SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari ranar ta kasance Juma’a ,ranace da mutanen gidan suke breakfast ƙarfe (8:00am) taƙwas ,bayan sun yi sallah Zainab ta fito gaishe da momy ta samu bata ɗaki tana kitchen “kai tsaye Zainab ɗin ta bita kitchen tare da durƙusawa har ƙasa tace “momy barka da safiya “
Cike da farincikin ganin ɗiyar tata tace ” daughter barka ina fatan kinyi bacci ya isheki ?”sadda kanta ƙasa tayi kana tace “eh momy nazo tayaki aiki ne “flaks ɗin ruwan zafi momy ta miƙo mata tare da cups guda uku tace “kai dinning ” tom “Zainab tace takai dinning ta ajiye ta kuma dawowa ,a karo na biyu momy ta bata food flaks mai ɗauke da farfesun kayan ciki tace shima takai dinning ,daganan momy tace “an gama zanje wanka ki zauna ki fara ci “.
Batare da tayi musu ba taje ta ɗauko plets guda uku ta ajiye da cokali ta ɗauki guda ɗaya tasa kana ta haɗa tea ta ɗauki bredi .
Bata wani jima tana breakfast ɗinba ta kammala tare dayin hamdala ,tana shirin tashi Affan ya shigo cikin takunsa na ƙasaita zai zuba ƙamshi yake yace “keee ! ina momy ?” ko ɗago kai Zainab batayi ta kallesa ba tsawar daya daka mata ne yasa momy fitowa da sauri dan taɗan tsorata tace “lafiya Affan ?” yana wani cumo baki tare da harare -harare yace “momy wannan yarinyar nake tambaya ke amma bata bani amsa ba “murmishi momy tayi kana tace “ai ka fita sanin inda nake haba Affan yaushe zakayi hankali ? dole momy ta zauna shima Affan ɗin ya zauna ,dady daya fito yanzu suka gaishesa ya zauna sukayi breakfast , ganin Zainab bataci abinci ba ,yasa dady cewa “ƴata meyasa bakici abinci ba ?”kanta a ƙasa tace “dady ai tun ɗazu naci “
“Ok “
Dady yace “kana ya kalli Affan yace “yau bazakaje hospital ɗin bane ? ” Zani ” Affan ya faɗa kai tsaye ,inda abin da ya tsana bai wuce zuwansa aiki ba ,yafison a nemo a bashi yaci dady na gama yi masa magana yayi musu sallama ya fice.
Zuwa ƙarfe (10:am) Zainab tayi wanka ta taya momy gyara gidan suka dawo palo suka zauna , cikin sigar lallashi da ɗan tsokana momy tace “my daughter me yake saki kuka ko yanzu alhinin mutuwar mamanne ?” Zainab da kanar jira take , ta ɗago kai ta kalli momy ta fashe da kuka ,bayan ta share hawayenne tace “momy baba …baba … cikin rashin fahimta momy tace “to me baba yayi ?cikin kuka Zainab tace “momy akwai wata rana , lokacin watan mama biyar da rasuwa .

Ranar baba ya shigo ya sami ƴan matan maƙotanmu ƙawaye na su uku ,muna zaune kan tabarma muna hirar islamiya ,cikin faɗa ya fara korarsu har yana iƙirarin duk yarinya ko matar data sake shiga masa gida sai ya illata ta ,haka suka fice da gudu ,tun daga ranar ko an aiko yara basa zuwa gidanmu , da yamma da misalin ƙarfe (4:20) pm ,baba ya shigo hannunsa riƙe da lemun roba ,ya miƙamin tare da cemin inje in kwanta , to ni ban zargi komai ba ,tunda nasan tsakanina da mahaifina ko wasa bamayi , ina gama sha naji jikina ya mutu gabaki ɗaya , daƙyar na rarrafa naje ɗakina na kwanta jikina babu ƙwari ,gashi ina ganina a duniya ne ko a lahira ,sbda gabaki ɗaya bana ganin komai sai duhu ,inaji ina gani baba ya rabani da komai na jikina gashi na kasa ƙwatar kaina sbda koda hannuna bana iya ɗagawa , gashi yaƙi bari inzo gurinku ,tunda abin ya faru na daina fita gashi babu wanda yake leƙo gidanmu suna gudun masifar baba , har nakai wata biyar da faruwar abinda kullum cikin laulayi nake ni a zatona rashin lafiya ne ,ashe shi yasan ko meye yake faruwa ,cikin yana wata bakwai ,ya fito sosai a wata na tara da kwana goma naƙuda ta kamani da safe ƙarfe bakwai( 7:00)am , ranar banyi tsammanin zanci gaba da rauwa a duniya ba ,baba ya kirawo wata likita bama a anguwarmu take ba ,sai ji nayi baba na cewa “likita ki dubata mjinta ne ya tafi ya barta tun cikin na ƙarami ,wasu zafafan hawaye ne suka zubomin badan azabar da nakeji ba babu abinda zaisa ban yiwa baba maganar da zai daɗe bai mance ba”.
