SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna fitowa dogarai da fadawa suka dinga jera kirari har suka ɓace , hannun prince Abdallah ya kama ya kaishi bedroom ɗinsa ya zaunar dashi kan haɗaɗɗiyar kujera , cire masa alkyabbar jikinsa yayi kana ya janyo kujera wata marar nauyi ya zauna gaban prince kana yace “haba yarima mai yasa zakayimin haka ?kasan ko me mai martaba yace min bazan iya ƙetarewa ba ?”.
Shafo sajen fuskarsa prince yayi kana yace “kai dan uwarka ni zaka rainawa wayo ,meya kawo hoton Hindu wayarka ?mai yasa duk lokacin da bayi suka rakata gurin shukokin gudannan kake leƙenta ?”.
Tsit Abdallah yayi ,kafin yace “,sai aka ce maka babu so na ƴan uwantaka sai na aure koh ?”
Hararasa prince yayi kana kafin yace “haka dai kace ,inason a haɗa bikina da naka ” ido waje Abdallah ke kallon prince sbda tunda suka taso bai taɓa ganin yayi budurwa ba amma yau shine harda maganar aure…..!

Wannan littafin na kudi ne normal grp 300 VIP 600 special 1000 zaki turo da kud’inki ta wannan account d’in 3175689751 Zainab Habibu first Bank shedar biya ta wannan number 08241799224

Idan kuma kati ne zaki d’auki hoton katin ki turomin ta wannan number 08141799224 y’an Niger suyi magana ta wannan number +22784506476 .

MOM ISLAM
[5/13, 9:38 AM] Mom Islam Ce: SAHIBUL AMARAT 08141799224 kibiyani haƙƙina kafin ki karantamin littafi.

11-12
Prince ya ɗaga masa gira kafin yace “,kana mamaki koh ?”hmm idan lokacin yayi zakasan wacce zan aura kai dai ka shirya naka bikin mijin Hindu “.
Yana faɗar haka ya fara rage kayan jikinsa ya shige toilet , bayan yayi wanka ya fito hannunsa riƙe da towel da wani a ƙugunsa , ganin Abdallah ya fice ya sashi zama tare da dafe kumatunsa ya faɗa kogin tunani “ring ɗin da yaji wayarsa tayi ne ya sashi ɗago kai yakai dubansa ga fuskar wayar ,ya ɗaga tare da amsa kiran ,a hankali yace “Ammi na “ɗaga can ɓangaren Ammi tace “Babana kazo yanzu ina jiranka ” tom kawai yace “dan yasan baya rasa gulmar wani abun aka kai mata tunda babu abinda mutum zaiyi bai fita waje ba .
Cikin sauri ya shafa mansa mai ƙamshi da tsada ya kawo kayansa yasa ,t-sheet da jins  rigar fara wandon baƙi ya ɗauki wayarsa bayan ya feshe jikinsa da turare ya fice  ,yana fitowa palo ya sami dogaransa a zazzaune ,suna ganinsa suka miƙe suka kwashi gaisuwa , kai kawai ya gyaɗa musu , yana shirin fita yaci karo da Iyami a bakin ƙofa tana rakuɓe ,a hassale ya daka mata tsawa tare da cewa “me kike anan ?” kanta a sunkuye alamun rashin gaskiya yasa shi ƙare mata kallo na ƴan daƙiƙu kana yabar gurin , yana barin gurin ta miƙe da gudu ta wuce part ɗin Hjya Rabi , tana zuwa ta zube a gabanta ta kwashi gaisuwa ,Hjya Rabi na ganinta ta gyara zama tare da mayarsa dukkan hankalinta ga Iyami tace “nasan bakya zuwar min da banzan labari meya faru kuma ?”Jakadiyar Hjya Rabi tace “ana sauraronki yarinya kinyi shiru “
Iyami da bakinta ke karkarwa tace “babar yarima ce takeson ta hana auransa da gimbiya Hindu “
A zabure Hjya Rabi ta zaro ido tana yarfe gumin daya karyo mata kana tace “bata isa ba , nida mai martaba mukayi maganar nan har zata juyamin ?wlhi sai anyi koda za’a ɗaura yau gobe in mutu “.

