HAUSA NOVELNOVELSSADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

SADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

 

 

 

Koh da yarima mangul yaji kalaman ta sai yaji zuciyarsa ta kama tafarfasa ransa ya baci da sauri ya zare takobi da nufin ya datse mata kai amma sai ganin takobin yayi ta ratsata ta wuce kamar haske bata mata komai ba

 

 

Koh da ganin haka sai shamril ta kyalkyale da mahaukaciyar Dariya sai da ta kai Rabin sa’a tana wannan Dariya sannan ta kalleshi tana mai fadin lokacin daukar fansa yayi a kanka

 

 

 

Rasa abinda zai yi yayi kawai sai ya ruke kansa dayake juya masa chan kawai sai ya shammaceta ya riketa da karfi ya kwantar da ita ya biya bukatar sa da ita tana kallonsa bata hanashi ba haka ya tashi cikin izza ta kalleshi tace ni yanxun idan ka barni ma bansan inda zanje ba dan banda kowa a wannan duniya sabida haka ka sani indai nabar gidan sarautar nan to sai nna watsa lbrn ka duniya na ka xama kolo wanda koh mace bazai iya kashewa ba

 

 

Cikin tashin hankali ya kalleta lokaci guda idanunsa suka cika da kwallah ya kalleta yace ki xauna tare dani a cikin nan amma kada ki bari kowa yasan dake

 

 

Tashi tayi tana fadin da dai yafi ta wuce shi yana tsaye ya saki baki yana kallon ta,,,,,

 

 

 

 

A bangaren sadauki Razmir kuwa bayan wata bakwai ya kware ya zama gwani dan shi kadai idan ya fita daji yanxun yana iya yakar rukakkun zakuna guda hudu a lokaci guda ya kai su kasa

 

 

Shi kansa boka salsalul num sai yayi da gsky yake iya kaishi kasa a wannan lokacin nehh boka salsalul num ya kalli sadauki Razmir yana mai fadin “ya kai Dana yanxu nehh ya kamata Ku tafi izuwa birnin sin dan saduwa da boka MUTSULUL GAYUSH ya kai dana ina mai kara fada maka ka kula da hanyoyin da zakubi kaida gimbiya numaira dan akwai gungun yan fashi sannan ka kula da ita kamar yarda zaka kula da yar uwarka wato yarinya SAMRILA

 

 

 

bayan nan yanxun nan zan baka wani dan guziri da zai taimaka maka acikin wannan tafiya taka yana kaiwa nan ya dafah kan sadauki Razmir yana mai karamta wadansu dalasiman tsafi saida ya kwashi sa a daya da rabi yana abu daya sannan wani Jan haske ya fito daga kansa ya fara shiga kan sadauki Razmir ba a jima ba ya gama shiga

 

 

 

Yana gama shiga jikin sa yaji wani sabon karfi ya shiga jikin sa boka salsalul num nehh ya kallesa yace” a yanxu na baka sihirin tsafi kalan nawa wannan zai taimaka maka a hanya yana gama fadin haka ya kwallawa gimbiya numaira kira

 

 

 

 

Sai Bata ta fito cikin gagarumar shigar yaki mai matukar mini da jakar guziri a hannunta boka salsalul num ya kalleta kana yace ya ke yata kiyi sani cewa yanxu neh lokacin tafiyarku keda Razmir dan haka sai Ku kiyaye duk wata dokar Daji idan ba haka ba zaku fada tarko batare da kun sani ba nidai ba wani abinda zance kawai dai sai kun dawo inda rabon mu sake saduwa aljani shabrul yana bakin kogon nan yana jiranku shine zai kaiku duk inda kuke dan haka Ku gaggauta zuwa kusameshi yana gama fadin hakan ya bace bat kamar bai taba wanzuwa ba

 

 

 

A tare suka mike gimbiya Numaira tana ruke da jakar guzurinsu lokaci guda suka ruga da wani azababben gudu dan zuwa karshen kogon

 

 

 

Anan nehh fah sadauki Razmir yasha mamaki dan duk karfin gudunsa ya kasa bawa gimbiya Numaira rata a tare suke tafiya har karshen kogon wannan abun nehh ya matukar bashi mamaki dan shi tunda ya tashi bai taba ganin mahalukin da suka tsera bai wuce shi ba sai yau da wannan tunanin suka ruski aljani shabrul basu tsaya komai ba suka suka haye bayan sa ya wullah dasu sararin samaniya kai tsaye ya durfafi hanyar da zata kaishi birnin sin dan saduwa da BOKA MUTSULUL GUYUSH…………..

