SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

Aslamu alaikum nice na ɗauki yarinyarki ,dama na rubuta ne koda zakici karo dashi kai koma ba keba ina mai sanar muku wannan yarinyar ta zamo mallakina ,kuma yau zanbar ƙasarnan da ita .

A zabure Zainab ta miƙe tare da kurma ihu tana cewa “wlhi bazan yarda ba , Norr zaki dawo gareni “karaf a kunnen baba lokacin ya dawo daga masallaci sallahar isha’i ,ya taho da gudu ya buɗe labulen ɗakin Zainab kana yace “Zainabu me kuma ya faru ?”

Ƙin kulasa tayi sai da yayi magana har sau uku sannan tace “Norr aka sace “ido waje baba ya dafe ƙirji kana yace “dama ansan kin aihu ne” butar dake gefenta ta wurgawa mahaifin nata Allah yayi taimako ya kauce da ya sameshi tace “baba ka cutar da rayuwata ,tunda mamana ta rasu kaƙi yarda a kaini dangin su ,yanzu gashi rayuwata ta lalace ,mutanen garinnan zasu kasa sani ne ?ni gara in shiga duniya da zama a gidannan !”

Ɗiff numfashin baba ya kusa ɗaukewa ,ya sami guri ya zauna kana yace “Zainabu aini na ɗauka komai ya wuce tunda har an shekara ,kuma inhar mijin aure kike tararradi ninan ,nizan kawo miki shi har gida karki sami damuwa “.

Da sauri ta miƙe tare da janyo jakar kayanta ta fara haɗawa tana kuka mai ban tausayi .

Kasancewar baban ya fito ya ganta kana yace “ni yanzo neman Aisha zani ki zauna inje in dawo ” Zainab tace “dangin mamana zani “tana maganar tayi wurgawa mahaifinta kallon tsana ,kalmar da ta doki dodon kunnenta itace “zan tsine miki inhar kika sanya ƙafa kika bar gidannan “rass gabanta ya faɗi bawai dan ta karaya ko taji tsoro ba ,sai dan tana shirin ƙetare maganarsa a halin yanzu babu mai faɗa mata ta saureshi ,yana fita ta fice tare da zuwa bakin titi ta tari mota zuwa , Abuja.
Koda baba ya dawo gida ya samu bata nan ,ya jingina kansa da bango tare da .
Hawayen baƙinciki suna zarya a fuskarsa,a fili yace .”na cutar da rayyuwarki Zainab son zuciya ya jani na tarwatsa miki rayuwa ,tabas da wata ƴar ce ƙarata zatakai gurin hukuma .

Su Zainab sunyi nisa sosai ,ta ciro wayarta ƙirar Nokia ta danna kiran ƙanwar mahaifiyarta , bayan ta ɗauka ne Zainab tace “momy yau ina hanya “ƙanwar mahaifiyar tata tace “kodai ƙarya kike ?nasan mahaifinki bazai barki zuwa ko nan da can ba”Zainab tayi murmishin ƙarfin hali kana tace “momy mun ma kusa sauka gashi bani da kuɗin mota “daga can ɓangaren momyn tace “bari in kun kusa tasha ki kirani Affan zai taho miki da kuɗi ya ɗaukoki “to momy “Zainab tace “cikin sanyin murya .

Cikin ikon Allah suka iso KEFI ta kuma kiran momy ,gyan gyaɗi ne ya ɗauketa ba ita ta farka ba sai da taji ana cewa “waye mai sauka a INTANATIONAL MARKET ta farka a zabure tare da cewa nice anan zan sauka “. driver na parking sai ga motar Affan nan ta tsaya , ta glass ɗin mota Zainab ta hangosa kasancewar an buɗe motar da take ciki yasata sauka tare da cewa “driver dan Allah barin karɓo maka kuɗi a gurin waccan ,dai-dai lokacin da Affan ya fito tare da isowa gurin ɗrivern ,yace “gashi mungode “babu komai “driver yace , Zainab dake tsaye kasancewar ba wani shiri suke da Affan ɗin ba tun bai kai haka ba ,idan suka zo gidansu ita da mahaifiyarta ya dinga yi musu iskanci kenan sbda baya ƙaunar talakawa ko kaɗan ,dan yaga momynsa ta auri mahaifinsu mai kuɗi .

Affan ya kalli Zainab dake tsaye ,irin kallon wulaƙancin nan kana ya ɗan taɓe baki kamar mace ,yace “zaki iya shiga wlhi daga yau kika sake yimin haka ni dake ne ,sai lokacin da kika kusa garin mutane zaki kirasu kice su baki kuɗi ?”.
Ita dai Zainab ita tasan abinda ke damunta duk ba wannan bane a gabanta .
Kai tsaye ta shiga motar abda a halin yanzu ba buƙatar dogon surutu take ba ,koda yaci gaba ba jinsa zatayi ba.

