HAUSA NOVELNOVELSSADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

SADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

Ban bayyana ako ina ba sai a turakar sarauniya ina isa naga ta haifi ya mace amma ita ta mutu ba karamin bakin ciki nayi ba haka na dauko wannan yarinya MUKA bar birnin

 

 

 

Shiko sarki darraju koh da yaga sarauniya ta mutu sai ya nuna wa mutanen birnin suyi mubayi’a koya kashe su nan suka mika wuya ya Nada wani Babban hadimin sa mai irin halinsa akan karagar mulkin

 

 

 

Bayan wasu kwanaki nehh muna zaune nida wannan jaririya ina shayar da ita da madarar shanu itama hadimai na na aljanu nake sawa su kawo min kullum bayan tasha ta koshine naji Alamar tafiya a bayana

 

 

Nan take na dauki wannan jaririya na shige cikin bukkata na hada komai nawa nan take MUKA bace bat

 

 

Bamu bayyana a ko ina ba sai a karshen wannan Daji dake yamma da birnin rum anan nehh na yi bincike akan wadanda suka kawo mana nan naga dakarun sarki darraju nehh suka kawo min hari dan su kamani su kaini gunsa dan tun sanda MUKA fafata dashi ya kasa kashe ni yake kyankyamin kansa yace dole sai an kawoni ya kasheni

 

 

 

Koh da naga haka sai na shiga binciken mafita dan bazan iya tunkarar birnin Hindu da yaki ni kadai ba dan haka na shiga Neman mafita ban jima ina binceke ba a madubin tsafina na gano cewa banda wata mafaka inba cikin wannan kogon ba nan kawai xan shiga na tsira da rayuwa ta data wannan yarinya sannan idan ina cikin sa nan da shekara daya za a haifi wani yaro acikin birnin Hindu wannan yaron shine zai wanzar da adalci a wannan nahiya baki daya kuma shi kadai nehh zai iya Mayar da wannan jariri ya daya sawa suma NUMAIRA kasar ta ta haihuwa har ya cika burin mahaifiyar ta

 

 

 

 

Koh da naga haka sai na shiga binciken inda zan ganka acikin birnin Hindu bayan kazo duniya nan fahh Abu yaci tura sai a karshe nehh na gano cewa Indai ina Cikin wannan kogo kai da kanka zaka kawo kanka har inda nake kuma a sanda xakazo da Neman taimako zakaxo guna,,

 

 

 

 

Wannan shine lbrn na yanxun kasan koni waye sannan ina mai gabatar maka da gimbiya NUMAIRAH tsoho salsalul num ya fadi haka yana mai nuna wani bangare daban da hannun sa

 

 

 

 

Wata kyakykyawar budurwa ce ta fito ta gaban kwatance komai NATA yayi dai dai da tsarin jikin ta shi kansa Razmir sakin baki yayi yana kallon ta

 

 

 

Itako koh kallonsa batayi ba ta huce gurin boka salsalul num tana mai fadin gani ya kai abbana akwai abinda kakeso nayi maka nehh yanxun

 

 

 

 

Dafa kanta boka salsalul num yayi yana fadin babu komai yata bakin da muketa jira nehh sahon shekara 20 yau gasu sun bayyana kansu

 

 

Sai a wannan lokacin ta lura da Razmir da kuma wannan jaririya dake kan gadon ta sai wasan ta take

 

 

 

Kallon kallo suka tsaya yi itada Razmir acikin su an rasa Wanda zai dauke fuskarsa daga cikin su kowa da abinda yake sakawa a ransa……….

 

 

 

 

Wannan kenan ni kam nafi tunanin tafiya lbr ya kare yanxun ZAMU shiga cikin gundarin lbrn dan haka kubiyoni muje zuwa ni iya comments dinki kawai nake bukata

 

 

 

Vote
Comments and shared

 

 

 

WhatsApp number 08143314152

 

 

 

By fast class
????????????????????
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
????????????????????

Writing by

ALIYU H ISHAQ
(fast class)

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

DAGA MARUBUCIN

UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
And now

SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)

 

???? 15↔20

 

 

 

 

………bayan wadansu dakiku nehh gimbiya Numaira ta dauke kanta daga kan na sadauki razmir sannan ta kalli boka salsalul num tana mai yi masa murmushi batare da tace wani Abu ba ta tafi da sauri ta dauki wannan jaririya dake kan gado ta fara mata wasa

 

 

 

Hakan ba karamin dadi yayi wa Razmir ba nan take yaji sanyi a ransa

 

 

Kamar daga sama yaji maganar boka salsalul num yana fadin “ya kai Razmir shin zaka iya fadamin abinda kayi wa wadannan dakaru na sarki Darraju har suke binka

 

 

 

