SADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

Bokan sa ya tabbatar masa da cewa Kaine zaka kawo karshen mulkin zalunchin sarki Darraju lokacin da yaji haka sai yayi yunkurin sanar da kai komai amma sai bokan sa ya hanashi yace idan ya fada ma bazaka taba yin nasara akan sarki Darraju ba akwai lokacin da zaka sani da kanka Kuma gashi kasani yau dan haka sai ka shirya,
Cikin rashin fahimta ya kalli boka salsalul num yace”ya shugabana to taya zan iya tarar wannan azzalumim sarki alhalin ni ban kasance jarumi ba
Boka salsalul num ya kalleshi sannan yace”daga yau zam fara baka boron yaki iya kar iyawa ta bayan ka samu horo mai kyau kafin nan yar uwarka ta girma sai ka dauki gimbiya numaira ku tafi birnin sin domin ka sadu da BOKA MUTSULUL GAYUSH kasani cewa duk duniya ba wanda yake da karfin sihirin tsafi irin na boka mutsulul gayush zaka he ka zama yaron sa na mako daya a sannan neh zaka sami horo irin nasa kasamo cewa a hangar zuwa birnin sin akwai wani gwaggwan biri mai shekara dari uku a duniya kasani cewa a shekara arba’in baya ba a Kuma samin mahalukin daya ratsa wannan Daji ya shiga birnin sin ba a Raye kasani cewa dole saika kashe wannan gwaggwan biri sannan burin ka zai cika
Bayan nan kuma zaka tunkari birnin KUFA dan ka sadu da SADAUKI DARBUZA masana da masu bincike sun tabbatar da cewa ba wani mahalukin daya kai sadauki darbuza karfin dantse a dniya sai mutum daya ba kowa bane wannan mutumi ba face sarki Darraju nan ma acikin mako daya zaka gama komai ka huce gaba
Sannan a hanyarka ta zuwa birnin kufa acikin wani kungurmin daji akwai wata muguwar macijiya mai kawuna arba’in sama da shekara goma ba wani mahaluki daya taba ratsa dajin nan ya huce lpy saidai gawarsa
Bayan nan a gabas da birnin damaska akwai wani karamin kauye mai suna GURGUN acikin wannan Kauye akwai wata gawurtacciyar mayakiya mai suna MURHALU masana da masu bincike sun tabbatar da cewa a duk fadin duniya ba mayakin daya kaita iya sarrafa takobi
Haka a hanyar ka ta isa birnin damaska akwai wani rukakken zaki daya tare hanyar nan sama da shekara Biyar an daina shige da fice acikin wannan birni dole saika yaki wannan zaki ka kashe shi sannan zaka sadu da jaruma MULHALA
koh da jin wadannan batutuwa sai idanun Razmir suka zazzaro zuciyarsa ta buga amma daya tuna da mahaifan su sai yaji zuciyar sa ta keka she ga barin jin tsoro nan take yaje ya daga kan kanwarsa yana mai fadin
Na rantse da wannan kansa tawa koh zan rasa rayuwata saina cika burin mahaifina…………
TOM YANXUN FAHH AKA FARA FADAN BA A SOMA KOMAI BA FANS GSKY INAJIN DADIN COMMENTS DINKU ALLAH YA BAR KAUNA
Vote
Comments and shared
WhatsApp number 08143314152
By fast class
????????????????????
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
????????????????????
