SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

Mai martaba na fita daga sashen Hjya Rabi ta bugi bango ta cakumo wuyan Hindu kana tace “dan ubanki sai da nace miki muje mu rufe bakin ɗan iska amma kika ƙeƙashe ƙasa yanzu gashi nan ai koda Abdullahin ya mutu bakida ƙwaƙƙwaran gado “.
Hindu na kuka tace “Hjya ni a ganina har yanzu lokacɗi bai ƙure ba “tass tass Hjya Rabi ta zubawa Hindu tagwayen maruka kafin tace ,” kin mance a ina kike ? kin mance a nasarauta kike ?kina wasako ?to wannan auren naki har mutuwa kinji na gaya miki kinyiwa kanki babu abinda ya dameni .
Hindu ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro tare da ɗora hannu a kai.
Bayan anyi sallahr azhar lokacin su prince sun fito daga masallaci ,prince na sanye da kayansa na sarauta sunyi masa kyau sun ƙawatashi , shi kuma Abdallah yana sanye da shadda mai tsadar gaske ruwan malmo tayi masa kyau masha Allah,
Tsayawa Abdallah yayi daga  tafiyar da yakeyi ya kalli prince kafin yace “nifa so nake yau inje hira gurin Hindu “prince yayi murmishi kana yace “ai bakada matsala kaje kawai amma kafin nan zamoje ka rakani anguwarsu waccan yarinyar zanci ubanta la’ada waje

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8

Leave a Reply

Back to top button