SADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

Dodo darzaku yana zaune nehh acikin wani mugun Daji a arewa da birnin romaniya Ku sani daga nan Zuwa birnin romaniya tafiya ce ta wata biyar a doki koh rakumi sannan bayan min isa wannan birnin sai mun ratsa wadansu miyagun dazuzzuka guda uku Daji na farko wadansu manta manyan kunamu nehh masu cin naman mutum a dadin wadannan kunamu ya kai dubu daya sama da shekara biyu ba ya ba a samu wani mahaluki daya iya ratsa wannan Daji ba ya fita lpy
Daji na biyu wadansu manta manyan tsuntsaye nehh masu kan mutum adadinsu ya kai Dari uku da doriya sama da shekara biyu baya ba a samu wani mahaluki da ya iya zuwa wannan Daji ya wuce ba a Raye
Daji na uku wanda shine na karshe wani kogi nehh mai dauke da mamyan kadoji da kifaye da dodanni a tarihin wannan Kogi ba a taba samun mahalukin daya iya wucewa ta cikin sa ba
Bayan mun wuce wannan daji zamu tsinci kanmu a dajin sautil maut wanda anan nehh gidan dodo darzaku yake akan wani dogon tsauni duk shekara dodo darzaku yake hada wannan tsumi nasa yana sha
Wannan tsumi shikadai nehh maganin lalurar ka kasani cewa ba mu kadai ZAMU yi wannan tafiya ba dan muna bukatar abokan rakiya acikin wadannan abokan tafiya tamu akwai jarumi sarjun sai jaruma famila sai sadauki narkus
Sadauki surjan a duk wannan nahiya ba wani jarumi daya kaishi iya sarrafa takobi abinda yasa ZAMU tafi dashi kuwa ba komai bane ba illah wata masoyiyarsa da yake matukar so saidai kash sadauki surjan shikuma bayajin sha’awar mace kwata kwata ita kuma tace sai shi sabida haka nehh suka zo gurina da batun su na fada musu tsumin dodo darzaku nehh kawai maganin wannan cuta tasa ya bari akwai lokacin da za aje a debo wannan tsumi idan lokaci yayi zan masa mgn wannan shine lokacin sabida haka kawai biyawa zamuyi mu dauke shi
Sai jaruma famila wadda masani suka tabbatar kaf nahiyar nan ba wata jarumar data kaita zafin nama a fagen yaki ita kuma batada matsalar komai a rayuwata amma ZAMU je mata da batun aure a rayuwar jaruma famila ba abinda takeso kamar gahurtaccen basarake sabida haka idan ka nuna mata zaka aureta tsaf zata amince da batun ka
Sai jarumi na uku wato sadauki narkus shikuma masani masu bincike sun tabbatar da akaf wannan nahiyar ba wani jarumi da ya kaishi karfin dantse da tsagwaron iya yaki sai sarki Darraju da yarima mangul kai kuwa yarima mangul yanxu ka zama babu dan haka shima zai taimaka mana acikin wannan tafiya
Kasani a rayuwar sadauki narkus ba abinda yakeso kamar kudi da daukaka idan kayi masa alkawarin duniya mai farin yawa da matsayi mai girma zai yarda ya bimu wannan tafiya amma fahh kasani baxamu taba tafiya da sarki Darraju ba sabida abokan gabar dake kusan toshi
Ya kai sarkin sarakuna ka sani cewa dan sarki hawwasha da kayiwa juyin mulki ya girma a yanxun ya zama gawurtaccen jarumi mai dakawa maza gunba a hannu kuma a yanxu duk duniya ba mutum da ya kaishi karfin gudu a kafa sai kai maganar da nake maka a yanxu haka ya yayi tafiya mai dogon zango dan ya dawo ya fuskanceka ya karbi karagar mahaifin sa dan haka kenan da kai da yarima duk kuna cikin tsaka mai wuya kenan dan haka sai kuyi tunanin mafita ni dai a shirye nake yarima mangul idan ka shirya hadimina najiram mu a waje dan mu fuskanci wannan tafiya dake gaban mu koh da boka barnuhul masul yaxo nan a zancen sa sai yayi shuru yana Mao sauraren da da mahaifinsa,,,,,,,,,,
WANNAN KENAN
Al’amarin su sadauki Razmir da gimbiya Numaira kuwa lokacin da aljani shabrul ya daukesu suka fara tafiya saida sukayi tafiya sa’a daya da rabi sannan suka shiga yankin birnin sin
