SADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

Wai rigiji gabja din fah kenan shi kansa sarki Darraju abin kallo nehh sabida ya kasance tafkeke mai kirar mutanen farko yana kira irin ta manyan sadauki kuma ya kasance jarumi mai tarwatsa maza a filin daga wata zabgegiyar takobi ce daure a kugun sa tana mai fitar da jan haske gabaya kaf jikin sa gurayen tsafin sa nehh,
Daga gefen daman wani dan saurayi nehh wanda shekarun sa bazasu Haura na wannan saurayin na Daji ba saurayin yana sanye da kaya na alfarma shima ya kasan ce ya tamke fuska nehh tamkar bai taba Dariya ba a duniya lalle kam kyan da ya gani uban sa YARIMA MANGUL kenan daga sarki Darraju sarki Darraju yana matukar ji da yarima mangul sakamakon bishin da yayi aduk wani bakin hali nasa kuma shima ya gani uban sa a sadaukan taka da karfin zalunchi
Daga bangaren hagun sa kuwa kyakykyawar yarinya ce yar kimanin shekara uku a duniya tana sanye da kaya irin na sarauta da alfarma ta kasance kyakykyawa ta gaban kwatance haka ba abinda ya rabasu da yarima mangul sakamakon tsananin kamar da suke da juna GIMBIYA LAMRITA kenan ibn DARRAJU
Wadannan sune yayan sarki Darraju wadannan yafi jii dasu aduk duniya amma yafi ji da yarima mangul sakamakon yana taimaka masa abisa harkallar da suke yi tare da dan nasa
Ba wata harkallah bace bace bataucin bayi da Kuma farautar bayin a kaf fadin duniya ba wanda baisan sarki Darraju ba haka kuma duk birnin da yaga dama zai shiga yaje ya yaki garin ya kashe kowa ya kwaso dukiya mai dunbin yawa
Hakan nehh yasa kowanne birni ke tsoron Kuma suke yi masa biyayya dan dole badan sunso haka duk shekara sai sun biya haraji idan ba haka ba kuwa yanxun nan zai yi hawa shi kadai ya zo ya rushed birnin gaba daya a duniya ba abinda sarki Darraju ya rasa amma duk da haka sai yayi wannan barnar yake jin dadi
Bayan haihuwar yarima mangul nehh sarki Darraju yayi matukar farin cikin da ganin sa dan yasan ya samu magaji haka kuwa akayi din dan duk wani hali na sarki Darraju saida yarima mangul ya dauko shi sai dai shi har ma ya fishi zalinci da cin zarafi idan ya fita farauta shi bayan ya rushed gari da komai idan macece sarauniyar a gaban jama’ar ta zai yi mata fyade ya kashe t idan namiji nehh muddin yanada ya mace to akan idanun sa zai keta mata haddi sannan ya kashe ta a gaban Babban ta sannan ya kashe uban NATA ya kwaso ganima
Wannan dabi’a ta da da uba tana damun mutanen birnin Hindu amma ba yarda zasu yi dasu dole su hkr dan koh suma basu tsallake tarkon yarima mangul ba muddin ya kyalla ido ya hango yarka to fahh a ranar saita mutu bayan gama biyan bukatar sa da ita ………….
Wannan kenan gsky naji dadin son da kuka nunawa wannan book din nawa sannan naji dadin comments dinku Yan uwa da abokan arziki ALLAH yabar zumunchi ameen thumma ameen
Vote
Comments and shared
WhatsApp number 08143314152
By fast class
????????????????????
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
????????????????????
