nema kwasarsa. Yana dafe kansa kawai yaji an jasa ta ƙarfi an tura a mota, al’amarin kamar wani wasan yara. Suna sakashi a motar suka ɗora masa bindigu. Binsu kawai yay da kallo ɗaya bayan ɗaya ya girgiza kansa. Kafin yace wani abu ɗaya a cikinsu yace, “Indai kana buƙatar ɗanka a raye ka bimu salin alin”.
Guntun murmushi kawai yayi ya ɗauke kansa. Papa yana Nigeria kenan, dan a take ya gama fahimtar su ɗin yaran papa ne. A ransa yake tunanin shin da papa na buƙatar ganinsa sai ya bi ta hanyar sace masa yaro kenan? Minene amfanin yin hakan to?. (tsoron a kamashi mana) zuciyarsa ta raya masa. ‘To ashe kuwa shi da kansa zai damƙa papa a hannun huku yau ba sai gobe ba’.
Ganin baice komaiba yasa yaran ɗauka yayi ladab ne. A haka suka iso wani hotel. Duk maida bindugunsu sukayi a jiki daga su har Yoohan suka fito a motar. Yaji a ransa zai bisu kamar yanda suke buƙata. Sun shiga cikin hotel ɗin babu wani alamun rashin gaskiya tattare da su. Hasalima sun shiga a rarrabe ne. Yoohan tare da ɗaya a cikinsu, suma sauran biyun suka shiga su kaɗai.
Shi Yoohan sun wuce cikin hotel ɗin direct, sauran kuma suka tsaya reception kamar dai wani suke jira. Yoohan dai yanata bin hotel ɗin da kallon nazari har suka ƙarasa ɗaki mai lamba 23 vip section. Knocking ƙofar yayi sau ɗaya, sai ko gashi anzo an buɗe. da ido yayma Yoohan alamar ya shiga. Yoohan yay masa wani gajeren murmushi ya shige ɗakin, sai y bisa a baya yanayin ƙwafa. Dan yaji haushin murmushin Yoohan ɗin har ransa.
Ko kaɗan Yoohan baiyi mamakin cin karo da Momy a ɗakinba. Dan dama ai su zuciyarsa take raya masa gani ɗin. Ya kauda kansa daga kallonta saboda shegun kayan dake jikinta bata da maraba da tsirara. Takowa tai gabansa tana kwasar dariya da tafa hannaye ta shiga zagayesa.
Hannayensa kawai ya tura cikin aljihun wandon shaddarsa ya rumtse idanunsa. Sai da ta zagayasa sau kusan uku kafin tazo gabansa ta tsaya daf tamkar zata rungumesa. Ko motsi kuwa baiyiba, bai kuma buɗe idanunsa ba.
Cikin raɗan maganar shaƙiyanci da jin alfahari madam Chioma tace, “Abin mamaki ko my boy, haka muke ni da papanka kullum cikin bama mutane mamaki”. Sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya mai cin rai tana ja baya. Komawa tai bakin gado ta zauna tana wani lashe baki da banƙaro ƙirji. Tare da jan rigarta sama sosai cinyarta ɗaya ta fito waje idonta akan Yoohan da har yanzu nasa idanun ke a rufe. Cike da salon iskanci ta sake narke idanu tana lasar laɓɓanta.
“My boy karka takura kanka da tunani, dan baka buƙatar hakan musamman akan soyayyar jaririnka, oh sorry jikana nefa ashe”. Ta kwashe da dariya sanna ta cigaba da faɗin, “Yi haƙuri my boy na mantane. Ta hanya ɗayane kawai zaka iya cetar my grandson John. Dan nice kaɗai zan iya kaika inda zaka samesa. Hakan kuma bazata kasance ba sai ta hanyar biyamin buƙata ta. Hhhhhh My lovely john dolene fa na ɗanɗani zumar nan taka da kaketa min rowa, dan itace burina tun kana shekaru sha takwas a duniya. Hhhhhh kaga kuwa ai bai kamata nasha wahalar dakon lokaci ba, kaima nasan zaka tausaya min dear soooon”. Ta ƙare maganar da wani salon iskanci tamkar zatai kuka. Sai kuma ta taso zuwa gabansa ta tsaya tana matso hawayen da suka cika mata idanu.