Haka suka ci gaba da tafiya ba tare da tsoron komai ba bayan wadansu dakiku nehh gimbiya Numaira tayi gyaran muryanta Alamar tanada bukata nan take aljani shabrul y sauko kasa luuuuu bai dira ako ina ba sai acikin wani daji mai matukar muni da ban tsoro suna sauka acikin.dajin sadauki Razmir yasha jinin jikinsa kawai sai ya fara kallon yanayin dajin yana nazarin ko ina
Dajin ya kasance yana da manyan bishiyoyi dogaye wadanda ba a iya hango karshen su sannan dajin yana da matukar duhu tamkar dare nehh lokacin
Ba tare da bata wani lokaci da gimbiya Numaira ta zagaya bayan wata bishiya dan kawarta da bukatar ta
Bayan wadansu dakiku nehh sadauki Razmir ya jiyo ihun gimbiya Namaira cikin bakin zafin nama ya tare takobin sa da gudu yayi bayan bashiyar yana isa yaga wani Abu ya sumgumi gimbiya Numaira ya zubata da mugun gudu cikin bakin zafinnama sadaiji Razmir ya rufah masa baya suka kasa tsere nan take ya kama shi ba komai bane ba sai wani gwagwgwan biri nan dai suka ci gaba da gudu shi birin bai tsaya ba shikuma sadauki Razmir ya kasa kamoshi saida suka shafe sa’a daya da rabi suna wannan gudu a sannan nehh suka iso wani fili fetal filin ya kasance makeke birin yana zuwa gurin nan ya tsaya yana mai fuskantar sadauki Razmir wata kururuwa yayi kawai saiga birirrika suna fitowa daga ramuka wasu daga cikin daji kan kace wani Abu sun yi wa sadauki Razmir kawanya tako ina
Shiko sai ya gyara tsayuwarsa yana mai fuskantar birirrikan ana kallon kallo………………
KAKA KARA KAKA YANXUN FAHH AKA FARA LBRN MUJE ZUWA COMMENTS DINKU KAWAI NAKE BUKATA
vote
Comments and shared
WhatsApp number 08143314152
By fast class
????????????????????
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
????????????????????
Writing by
ALIYU H ISHAQ
(fast class)
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
DAGA MARUBUCIN
UMAR FAROUQ
KAUNAR UWA
TARTSATSIN WUTA
(Adventure story)
SANDAR GIRMA
(Adventure story)
HAEEDARR
And now
↙
SADAUKI RAZMIR
(Adventure story)
IG, haidar_Ishaq_576
Email, haidarishaq@gmail.com
WATTPAD, @FASTCLASS
Facebook, haidar ishaq
…………Lokacin da sadauki Razmir suka fafata kazamin yaki da shugaban wannan biririkan har ya bamu nasarar kashe shi nan fahh labari ya sauya ga dai na Razmir a tsaye cikin mawuyacin hali amma acikin wadannan birirrikan an rasa wanda zai yi ta maza ya kawo masa wani farmaki
Koda sadauki Razmir yaga haka sai ya takarkare ya kwarara uban ihu yana mai daga takobin sa sama nan take wadannan birirrikan suka ce kafa mai naci ban baki ba kan kace wani Abu sun gudu ba koh daya a gurin sai gimbiya Numaira dake gefe daya tana maida numfashi
Da rarrafe ta taho inda sadauki Razmir yake a tsugune tana mai dafa kafadar sa suna hada idanu ta sakar masa wani tattausan murmushi kana ta bude baki tace”ngd da ceton rayuwata da kayi
Shima murmushi yayi mata amma baice kala ba ya mike y zaro battar ruwansa ya kafa baki ya kama sha bayan ya sha ya isheshi nehh suka tashi suka koma inda sukabar aljani shabrul
Ba tare da bata wani lokaci ba suka ci gaba da tafiyar su inda suka durfafi birnin sin kai tsaye ba tare da shakkar komai ba
A cikin Rabin sa’a suka iso birnin sin basu sha wahala ba gurin Neman gidan boka mutsulul gayush dan ya shahara a birnin
Da Isar sadauki Razmir fadar boka mutsulul gayush nehh yaji an fara tafa masa ana mai yi masa kirari gaba daya bangon fadar ya dauka ko ina amma baiga Wanda yake masa wannan tafin ba