Tana kaiwa nan ta fashe da kuka ,momy ma da kukan take tace “Allah zai saka miki insha Allah zakiga sakamako tun a duniya ,to yanzu ina abinda kika haifa ?” momy ta tambayi Zainab cikin ɓacin rai ,baki na rawa Zainab tace “na yar da ita a bola satinta biyu ma lokacin “tasss tasss momy ta wanke Zainab da mari kana tace “ke wacce irin dabba ce wacce irin mara lissafi ce ?halitar Allah abin wasa ne ehe ?”Zainab na riƙe da kumatu tace “momy ki yafemin nakoma ban ganta ba “.
Momy kam ta rasa inda zata sanya ranta taji daɗi gumi ne yake karyo mata ta ko ina duk da AC da fanka dake aiki a ɗakin amma kamar babu , Zainab ma kuka take sosai sbda bata ma gama nadamar abinda ta aikata ba sai yanzu da momy ta tsinka mata mari .

Ƙarfe (2:pm) na ranar Juma’a ,momy ta mance dady ya fice sbda jinta take kamar mara lafiya ga jiri da yake neman yarda ita ,kuma batason gayawa kowa .
Ring ɗin watarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga ,ta amsa tare da sallama ,daga can ɓangaren naji ance “Nasir ne fa na sauya layi shiyasa baki gane ba “
Ƙaƙalo fara’a momy tayi kana tace “ayya ɗan uwana ai naɗau murya ” uncle ɗin yace “Zee tazo koh “
“Eh “
Momy tace kai tsaye.
“Gani a kusa da gidanku nakusa shigowa ” tom momy tace “ta miƙe da sauri taje ta wanko fuskarta ta shafa hoda tazo gurin Zainab tace “maza jeki gyara fuskarki ” a hankali Zainab tashi taje toilet ta wanko fuskarta tasa kwalli ta fito.
Sallamar uncle da su momy sukaji ne yasa momy ƙirƙiro murmushin dole tace “oyoyo da autan Hajiya ganinka sai shekara-shekara “dariya uncle yayi kana ya gaishe da momy suka gaisa da Zainab yace “ya ƙarin haƙuri ?”sukace masa alhmdulilh ,uncle yace “amma dai kin dawo mana kenan ko ? kan Zainab a ƙasa ta kasa cewa komai sai momy da tace “insha Allah kam ta dawo ” uncle yace “masha Allah ni ina Affan ne ?rabona dashi wata shida kenan “momy tace “ɗazun nan dadynsa ya gama yi masa faɗa akan zuwa gurin aiki inaga ya tafi “daganan momy ta tashi ta kawo masa kayan motsa baki ta janyo tebur ɗin gilashin dake ajiye a tsakiyar palon ta ajiye tare da cewa “ina Farida amarya “uncle yace “ai da taso biyoni nace tazo ita kaɗai “momy tayi murmishi kana tace “Allah sarki “.
Daganan suka ɗan taɓa hirarsu har wajen ƙarfe (3:pm) uncle yace zai tafi ya ajiyewa momy 20k yayi musu sallama ,har bakin motarshi suka rakashi sai da ya ɓace suka dawo gida ,suna komawa momy ta ciri 10k taba Zainab tace koda zata buƙaci wani abun.
Suna zaune suna kallo kowannensu da abinda yake saƙawa a ransa , momy batason kaf familynsu kowa yasan abinda ya faru da Zainab dan haka take ta tunani iri-iri , gadai T.V nayi amma kaf ɗinsu babu wanda hankalinsa ke gurin , zuwa ƙarfe( 3:50pm) anshiga sallahar la’asar kasancewar juma’a tanada ƙurarren lokaci , momy ta fara tafiya sallah Zainab ma ta tashi ta wuce ɗakinta ,bayan Zainab ta idar da sallah ta ɗan kushingiɗe bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita .
Har momy ta kammala abincin dare bataji motsin Zainab ba ,ta taho bakin ƙofar tata ta ɗan buɗe kaɗan ta ganta a kwance a kan sallahaya ta girgiza kai ta koma gyara kitchen , sai da ta gyarashi tsaf ta fara ɗibo abincin tana jerewa a dinning , bayan ta kammala ta wuce ɗakinta tayi wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga baƙa mai adon golden ɗin duwatsu masu kyau sai sheƙi suke ga wasu ɗan kunne da sarƙa da momy tasa sunyi mata kyau sosai , kasancewar daga daren ranar Juma’a har assabar da lahadi ,dady baya fita aiki sai ranar litinin yasa momy take bawa ranakun muhimmanci gurin gyara jikinta da fitinannun turaruka masu ɗaukar hankali .
Kiran sallahar mgrib da aka ƙwala ne ya farkar da Zainab daga bacci tayi mamakin baccin da tayi ,ta tashi ta ɗauro alwalah ,sai da akayi isha’i sannan ta fito palo ta zauna kan sofa tare da cewa momy “sannu da aiki momy “sai kuma tayi murmishi tace “momy kinga inda kikayi kyau kuwa ?…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button