Hannayenta ta ɗora akan ƙirjinsa ta fara ɓalle maɓallin shaddarsa tare da cigaba da faɗin, “Karka damu duk ma na yafe maka wahalhalun dana sha a waɗancan shekarun kaji baby. Dan wannan daren kawai ya wadatar da cike gurbin duka sauran dararen da suka shuɗe”.
Duk wannan iskanci da madam Chioma keyi Yoohan na tsaye tamkar gunki, har yanzu idanunsa a rufe. Sai da takai ƙarshen duka maɓallansa tana sambatun haukan zantukanta, ta tura hannunta cikin rigar ta fara shafa ƙirjinsa ta saman singlet ɗinsa. Wani irin cije baki yayi ya hankiɗata baya da iya ƙarfinsa.
A take ta saki wani irin wahalalliyar ƙara saboda da gaske ta bugu. Da sauri yaran da suka kawosa wajen suka zagayesa da bindugu. Buɗe idanunsa dake a matuƙar jazur yayi akansu, ya wani ɗauke kai irin ba kune a gabana ba ya maida kan madam Chioma dake kwance ƙasa wanwar tana numfashi da ƙyar saboda azaba.
A hankali ya fara takawa gareta fuskarnan kanta tayi jazur kai kace aman wuta zatayo. Suko yaran madam Chioma na biye da shi da bindiga abin nasuma abin dariya.
Ƙafarsa ya taka a samna gadon ya ranƙwafo kanta. Wani murmushin tsantsar tsana ya jefeta da shi tare da nunata da ɗan yatsa. “Na tsaneki, har cikin raina na tsaneki, tsana irin wadda ban taɓama wani mahaluki ita a wannan duniyarba. Indai nine zaki mutu da takaicin rashin samuna har ƙarshen numfashinki. Nayi takaici mai yawa akan kasancewarki mahaifiya a gareni. Bakuma zan taɓa yafe miki ba har abadan tunda ke karya ce wadda sam bata da zuciya a ƙirjinta balle ƙwaƙwalwar tunani. Badan ke uwata bece da yau na tabbatarma duniya ke ɗin dabbace, a cikin dabbobinma kina jerin aladu dan sune basu banbance junansu wajen neman kansu. Wlhy kinji na rantse ko tabon ƙwarzane na samu a jikin yarona saina halakaki da wannan hannun nawa”. Ya kai ƙarshen maganar yana wara yatsun hannunsa da jujjuyasu akan fuskarta.
Da gaske tsoro ya shigi Madam Chioma, dan tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin irin wannan fusata da fushin na Yoohan ba. Tsaye ya miƙe yana zuba mata wani mummunan kallon tsana da ƙyama.
Da sauri ta zabura ta miƙe duk da azabar da bayanta ke mata. Tace, “Ku ɗauremin shi, wlhy koda ƙarfi saina lashi zumarka John. Kaje kaita tsanar tawa kai ya dama wannan kuma, ni ban tsaneka ba. Ba kuma zan tsneka ba”.
Kafin Yoohan yay wani yunƙuri kuwa suka dabaibayesa da igiya, duk yanda yaso kuɓutar da kansa ya gagara hakan sam, dan tsam suka ɗauresa a tsaye sannan suka kamashi suka ajiye a kujera suka sake ɗaurewa suna dariyar yanda sukaga yana wani irin huci na zafin zuciya.
Itama kanta Madam Chioma dariyar take tayasu da iya ƙarfinta. Ta tashi tsaye da ƙar tana riƙe ƙugu. Gabansa tazo ta tsaya tana cije baki. “John kana wasa dani ko? Na fika hatsabibanci yaro. dan tunkan asan za’a haifeka nake da taurin kai. Ai tunda nayi alƙawarin saina cikama rayuwata”.