Jakadiya tace “uwar ɗakina ko jiya sai da nayi mafarkin auran gimbiya da yarima ” Hjya Rabi tasa dariya batace komai ba.
Prince na shiga part ɗin Ammi ya samu tana zaune kan kujera hannunta riƙe da alkur’ani , yaɗan jima a zaune kafin ta shafa adu’oin da take ta juyo ta kallesa kana tace “babana nasan kana yimin biyayya dai-dai gwargwado amma mai yasa zaka yiwa Abdallah katsalandan ba tare da sonsa ba ?” sunkuyar da kai prince yayi kana yace “Ammi na waye ya gaya miki hakan ?” kai tsaye Ammi tace “daga fadar mai martaba nake yanzu yace “kai da Abdallah kuka shigo wai akan maganar yana son Hindu  ,bayan na dawo ɗaki na zauna nayi tunani nace kai ,anya ba tilasta masa babana yayi ba ?” ka sani sanin kanka ba’a yiwa mai martaba magana biyu ,yanzu idan har shi Abdallahn baya sonta fa ka faɗamin inda zakayi?”.
Kan Prince Khalil a sunkuye idanunsa sunyi jajir sabda Amminsa ta koyar masa da faɗa mata damuwarsa tun yana yaro ,bata taɓa yarda yayi abu baiyi shawara da ita ba  ,yau kam ya mugun ɓata mata rai sosai.
Kan Prince a ƙasa yace “tuba nake Ammi na , wlhi ki kira Abdallah ki tambayeshi yana sonta “.
Ammi tace “to ita Hindun an tabbatar da tana sonshi ?”
Prince yace “eh ina tunanin hakan “
Girgiza kai Ammi tayi sbda bata son hayaniya ko kaɗan.
Washe gari ta kama Juma’a bayan an sakko daga sallah mai martaba ya tara iyalansa tare da shaida musu yabawa Abdallah Hindu “
Cikin tsiwa Hjya Rabi ta fara masifa tana cewa “dan anga ita marainiya ce shine za’a haɗa auranta da ɗan waziri wlhi bazata yarda ba ,ina laifin ma ace Ibrahim ne “
Kasancewar babu fadawan da sauran hadiman yasa take wannan surutun kuma dayake family meeting suke babu kowa.
Dakatar da ita mai martaba yayi cikin kakkausar murya yafara magana cikin izza ,maganar da komin taurin mutum dole ya tsaya ya saurareshi yace ” dan na zaɓarwa Hindu miji shine abin jin zafi ?” karki mance kamar inda zan kula da Khalil haka zan kula da Hindu , kuma fatan duk wani uba shine ƴarsa ta auri miji na gari , bana haufi akan auran nan kuma an tabbatar min akwai alkairi a cikinsa , Abdullahi mutum ne mai tarbiya tun bayan rasuwar mahaifinsa muke tare da shi anan gidan kema zaki bawa mutane labarin waye Abdullahi , kaima Babana ka fito da mata nan da kwana goma insha Allah bikin bazai wuce mako uku ba ,kafin nan zanyi magan da iyayen ita Hindun abinda sukace dashi zamuyi amfani “.
Idanun Hjya Rabi sun ƙaɗa sunyi ja ta kasa furta koda kalma ɗaya sbda zafafan maganganun mai martaba da suka dinga kuwwa a kunnuwanta .
Ammi kam tunda ta zauna ko uffan batace ba , a ƙasan zuciyarta bataso akaba Abdallah Hindu ba ,sbda rashin tarbiyarta .
Abdallah dake zaune kusa da prince ya taɓo prince alamar su fice sbda jinsa yake kamar an ɗauresa .
Saida suka ƙara kwasar gaisuwa a gurin mai martaba kana suka miƙe suka bar fada.
Abdallah na riƙe da hannun prince har suka iso part ɗinsa ana ta yi masa kirari da gaisuwa , kai tsaye a palo suka yada zango , Abdallah ya ƙyal-ƙyale da dariya kana yace “wayo Hindu masoyiyata “sai yaja kumatun prince.
Harara Prince ya galla masa kana yace “wlhi zamuyi faɗa ni yanzu a ina zan sami wata mata nida ba kula kowacce mace nake ba ?”Abdallah yace “kazo mu shiga gari kawai muyita yawo ƙila Allah zaisa a dace “Prince yayi dariyar yaƙe kana yace “ashema cigiya zamu ?” Abdallah yayi gum.
