Labarai

Rayuwata na cikin hadari a gidan yari, Abba Kyari ya shaidawa kotu

A ranar Alhamis din yau ne Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar ya garzaya wata babbar kotun tarayya domin neman karin beli.

Abba Kyari da mutun uku da ake tuhumarsa, ta bakin lauyansu, sun bukaci mai shari’a Emeka Nwite da ya amince da bayar da belinsu saboda rayuwarsu a gidan gyaran hali yana cikin hadari na premiumtimes ta rawaito.

A ci gaba da zaman, Onyechi Ikpeazu (SAN), lauya ga abba Kyari da kuma dakatar da ACP Sunday Ubia, ya sanar da kotun cewa an shigar da bukatar neman belin wadanda ake kara na 1, 2, 4 da 5, kuma an shigar da su a kan dokar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa. (NDLEA).

Ya ce bukatar ta zama dole saboda yanayin aikin da wadanda ake tuhumar suka yi a aikin ‘yan sandan kasar.

Mista Ikpeazu ya ce ana ci gaba da tsare wadanda ake tuhuma tare da masu aikata laifuka a gidan gyaran hali, wadanda kokarin wadanda ake kara suka yi ya sa aka kama su.

Babban Lauyan ya ce rayukansu na cikin hadari, don haka, a karbi bukatar belin su.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an dakatar da jami’an ‘yan sanda hudu da suka hada da ACP Ubia, ASP Bawa James, Insfekta Simon Agirigba da Insp. John Nuhu, wanda aka lissafa a matsayin na biyu zuwa na biyar da ake kara, hukumar NDLEA na tuhumarsu da laifin safarar miyagun kwayoyi tare da abba Kyari.

Sai dai a yayin da Messrs Kyari da Ubia da Agirigba da Nuhu (masu kara na 1 da na 2 da na 4 da na 5) suka nemi a bayar da belinsu kan zargin barazana ga rayuwarsu, ASP Bawa James wanda shi ne mutum na uku da ake tuhuma kan lamarin bai yi nasara ba.

A halin da ake ciki, Lauyan masu shigar da kara (NDLEA), Sunday Joseph, ya ki amincewa da bukatar neman belin, inda ya dage cewa an shirya yin nazari kan gaskiyar wadanda ake tuhuma na shida da na bakwai wadanda suka amsa laifin da ake tuhumar su da su.

Chibunna Umeibe da Emeka Ezenwanne (Masu tuhuma na 6 da na 7) su ne wadanda ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi a filin jirgin saman Akanu Ibiam da ke Enugu.

Messrs Umeibe da Ezenwanne sun amsa laifuka biyar, shida da bakwai sun fi son a tsare su a gidan yari na Suleja.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button