HAUSA NOVELNOVELSSADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

SADAUKI RAZMIR Complete Hausa Novel

 

 

Bayan wasu yan mintuna nehh yaga mutum ya bayyana tsulum a gabansa mutumin ya kasance zabgegen kato mai kirar karfi gaba daya jikin sa daure yake da kayi da gurayen tsafi koh da sadauki Razmir yayi arba d boka mutsulul gayush nan take sai zuciyarsa ta buga da karfi har boka mutsulul gayush yazo kusa da shi baisan yazo ba saida ya tabashi yayi firgigit kamar wanda yake bacci ji yayi boka mutsulul gayush yana fadin

 

 

 

Lale marhabun da jarumi uban jarumai sadauki uban sadaukai sadauki Razmir ibn hawwasha kasani cewa naga duk gumurzun da kuka yi da wadannan birirrika kasani ba karamin kokari kayi ba hakan shine yake nunamin ka shirya tsaf dan tunkarar abokan gabarka kasani cewa akwai aiki a gaban ka aikin kuwa ba karami bane dan saikayi da gsk sannan zaka iya samun nasara akan sarki Darraju dan ya kasance babban hatsabibi koh ni kaina ina shakkarsa a duk duniya kai kadai nehh xaka iya tunkarar sa da yaki sabida haka idan ka shirya yanxu zamu fara abinda ya kawo ka dan bata lokaci a wannan lokacin yana daya daga cikin Babban kuskuren da zamuyi

 

 

 

Koh da jin haka sai sadauki Razmir ya kalli boka mutsulul gayush yace a shirye nake da duk wani horo da zaka bani ya shugaba kai kawai nake jira

 

 

 

Ko da sadauki Razmir yazo nan a zancen sa sai boka mutsulul gayush yayi murmushi sannan yace to yanxun zan sa a kaiku masaukin Ku kaida abokan tafiyar ka Ku Hutu zuwa gobe da safe sai mu fara abinda ya kawo mu

 

 

Ba tare da bata lokaci ba boka mutsulul gayush yasa aka basu masauki mai kyau aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma suka ci suka sha sannan suka dan kishin gida dan su huta

 

 

 

Was he gari da sassafe boka mutsulul gayush ya aiko aka tashi sadauki Razmir ba tare da bata wani lokaci ba ya fara bawa sadauki Razmir wani tsumi yana sha da kuma horo mai tsanani saida suka sami sati daya a sannan nehh sadauki Razmir yaji wani gagarumin karfi ya shigeshi wanda bai taba jin kamarsa ba a sannan nehh boka mutsulul gayush ya kawo wasu guraye ya daura masa a dantsensa hagu da dama sannan ya dafa kansa yana mai fadin ya kai Razmir wannan shine iya taimakon da zan iya baka a yanxun haka duk duniya ba wanda yake da irin sihirin tsafin da kakeda shi saini da sarki darraju sabida haka ina maka fatan nasara yana gama fadin hakan ya bace bat kamar bai taba wanzuwa a gurin ba

 

 

 

Ba tare da bata wani lokaci ba suka hau kan aljani shabrul dashi da gimbiya Numaira ya tashi ya luluka dasu a sararin samaniya ya durfafi birnin KUFA dan saduwa da SADAUKI DARBUZA………….

 

 

 

kuyi manej da wannan bani da lokaci mai yawa nehh shiyisa idan naga comments zan ci gaba da typing insha allah idan naga akasin haka kuma sai allah ya kaimu bayan sallah da rai da lpy kada fa Ku manta lbrn mu yana da yawa yanxun aka fara fahh

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button