Writing by
ALIYU H ISHAQ
(fast class)
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
DAGA MARUBUCIN
UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
And now
↙
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
???? 20↔25
……….Kamar yarda boka salsalul num ya fada haka al’amarin ya kasance wato shi da kansa ya fara bawa Razmir horon yaki mai tsanani a kullum idan suna horon nan sai ya suma sau bakwai amma daya farfado ya tuna da mahaifan sa sai yaji zuciyarsa ta keka she ga barin jin tsoro nan take zai zage kwanji
Ta guri daya Razmir ya ke samun saukin wannan horo shine ta gurin gudu indai anzo fagen gudu to shi gwani nehh dan yana iya shafe kwana arba’in yana gudu ba tare da ya nemi abunchi ba shi kansa boka salsalul num yayi mamakin wannan baiwa tasa sabida a lokacin da yazo bashi wannan horo suna kasa tsere kan kace wani abu Razmir ya bashi rata mai yawa ta yarda bazai iya kamo shi ba
Haka al’amura suka ci gaba da tafiya inda Razmir yake karban horon a gefe daya kuma ga yarima mangul da zaluncin sa ya Kuma shahara a kasashen duniya dan yanxun ma kasa kasa yake turawa indai aka ga yarinya mai kyau sai a dauko masa ita a kawo masa shikuma da yagama amfaninsa da ita zai kasheta dan shi bayason magaji a rayuwarsa
Idan ko aka Nuna masa yarinya ya nemi ta taki to fahh har birnin su xai dauki runduna suje ta jawa yan birnin koh sun kai su million sai ya kashe su zai dauko ta a gurin zai keta haddin ta ya kashe ta ya debo bayi da ganima ya taho gida
Ta kai ta kawo shi kansa Darraju abin yana matukar damunsa yana son ya hanashi abinda yake yi amma baya son bacin ran dan nasa dan haka ya kyaleshi yayi duk abinda yake so sabida yana kawo makudan kudade cikin kasar sannan yana kawo bayi kosassu wadanda idan aka sai da su za a sami riba mai yawan gaske
Yarima mangul nehh zaune acikin turakar sa yana wa yar kanwarsa wasa wato gimbiya lamrita dan yana son ta sosae wani badakaren sa nehh ya shigo mai suna dufan yana shigowa ya zube ya kwashi gaisuwa
Dagowa yayi ya kalleshi sannan yace”an gaisheka dufal jarumin jarumai kuma amin tacce na shin akwai wani kamun nehh
Cikin biyayya dufal yace”kwarai da gsk ya shugaba sunan ta shamril anan yamma da wannan birni namu mai albarka take cikin birnin damjul ranka ya dade sai dai itace sarauniyar birnin shugabana
Cikin izzah yarima mangul ya dago ya kalleshi yace to dan itace sarauniya sai me kawai kaje mata da bukata ta idan taki nayi aikina
Cikin biyayya dufal yace an gama ya shugabana yana kaiwa nan ya Mike ya fita
Bayan kwana daya ya dawo wa yarima mangul da mgnr sarauniya shamril akan taki amincewa da bukatar su
Cikin matukar fushi ya dauki takobin sa ya five daga turakar tasa dufal ya rufah masa baya kai tsaye burgar dawakai ya nufah tun kafin ya karaso aka daurawa doki siddi yana zuwa ya haye ya sakar masa linzami
Shima dufal baiyi wata wata ba ya rufah masa baya kai tsaye birnin damjul ya nufah kafin faduwar rana ya isa
Suna isa suka hau mutanen garin da Sara da suka cikin bakin zafin nama juriya da bajinta cikin kankanin lokaci ya gama da duk wani badakare na garin ya kama bayi da barori kai tsaye suka nufi gidan sarautar inda anan ma sun gwabza kazamin yaki mai muni yarima mangul bai bar kowa ba acikin wannan masarauta ba illah gimbiya shamril daya kama ta ya sata acikin bayi suka baje garin sannan sika tiso keyarsu Zuwa birnin Hindu
Bayan sun iso nehh yasa aka kai masa ita turakar sa a ka’idar yarima mangul sai ya buge mace ta suma sannan zai biya bukatar sa da ita hk kuma bokan sa ya tabbatar masa da cewa duk SANDA ya daga hannu da niyyar sumar da mace ya kasa to alkadarin sa ya karye burin sa ya karye dan sai ta haifah masa magaji
Bayan ya gama komai nasa nehh da dare ya shiga turakar sa a aure ya sameta kamar yarda suka jefah ta turakar kai tsaye kanta ya nufah tana ja da baya har ta kai bakin makeken gadon sa cikin zafin nama yasa hannu da nufin ya mangareta amma sai ya tsaya chak kome ya tuna
Ji yayi ta fashe da Dariya saida tayi Mai Isar ta kana ta hade rai tana fadin yarima kenan ka sani cewa ka shiga komata dan haka ina mai sanar da kai ni shamril saina tozarta ka kamar yarda ka tozarta sauran yan uwana mata ciki koh harda yar uwata rabin jikina kasani yanxun nehh lokacin daukar fansa a kan ka ina mai farin cikin sanar da kai daga yau daga yanxun duk wani sihirin tsafin ka ya daina aiki sabida haka sai kayanke wa kanka shawara mai kyau