Writing by
ALIYU H ISHAQ
(fast class)
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
DAGA MARUBUCIN
UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
And now
↙
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
???? 10↔15
Dedicated to A T K PALACE GROUP
…………..Al’amarin wannan saurayi dashi da yar jaririyar kanwarsa kuwa lokacin da ya shiga cikin wannan kogo mai zurfin bala’i har ya samu damar kaiwa karshen sa ya fadi kasa sumamme bashi ya farka ba sai bayan sa’a daya da rabi yana farkawa ya shiga laluben bayan sa jin da yayi wayam Alamar ba kanwarsa nehh ya matukar daga masa hankali biye da ko yaushe
Kawai sai ya Mike zumbur ya kama waige² yana Neman inda take
Chan ya hangota kan wani dan karamin gadon karfe na alfarma tana kwance ga madara nan a kusa da ita da alama an bata madarar
Zuciyarsa ce nan tayi masifar bugawa hankalin sa ya kai koluluwar tashi tsoro ya darsu a ransa
A hankali yake matsawa kusa da gadon yana mai waige² gani yake yi ako da yaushe wani abun zai iya bayyana ya illatashi a hakan ya kusa kaiwa bakin gadon kenan kwatsam ba zato ba tsammani sai jin wata murya yayi ta cika kogon baki daya tana fadin
Lalle marhabun da sadauki uban sadaukai jarumi uban jarumai fasa taro SADAUKI RAZMIR IBN HAWWASHA
Ya kai Razmir ina son ka saki jikin ka tamkar kana dakin baccin ka dan idan kana nan ba wani mahaluki daya isa ya ganka balle ya kamaka ya kai Razmir kasani cewa yau shekara 20 kenan ina cikin wannan kogon dutse ina jiran zuwanka
A matukar tsorace Razmir yake fadin “shin waye kai kuma mene nufin ka na jirana acikin wannan kogon har na tsahon kimanin shekaru 20 wanda a lokacin nan ma banzo duniya koh da Razmir yazo nan a zancen sa sai ya dan saurara yana jiran amsar tambayoyin sa
Ji yayi an kece da wata mahaukaciyar Dariya wadda take barazanar kashe masa dodon kunne daga bisani kuma sai yaji dariyar ta koma kuka sai da suka kusa rabin sa’a acikin wannan yanayi nehh sannan wannan mutumin da nima bansan ko waye ba ya ya tsagaita da kukan da yake yi
Zuwa wani dan lokaci dan Razmir yaga wani tsohon mutum ya bayyana a sama fuskarsa cike da hawaye tsohon yana ruke da wata farar SANDA a hannun sa sandar tana fitar da farin haske Wanda ya gauraye kogon baki daya
Fuskar tsohon cike take da gashi tako ta ina kallon Razmir yayi sannan yace” da farko dai sunana BOKA SALSALUL NUM ni haifaffen birnin rum nehh
A shekaru 20 baya lokacin sarki darraju yana kan ganiya zaluncin sa yarda ya keso to shine ya kawo wa birnin mu ziyara ta bazata saida ya kashe kowa da kowa na birnin sannan ya tunkari gidan sarautar birnin a wannan lokacin sarauniyar dake mulkar mu tana dauke d tsohon ciki bazata iya yaki ba shine ta samu aka kirawo ni bayan mun kadaita nehh take cewa
Ya kai abin dogaro kasani cewa tun kafin wannan masifah ta afko mana nariga nagani a mafarki ni a yanxun burina daya nehh nasan bazan rayu ba a wannan rana amma ina matukar San abinda zan haifah ya rayu dan ya gaji karaga kuma nayi bincike na gano cewa kaf cikin birnin nan kai kai nehh zaka iya bashi kariya yarda ya kamata har ya rayu ya kai munzalin da ake so a rayuwa
Daga yau daga yanxun na dam ka maka amanar abinda zan haifah
Tana kaiwa karshen wannan furuci NATA nehh nakuda ta kamata amma abin mamaki mai makon tayi kuka sai murmushi ya bayyana akan fuskar ta
Da sauri na fita na samo wasu kuyangi suka taimaka mata nikuma na fita chan filin fadar inda dakarun mu ke fafata kazamin yaki da sarki darraju shi kadai ya zame musu tamkar shaidani duk inda yasa gaba saidai kaga kawunan bil’adama na shawagi a sama
Wannan abun shine yasa raina yayi mugun baci cikin bakin zafin nama na zare sandar tsafina nayi kansa da mugun gudu ina mai kwallah ihu ina isa na shammace shi na dankara masa naushi a kirji saida yayi juyi biyu a tsaye sannan ya durkushe yana tashi muka kachame da masifaffen yaki sai da MUKA kwashi sa’a hudu muna kwabzawa amma dayan mu bai sani wata nasara ba dan haka da naga wankin hula yana Neman ya kaini dare nehh yasa na shammace shi na make kafar sa ya durkushe kafin ya Ankara na bace