SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani gida naga ta shiga ,gidane madai-daici yana ɗauke da ɗakuna uku daga gefe kuma wata matace wacce a ƙalla zatayi 40yrs tana sanye da dogon wando na jeans hannunta riƙe da kuɗaɗe masu yawa , shigowar budurwar da tayi ne da gudu yasa datijuwar cewa shamsiyya mai ya faru na ganki haka ? wacce aka kira da Shamsiya tana huci tare da cuno baki tace “mama wani saurayi ne ya bigeni na fasa wayata nayi ƙoƙarin binsa ya gudu “tsaki maman tayi kana tace “ke nifa banason ki dinga yawan fushi inhar waya ce sai wacce kika zaɓa amma kafin muci gaba da magana inaso kiyi sauri kije ki sallami alhaji Ubaid “waro ido tayi tare da dafe goshi kana tace “ni walhi bani son zuwansa mama dan Allah kice bana nan ” waro ido maman tayi kana tace “ai kuwa baki isa ba ,ko kije ki bashi abinda yake nema ko inci miki mutunci “wata budurwa ce ta fito daga ɗakin dake kallon nasu tana ɗan yamutsa fuska tace “mama Sadiƙ fa yana ƙofar gida kuma yau dai Allah yayi taimako zai ƙaramin 20k ya zamo 50k “tafawa sukayi da maman tace “yawwa ƴar gari kinga irin abin da nakeso gashi ita wannan tana neman wancan attajirin ya gudu mana “ɗagawa budurwar hannu mama tayi kana tace “baby a dawo lafiya “
Da ƙyar Shamsiya ta yarda da zuwa gurin Alhji Ubaid sbda bata ƙaunar irin kwashen mutane haka ,hannunta mama taja tare da kaita wani ɗaki ,ɗakin cike yake da kayan kwalliya da kayan sawa kama daga turaruka mayuka da shu’umar humra da idonka idona da sauransu ,
Tasha mutsika aka sauya mata kaya i zuwa shadda ruwan madara tasha aiki ja tayi kyau sosai tasa mayafi ja da takalmi ta fito ,ganin fuskar babu fara’a yasa mama cewa “haba shamagirl ki ɗayi murmishi man “murmishi tayi badan taso ba wanda yasa point ɗinta dake kumatu loɓawa ta wuce gurin Alhji Ubaid ,tana shiga ta samesa zaune kan sofa wacce inhar sunyi baƙi to ɗakuna biyu nasu ne koda kwana zasuyi , hannunsa riƙe da kofin gilashi yana shan ruwa , jin shigowarta ya sashi ajiye cup ɗin hannunsa yaje da sauri ya rungumeta kasancewer shi ba wani mai ƙiɓa bane amma yana da ɗan jiki badai irin sosai ɗinnan ba, fuskarta a ƙirjinsa ta ɗan…!

Wannan littafin na kudi ne normal grp 300 VIP 600 special 1000 zaki turo da kud’inki ta wannan account d’in 3175689751 Zainab Habibu first Bank shedar biya ta wannan number 08241799224

Idan kuma kati ne zaki d’auki hoton katin ki turomin ta wannan number 08141799224 y’an Niger suyi magana ta wannan number +22784506476 .

MOM ISLAM
[5/12, 12:07 PM] Mom Islam Ce: ????????????????????????
SAHIBUL AMRAT

????️????????????

Funny love and romantic story

Zainab Habib(Mom Islam

            Free page

Ina mai baku haƙuri akan soyayyar da zaku gani a cikin littafin sbda haka labarin yazo ,ina fatan zaku fahimceni