Affan dogo ne fari matashi a ƙalla zaikai shekaru talatin a duniya ,ya kammala karatunsa a halin yanzu aiki yake a company na dad ɗinsa ,inda suke sarrafa aduga izuwa kayayyaki na moruwa masu kyau

Kasancewar tsakanin kasuwar da aka sauketa da anguwar tasu da nisa ,hakan yasa sai da suka sha tafiya sannan suka iso anguwar su Affan Wuse two G.R.A.

Gaban wani haɗaɗɗen gida naga yayi parking , kai da ganin gidan zakasan nera tayi kuka ,duba da yanayin tsarin gidan da kuma nerorin da aka narka. sai da ya jira mai mota gadi ya buɗe masa get sannan ya shiga ,bayan sun shiga yayi parking a inda aka tanadar dan ajiye motoci ya fito ,tare da ƙare mata kallo kafin yace .” saura idan mun shiga ki faɗawa momyna komai kema kinsan sauran “.
Bata kulashi ba ta fito daga motar tare da gyara zaman wuyan hijab ɗinta da yaɗan yi mata yawa kana ta rufa masa baya suka ƙarasa ciki.
Da sallama ta shiga tare da faɗawa jikin momy da gudu ,kasancewar momyn na tahowa sbda taji ƙarar motar Affan kawai taji Zainab ta rungumeta tare da sakin kuka mai cin rai .
Momy ta kamo hannunta tace “zomuje kiyi wanka kiyi alwalah kiyi sallah kinga ana zafi a garin kyaji daɗin jikinki “cikin jin daɗi tabi momy ɗakinta ,tana shiga ta zube kan kujerar dake bedroom ɗin guda biyu a jere ta lumshe ido hoton fuskar Norr ɗinta na dawo mata ,da sauri ta fashe da kuka tare da cewa “innalilahi wa inna ilaihir raji’un “
Momy da ta fito cikin sauri taga Zainab ta sunkuyar da kanta ƙasa ,taɗan ƙare mata kallo kafin tace ” daughter maza tashi na haɗa miki da ɗan zafinsa…..!

Wannan littafin na kudi ne normal grp 300 VIP 600 special 1000 zaki turo da kud’inki ta wannan account d’in 3175689751 Zainab Habibu first Bank shedar biya ta wannan number 08241799224

Idan kuma kati ne zaki d’auki hoton katin ki turomin ta wannan number 08141799224
[5/12, 12:06 PM] Mom Islam Ce: ????????????????????????
SAHIBUL AMRAT

????️????????????

Zainab Habib(Mom Islam

Banyishi dan wani ko wata na ,inhar yazo dai-dai da labarinki arashine????

_____________________3-4

A hankali ta tashi ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da ɗauro alwalar magrib ta fito , tana fitowa taci karo da Affan a zaune ,bata ma san ya shigo ba sai ƙafarsa data buga ne ya tabbatar mata da hakan , a faɗace ya wurga mata harara kafin yace “karki ɗauka kinzo zama ne komawa gidanku zakiyi “ya miƙe ya fice .

Yakai kamar 10mins da fita ,momy ta shigo tare da cewa “tashi kije ga dadynku ya dawo ki gaishesa ” cikin bin umarnin momy ta sanya hijab tafita ,kana taje ɗakin dadyn ,sai da ta tsaya a bakin ƙofa tayi sallama bayan ya amsa ta shiga .
Kasancewar yana sama a kan kujera hakan ya bawa Zainab damar zama kan kafeta tace “sannu da dawowa dady ina yini “

Cikin sakin fuska dady yace “lpy lou uwata yau kece a gidan namu ?”
Murmishi Zainab tayi kafin tace “dady sai anjima “
Dady yace “to Allah ya tashemu lafiya amma dai zaki kwana mana biyu koh ?”
“Eh” tace tare da yin gaba.

Dagannan ta koma bedroom ɗin momy sukayi sallama ta wuce ɗakin da idan sunzo da mamanta suke kwana .
Tana fita momy ta zauna a bakin gado tare da yin tagumi a fili tace “to me ya sami Zainab ?kodai ta gudu uban nata zeyi mata auran dole ne ?tana tsaka da tunani taji Affan na cewa “momy nadawo daga masallaci sai da safe “
Ba tare da ta tashi ba ,tace “Allah ya tashe mu lafiya my son “.
Koda Zainab ta kwanta sana’ar tata takeyi wato kuka ,sai dai yanzu babu ruwan hawaye sosai sai matsosu take amma sun ƙafe ,ga idanunta nayi mata zafi ,ta daɗe a haka batayi bacci ba har ƙarfe (1:10 am) na dare ,bata san lokacin da bacci ya ɗauketa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button