NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

     **NI DA YAYA  LAMEER**

                          ❤❤❤❤
                           ????????????????

Gajeran labari

Story and written

By

Fateemah Sununi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????

NI DA YAYA LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144

SHINFIƊA
Godiya ta tabbata ga Allah (S W T)da yasake bani dama na rubuta muku wannan littafin,Tsira da aminci suk’ara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (S A W)da alayensa da sahabbansa da wad’anda sukabi ta farkinsa har zuwa ranar sakamako.

GIRGIƊI

Wannan labarin k’irk’irar ran labari ne banyisa don chin zarafin wani ko wata ba duk wanda yaji yayi kama danashi to arashi ne da fatan za’a guji zargi banyisa don wani ko wata ba ko cin zarafin kowa ba,banyarda a juyaminshi to ko wacce suffah ba da fatan za’a kiyaye.

DIDECATED TO ATK

SPECIAL GIFT TO
ANTY HAUWA

GAISUWA TARE DA FATAN AL’AMARIN ƳAN UWANA NA AREWA WRITER’S ALLAH YA ƘARA HAƊA KANMU AMEN

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM

????1↪2

“Ni aradun Allah ba inda zani haba Kakar nan wai me ke damunki ne ko duk rud’un tsufan ne,

Muryar wata ‘yar matashiyar budurwar yarinya kenan wacce bazata wuce shekaru goma sha hud’u da haihuwa ba,

Kakar tata wacce ashekaru zatayi sittin da biyar tace”haba ‘yar jikallena zenabubuwata ‘yar abullena don Allah kije mana kinga yanata jiranki kar yajiki shuru,

Turo baki gaba tayi cikin tsabar shagwa6a irin ta goyan kaka tace”Aradun Allah mutumin nan d’an renin wayau ne Kaka jiya fa har mazge min baki yayi sbd tsabar mugunta irin tasa nifa nagaji da zuwa gurinsa,

Kaka ta fara turata”don Allah Abulle ki wuce banson shak’iyanci irin naki,d’an murmushi tayi aranta tace”uhmmm wllh nasan mgninsa yau,

Da gudu ta ruga ko mayafi babu,ita dai Kaka cewa tayi “sai kin dawo Abulle na,ko juyowa batayi ba,bata dire a ko ina ba sai k’ofar gida,daidai inda yayi parking motarsa,

Sai lokacin na k’are mata kallo ba laifi kyakkyawace ‘yar dubaduba,Choculate colour ga idanuwa da dogon hanci d’an bakinta me kyau,bata cika tsayi ba kuma ba gajera bace daidai daidai misali

Jikinta kuwa atamfa ce,riga da zani sai kallabi da ta d’aura fuskarta ba kwalliya don ba kwalliyar take ba,

Tsaye yake jingine a bakin motarsa kyakkyawan saurayi fari dogo,ai ina kallonsa nace masha Allah don guy d’in ya had’u ba makusa ko ta ina yayi,d’an boko wayayye daga ganinsa kasan nera ta zauna ajikinsa,

Tana zuwa taci burki gabansa,da sauri ya matsa,”subuhanallahi ya fad’a duk a zatonsa dokine ya antayo a guje,”Lah YAYA LAMEER gsky yau ka had’u d’an bani wannan k’atuwar wayar taka na d’auke ka photo,

Nan ta zura hannu aljihunsa tana k’ok’arin cirowa,

Rik’e hannun yayi gam yana kallonta,d’aure fuska yayi”wai ke Zainab sai yaushe zakiyi hankali ne,harara ta banka masa,

Sai kuma ta k’wa6e fuska”uhmm don Allah ka kawo na d’aukeka photo yaufa ka had’u sosai,

Mik’a mata wayar yayi,ta kasa danno inda ya kamata don ba iyawa tayi ba,jikinsa ta dawo,yauwa nama fasa d’aukarka kunnamin game na fad’an nan,

Wanda ake haka,nan ta fara nuna masa da hannu da k’afar ta kama hannunta yayi yace”to naji yau bazan kunna miki ba sai kin amince zaki koma gurin Ammi,

Mak’e kafad’a tayi”uhhhm uhmmm Wllh bazai yarda ba,ba kai bane chaf ni bazan yarda ba,

Juyawa yayi zai shiga mota alamar yayi fushi “da sauri tasha gabansa tare da rungumesa ta mak’alk’ale ajikinsa,turo baki tayi cikin shagwa6a tace”Am Sorry Yayah Lameer zan koma amma saidai na dunga kwana d’akin Ammi,ka amince?murmushi yayi tare da gyad’a kai bayan ya lumshe ido alamar ya amince,

Tace”yauwa to kunna min game,yace”mushiga ciki zan kunna miki a d’akin KAKAH,

Ya kukaji littafin muci gaba ko mu tsaya,

Yawan comments yawon tyiping,baida yawa labarin idan kuka bani had’in kai da comments kuma shirhi masu dad’i to nima zakusha mamakin typing✍️✍️✍️
❤❤❤❤
????????????????