_____________________7-8

Ɗan goga kana tace “barka da isowa “.
Alhji Ubaid dake ƙare mata kallo kamar yau ya taɓa ganinta yace “baby wannan wankan duk ni kaɗai ?” murmishi Shamsiya tayi kana tace “eh naka ne “
Bayan sun zauna tunanin wayar dake hannunta ya faɗo mata ,a zuciyarta tace “duk da farfashewar da gilashin wayar yayi bai hanata yimin amfani ba , sai ta zuba tagumi .
Alhj Ubaid dake karantar yanayinta sbda yaga damuwa ƙarara a fuskarta yaɗa dada matsawa daf da ita kafin yace “mai ƙamshi na tunanin me kike ?” cikin sigar shagwaɓa Shamsiya tace “uhm uhm ba wani mutumi bane ya bigeni wayata ta faɗi ta fashe gashi taƙi kawowa “
Alhj Ubaid dake tsananin son yaji anyi masa shagwaɓa ,ya ɗan jijigata alamar rarrashi kana yace “karki damu inhar waya ce kin samu baki da matsala amma kafin nan a bani abin “
Farr tayi masa da ido kana tace “yanzu kam ai ina period i promise jibi har sai ka gaji “bai wani damu ba ya tuntsire da dariya kasancewar a inda tayi masa magana dole ta ɗauke masa hankali .
Hannunta ya kama suka fito tsakar gida , mama na zaune da redio a hannunta ,duk da Alhj Ubaid yaga mama bai sake mata hannu ba ,itako mama sai murmishi take na jin daɗi.
Suna fita suka nufi gurin motarsa ,haɗaɗɗiyar motace mai kyau har wani fitar da raɓa take fara sol.
Alhj Ubaid ya buɗe mata gaba ta shiga ya shiga mazaunin driver ,bayan sun rufo motar a hankali ya fara driving  yanayi yana satar kallonta ,a wani katafaren shagon siyar da wayoyi naga yayi parking da sauri ya buɗewa Shamsiya ta fito ,ya rufe suka shiga shagon da sallama , amsawa mutanen shagon sukayi tare da yi musu sannu da zuwa , wani daga cikin masu zama a shagonne ya ajiye musu kujerar roba guda biyu , bayan sun zauna Alhj ya kalli Shamsiya kana yace “mai ƙamshina wace iri kikeso ?”murmishi tayi kana tace “duk wacce na samu ” Alhj ya girgiza kai kafin yace “ba girmanki bane dole sai wacce kikeso kamar inda nima na zaɓo tauraruwa ” miƙewa tsaye tayi tare da nuna wani kwalin waya a jiki an nuna google pixel 2 , murmishi kawai Alhjn yayi tare da miƙa ATM ɗinsa , bayan sun miƙa masa pos yasa code aka cire iya adadin kuɗin wayar , jikin Shamsiya har wani tsuma yake tsabar farinciki da jin daɗi , a gurin ta rungume Alhj tare da manna masa kiss aka sanya musu a leda suka fito , kai tsaye hanyar da zata sadasu da gida suka nufa yana driving yana kallonta a karo na biyu yana murmishi , kafin yace “, Me ƙamshi na ” na’am tace “masa fuskarta yalwace da fara’a kasacewar ta kasa ɓoye farincikin dake ranta , Alhj ya nisa tare da rage gudun da yake ya kamo hannunta kafin yace “ada nasan kinyi taraiyya da mazaje da yawa ,a halin yanzu na haneki da kula ko wanne namiji ,bana son tarkace pls ki kiyaye inahar kinaso mu zauna lafiya “tashi ɗaya idon Shamsiya ya sauya i zuwa ja jawur ta share ƙwallar data zubo mata kana tace “ni ban taɓa amimcewa da kownne namiji ba !babu saurayin da yasannni duk wanda ya gaya maka haka wlhi yayi ƙarya ” da sauri Alhj yai parking a gefen hanya a zuciyarsa cewa yake “maganar wannan yarinyar ba abin yarda bane ko kaɗan ,uwarta fa gogaggiyar ƴar bariki ce  , babu wanda bashi da tarihin UWAR BARIKI ta shahara gurin tara maza a gida ,gashi yanzu ƴaƴanta sun gajeta tun kafin ta mutu , tsinkayo muryar Shamsiya yayi tana magana tana cewa “nasan ko ita maman namu bazata amince ba bare kai da kasan gidanmu yayi suna a gari ”  uhm ” Alhj Ubaid yace kana ya kalleta ya kuma kallonta sai kuma yace “nidai ki ajiyemin kanki karki bawa kowa kimin alƙawari yin hakan zai sa in tabbatar ke masoyiyace ta gaske “kallon wayar hannunta tayi ta tuno tsadarta ta kalli Alhjn kafin tace “nayi maka alƙawari ” okay yace dan shi har yanzu yana ganin she is not… a haka suka ƙarasa ƙofar gidansu ta fito shima ya fito , har zata wuce ya tsayar da ita ,kashe mata ido yayi kafin yace “idan kuɗin acct ɗinki sunyi low ki kirani pls ” murmishi tayi kana tace “insha Allah zan kiraka , ta wuce gida shikuma ya shiga mota .
Tana shiga ta samu mama ta tashi a gurin , ta shige ɗakin maman tana cewa “mama zokiga wayata , mama dake kwalliya a uwar ɗaki kasancewar zatayi baƙo bayan isha’i.
Maman tace “Shamagirl shigo ” da sauri ta ƙarasa tana dariya ta ajiye wayar a cinyar mama ,waro ido mama tayi cikin farinciki tace “bayan 100k ɗin daya baki ?”eh Shamsiya tace ” mama tace “to yanzu ba gashi kin samo arziƙi ba ,ana binki da arziƙi kina gudu , dariya sukasa tare da tafawa ,
Sallamar da baby tayi ne yasa mama amsawa tare da cewa “kinga Shamsiya tayi waya ƴar yayi ” ta miƙawa baby wayar , taɓe baki baby tayi kana tace “aikuwa gashi nan Allah ya sanya alkairi “kasancewar murmishin yaƙe take duk basu lur da abinda take ciki ba , ƙasan zucitarta ji  take kamar an caka mata wuƙa ,gefe koma tanajin wataran sai ta ɓatar da Shamsiya a doron ƙasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button