 

 

 

wannan kenan comments dinku shi zaisa na ci gaba da rubutu

 

 

 

Vote
Comments and shared

 

 

WhatsApp number 08143314152

 

 

 

By fast class
????????????????????
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
????????????????????

Writing by

ALIYU H ISHAQ
(fast class)

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

DAGA MARUBUCIN

UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
And now

SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)

???? 25↔30

 

 

 

 

………..Al amarin yarima mangul kuwa lokacin daya fita daga cikin turakar sa bai zame koh ina ba sai turakar mahaifinsa yana zuwa ya zube bisa guyoyinsa yana mai sunkuyar da kansa

 

 

 

Koh da sarki Darraju yaga yanayin da dan nasa ta shiga sai ya taso cikin sauri yana mai dafa kafadar sa yana fadin

 

Ya kai dan shin me yake faruwa da kai nehh waye ya taba ka

 

 

Ko da jin wannan tambaya sai yarima mangul ya dago rinannun idanun sa da suka kada sukayi jajur ya kallo sarki Darraju lokaci guda ya fashe da kuka yana mai fada wa jikin sarki

 

 

Cikin tashin hankali sarki Darraju ya fara girgiza shi yana mai tambayarsa abinda ya sameshi

 

 

Sai da ya yayi kukan sa mai Isar sa sannan ya dago jajayen idanun sa ya fuskan ci sarki Darraju ya zayyane masa duk abinda ya faru tsakanin sa shamril bai boye masa komai ba

 

 

Wata kururuwa sarki Darraju yayi lokaci guda kuma ya fashe da kuka chan kuma sai ya tsagaita kukan yana mai kallon dan nasa yana cewa”kaico da kai yarima kayi Babban kuskure kuskuren kuwa ba komai bane illah saduwar da kayi da wannan budurwa da ka kyaleta da zan iya dawo make da dukkan karfinka da karfin sihirin ka da karfin sihiri na amma yanxun aikin gama ya gama kasani cewa daga rana irin ta yau ka daina jin sha’awar kowacce mace a duniya inba shamril ba sannan ina mai sanar da kai a yanxun hakan nan baka da wani sauran karfi ajikin ka da kai da macen data shekara Dari a duniya duk daya dan ba abinda zaka Iya tabukawa

 

 

 

Magana ta karshe shine tabbas shamril zata samu ciki da kai kuma zata haifama magaji kuma zai taso da tsananin tsantsar jarumtar da kai karasa kuma tabbas sai yayi ajalinka dan shine zai kashe ka idan kanaso ka hana faruwar wadannan abubuwa anya daya ce hanyar kuwa ni kaina bansan ta ba amma tabbas akwai mafita a yanxun hakan nan duk duniya boka daya nehh zai iya ma wannan aikin ba kowa bane face BOKA BURNUHUL MANSUR amintaccen da nakeji dashi acikin wannan birnin

 

 

 

Kasani a duk duniya ba wanda yake da maganin wannan matsala taka inba shi ba sabida haka yanxun zan kirashi sai ya fada maka maganin kafin sarki Darraju ya rife bakinsa kawai sai ganin wani koren haske sukayi ya ratso bangon dakin ya shogo take haske ya rikide ya koma boka barnuhul mansul yana mai kyalkyala Dariya saida ya jima yana wannan Dariya tukun daga bisani ya turbine fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya kalli sarki Darraju yace”

 

 

 

 

Gani ma na bayyana ya shugabana kuma naji duk abinda yaje faruwa da yarima mangul tabbas yayi ganganci ba kadan ba domin wannan yarinya shamril yar wani gahutaccen boka ce shi yarima mangul da kansa ya kashe mata mahaifin ta ya dauko ta daga birnin su shiyisa ta masa wannan shiri batun haihuwa kuwa wannan bakin alkalami ya ruga ya bushe tabbas sai ta haihu da kai kuma idan kayi wasa danka shine zai kashe ka

 

 

 

 

Kasani cewa a yanxu duk duniyar nan ba abinda zakasha ya dawo maka da dukkan karfin dantsen ka da karfin sihirin ka face wani tsumi da wani dodo da ake kira DARZAKU yake hadawa duk shekara

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button