        **NI DA YAYA  LAMEER**

                          ❤❤❤❤
                           ????????????????

GAJERAN LABARI

Story and written

By

Fateemah Sununi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????

NI DA YAYA LAMEER!

Rawa da girgiza zanyi gabanku in jujjuya????????Ina muku albishir kunyi dace da mai tarbiya,Comments d’inku na jiya yasa na jujjuya????????????Idan kukaci gaba da haka zakusha mamaki,

Wow Aradun Allah jiya kunsani farinciki na yarda littafin nan ya samu kar6uwa,tom acigaba da gashi,
NI DA YAYA LAMEER Fans ina godiya,kuma ‘yan Facebook ba’a barku abaya ba gsky inayinku over ana tare????

WhatsAPP no 08104335144

Diditated to ATK

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

????️3↪️4

Suna shiga suka iske Kaka har ta baje kan kujera tana gengad’i,sallama sukayi ta bud’e ido nan ta fara washe baki,

Tace”d’an tselan uwa LAMEERU kaine yaune kayi niyyar shugowa da ba kiranta awaya kake ku zauna amoto ba yau kuma me yashugo da kai,

Yace”Allah ya baki hak’uri Kaka yauma abinda ya shugo dani had’a kayan Zainab zanyi mu wuce gida ai bakisan fushi nake dake ba tunda kika rik’emin mata,

Zaro ido Zainab tayi????tace”Chaf chafd’i jan aradun Allah bazai yarda ba wace mata ni ce mata,saitasa kuka tana nuna kanta”cikin kukan tace”ni YAYA LAMEER nace kadena cemin mata,ai sai araina ni ace ni mata ce,haik’an take kuka,

Da sauri yazo kusa da ita ya zawota jikinsa yarungume yana buga bayanta alamar rarrashi yace”Sorry My Wife bazan sake ba,sai kawai ta tun tsuro da dariya tasake hawa jikinsa tace”yauwa YAYA LAMEER haka nake so amma da zakace min mata

????????????(Kunji Ummu Inteesar to meye ma’anar Wife d’in na zaci duk d’aya ne,????)

Kaka tace”shashashar banza kawai ai daman ko LAMEERU baizo ba nayi niyyar yau saikin bar gidan nan baki da aiki sai shashanci,gwalo tawa Kaka tace”kedai rud’un tsufa ne ke damunki,

Sallama muka juyo duka muka juya,Abbu ne sai Ammi da Baba sai Umma,

Ai da sauri na sauka jikin YAYA LAMEER naje na d’ane Abbu nace”sannu da zuwa Abbuna,rik’eni yayi cikin murmushi yace”yauwa Ummina,murmushi mukayi muka zauna bisa kujerun dake farlour,

Baba yace”Gwoggo sai mukaji Ummi ta dawo gidan nan,da yake haka suke kiran Zainab,kasantuwar sunan Gwoggonsu gareta wato Kaka,

Tun kafin Kaka tayi magana Zainab tace”Wllh Baba Yaya Lameer ne ya ke…..Umma ce ta buge mata baki sanadiyyar shurunta,Ammi tace”haba meye hakan ne kike bugemata baki ki bari ta fad’a kika sani ko wani abun yake mata,

Umma tace”haba gida d’aya fa kuke ya za’ayi ya mata wani abu na ba daidai ba,Ammi tace”amma kinsan part d’insu daban ko?,

Umma tace”duk da haka,Zainab ce ta fara cewa”kuma wllh nan….Baba ya daka mata tsawa “Ummi meye kikeyi haka,Kaka tace”wllh ni duk tabi ta isheni LAMEERU d’auketa ku tafi,kamar yana jira ya kafa hannunta sukayi waje,su Abbu da Baba dry suka saka,Kaka kuwa sai mita take,

Cikin mota ya sakata ya zagaya yaja motar,bai mata magana ba har suka isa gida,Wow masha Allah gidan ya had’u over,

Yana parking ya fice baibi takanta ba,da sauri ta fito tabi bayansa,daidai shigarsa farlour ta cimmasa,”wai Yaya Lameer meke faruwa ne,banza ya mata ya zauna a kujera jikinsa ta fad’a tana tumurmusarsa,

Ta turo baki”me nayi maka ne,Jan kunnenta yayi ta saki k’ara ya matse mata baki,6oye fuskarta tayi a k’irjinsa,tace”don Allah na tuba,daman duk lokacin da yayi mata hakan tasan laifi tayi,

Yace”meyasa kunnen nan naki bayaji Zainab saunawa zan ce miki duk abinda ya faru tsakaninmu karki sanar da kowa,

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button