Koh da jin wannan tambaya sai idanun Razmir suka cika da kwallah kana ya kalli wannan tsoho yace ” ni dai tunda na taso acikin Daji naga iyayena anan na girma babana mafarauci nehh amma koh kadan bayaso na gajeshi duk SANDA nayi masa batu akan ya koya min yaki da yadda ake farauta sai ya dafah kaina yace

 

 

Ya kai Dana kayi sani cewa nayi bincike akan alkaluman taurarin ka nagano cewa har abada bazaka taba gada ba idan zan shekara dubu ina koyama farauta bazaka Iya ba balle har ka gajene

 

 

 

Kasani cewa ina hango mutuwa ta nan kusa tare da mahaifiyarka dan inaji a jiki na mun kusa rabuwa dakai dan akwai wani babban al’amari dayake tun karo rayuwarka Kuma wannan al’amarin shine zai yi silar mutuwa ta nida mahaifiyar ka sannan ina mai tabbatar maka ni farauta ba gadar ta nayi ba a bisa dole nakeyin ta dan mu rayu da ni da Ku yana kaiwa nan naga ya fashe da kuka

 

 

 

Nan na shiga rarrashin sa amma saida yayi mai Isar sa sannan yayi shuru ya kalleni yace”ya kai Razmir kasani cewa na boye ma abubuwa da yawa acikin wannan DUNIYAR amma da sannu zaka sani bayan bana raye yana kaiwa nan ya tashi ya shiga yar bukkar mu sakamakon nishin da yaji ammina tanayi dan dama tana dauke da cikin wannan jaririya

 

 

 

 

Bayan wani dan lokaci nehh nafara jin kukan jariri na tashi daga cikin bukkar nan ba karamin farin ciki nayi ba dan banda burin da ya wuce naga kani na koh kanwata ba a Jima ba saida abbana ya tare da wannan kanwa tawa a hannu yana zuwa ya damkamin ita a hannu yana hawaye sannan yace”ya kai dana wannan itace kaddarar ka a wannan duniya sabida haka inason ka tafi da wannan yarinya wani wajen kuje ku rayu kasani cewa a yanxun hakan nan dakaru sun xagaye wannan guri da miyagun makamai dan su kashe mu kayi amfani da baiwarka gurin tsira da rayuwarka nasan zaka iya yana fadin haka ya karbeta ya daureta a bayana sannan ya miko min guziri yace na tafi

 

 

 

Kasa motsawa nayi na tsaya agu daya ina hawaye ina kallon sa ban Ankara ba naji wani Motsi mai yawa ya cika da jin wata Uwar tsawa Abbana ya buga min yana mai bani umarnin na tafi

 

 

Ban yi wata wata ba na yanki hanya na run tuma da azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya ban jima ina gudu ba nafara jiyo kururuwar iyayen mu suna ihu bayan wani dan lokaci kuma naji shuru nan take kwallah ta fara zubo min dan nasan na rabu dasu har abada baki daya

 

 

 

Ban gushe ina gudu ba har saida na iso birnin Hindu anan na ci gaba da rayuwa har tsahon wata uku ina shayar da wannan kansa tawa da har yanxun ban sa mata suna wata Rana ma saina sha duka kafin na samu abinda zan bata taci nasha wahala sosae kafin zuwan wannan rana da na kwaci gurasa a hannun badakaren sarki darraju suka biyoni nasha dakyar a hannun su,

 

 

 

 

Kwalla ce ta cika a idanun boka salsalul num saida ya zubar da kwallah kana daga bisani ya kalli Razmir yace”lalle kaga rayuwa Dana to kasani cewa wadannan dakarun da suka kashe iyayen ka ba kowa ya tura su ba illah sarki Darraju kasani cewa da chan baban ka shike mulkin birnin Hindu wato SARKI HAWWASHA sarki nehh mai adalci da kyautatawa talakawan sa Darraju ko bawansa nehh wanda ya amince dashi Dari bisa dari yaudarar sa yayi wata rana bayan an haifeka mahaifiyarka ta koma gida wanka tsakanin birnin Hindu da birnin su tafiya ce ta kwana daya da yini daya to a ranar da zata dawo nehh sarki hawwasha yace shi kadai zaije ya taho da ita shine ya bar Darraju a matsayin wakilinsa to dama Darraju yana da shirin sa nayin juyin mulki to ga dama ta samu kawai sai yayi amfani da wannan dama ya kashe duk wani babba a garin ya dare karaga a ranar da sarki hawwasha ya dawo ya sami lbr sai yaki shiga birnin kuma yayi Dana sanin yarda da Darraju da yayi Daji ya koma Ya kafa tantinsa daga ranar ya koma mafarauci yana badda kama ya kai birnin Hindu a siya ya sayo kayan abinchi wannan shine lbrn da abban ka yake boye ma Kuma dalilin sa nakin koyama farauta ba komai bane illah burinsa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button