Gyara zaman ƙafarsa daya ɗora ɗaya kan ɗaya yayi kafin yace “.wato har yanzu baka fahimci wanene Ibrahim ba ko ? to barin faɗa maka , wacce zan aura sai ta haɗa duk waɗannan abubuwan ,na farko ilmi ,hankali,kunya,dakuma kamun kai gurmama magaifiyata ,wayayya kuma kyakkyawa ƴar manya kasan tuwon girma miyarsa nama ” gyaɗa kai Abdallah yayi tare da ƙumshe dariyarsa yace “to yanzu meyasa kake son auran waccar ƙazamar ?”,prince yace “anzo gurin , dalili shine ina son rama abinda tayiminne ,inba ta wannan hanyar ba sam bazan samu damar cin mutuncinta ba “.
Abdallah ya ɗanyi murmishi kafin yace “to inhar ka aureta daga baya sakinta zakayi ?”, prince yayi tsaki mtsw kana yace “,baiwa zata koma mai yimin wanki da goge min takalmi da gyaran gida ,ni kuma a lokacin zan auro wacce zataci ubanta “.
“Inaa gaskiya ka haƙura ka ƙyaleta dan bazamuci riba ba ” .
Abdallah ya faɗa yana mai haɗe hannuwansa alamar haƙuri .
Kallon bakada hankali prince yayiwa Abdallah kafin yace “banfa ce ka rakani ba ,so zanyi komai da kaina “.
Daganan suka tafi sallah.
Zuwa dare bayan sunci abinci suka nufi makwanci ,acan ma sai da sukaso yin faɗa ,Abdallah kam sai da ya kwanta tunanin Hindu ya fara yi masa zagaye a kwanyarsa ,shin shi yana sonta ita bata sonsa ya rayuwar auransu zata kasance ? anya Hjya Rabi zata amince kuwa ?
Bata isa ta yiwa mai martaba musu ba amma shi kansa yasan zai fuskanci matsaloli sai dai ya daure ,kuma Allah yagani yana son Hindu tun kafin rasuwar mahaifiyarta ,ya ɓoyewa zuciyarsa ne.
Washe gari ,an tashi da iska mai ƙarfin gaske ,wacce ta haifarwa garin hadari yayi duhu kamar almuru ,
Mai martaba na zaune a ɗakin Hjya Rabi da misalin ƙarfe 9:am ruwa ya tsinke sosai ga tsawa da aketayi ikon Allah kenan , kasancewar wutar lantarki data haska ɗakin yasa bazakace garin yayi duhu ba sbda engine aka tayar .
A cikin ɗakin daga mai martaba dake karin kumallo sai Hjya Rabi data cika tayi fam kamar zata fashe .
Mai Martaba ne ya kalli Hjya Rabi kafin yace ,” Rabi’atu nasanki da hankali mai yasa kike fushi da zaɓin da nayiwa Hindu?”.
Hjya Rabi da kamar jira take tace “kaima kasan wannan abun  dai babu adalci ga wanda takeso yake sonta shine zaka haɗata da wani ɗan wazirinka “ta turo baki gaba .
“Eh lallai ” Rabi’atu abu mai sauƙi bane cikin yardar ubangiji miji ya janyo hankalin mata ba ?” har mai martaba ya gama maganarsa Hjya Rabi ko uffan bata ƙara cewa ba har aka ɗauke ruwa gari yayi haske ,sai wajen 12:pm mai martaba yabar ɗakin .
Yana zaune a fada , fadawa sunata bashi labarin ci gaban da aka samu amma sam hankalin mai martaba yayi gaba tunanunsa shine ,wato dayawa mutane suna ganin kawai dan Hindu marainiyace shine ya zaɓa mata Abdallah ko ?
yaci gaba da cewa “nayi alƙawari babu abinda Abdallah zai nema inhar inadashi banyi masa ba muddin bai ƙetare shari’a ba”.
Sallamar da akayi ne yasa Mai martaba dawowa daga dogon tunanin daya tafi , ɗora idonsa kan prince da Abdallah da fadawa ke kwasar gaisuwa a gurinsu , bayan an amsa sallamar suka zauna cikin girmamawa suka gaida mai martaba yasa musu albarka , kasancewar Abdallah tare suka taso da prince tun suna shekara goma 10yrs iyayen Abdallah sukayi hatsari a hanyar KD lokacin zasu ganin gidan marayu wannan kenan.
Bayan ya gama sanya musu albarka suka miƙe suka fice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button