NOVELSUncategorized

KWARATA 70

 ???? —— 69

           Hihihihihihi yayi wannan munafikar dariya da bana so , saitin wuyana ya ɗora wuƙar dai² maƙoshina lokaci guda na ɗauke numfashina zufa ta ketomin hawaye suka ci gaba da gangarowa nabi Bello da kallo , dariyar ya sakeyi tare da jan majina , yace kin tuna kika tuɓeni kika ɗaukeni video ? Ka turo da dubu
ɗari biyar idan ba haka ba zan watsa su a yanar giza gizo , yayi irin magana na , dakel na haɗi yawun bakina cikin tsoro nace wai me kake so da rayuwata ne ? 

      Bana buƙatar komai a halin yanzu sai mutuwarki , bara in faɗa miki abinda kika kasa sani nine nan na kashe Binna da hannuna , kuma nine na toshe miki kwalwa na maidake kidahumar ƙarfi da yaji nine na haɗa Binna da Hafsa da Amisty suka zama karuwanshi , haka yake jerasu a layi ya hau akan ɗaya ya sauka ya hau ɗaya , nine nan na shirya komai ta yadda ya faɗa wasan caca shine kawai zai fita a caca nayi na mayar dashi ya ƙiya saboda kawai yayi miki alƙawari ya daina yaso ya lalatamin tsarina ne ni kuma kawai na kashe banza , to me Babana yayi maka haka da zafi ? Ke matar da nake so ya maida ita zawara a ranar da nake farin ciki zan shiga daga ciki , da farko na barshi ta tafi Yayan Babanki ya zugani na dawo dashi ni kuma na hura wutar ɗaukar fansa a zuciya , zan gama da matsalar Binna dake na koma wurin ɗayan ɗan iskan saina ƙare kaf ahalinku dan bana buƙatar ganin jinin Binna a saman doron ƙasa , kauda kaina nayi gefe ɗaya ina wani irin gumji nace kaine ka kashemin min Babana……? Nine na kashe shi ko in nuna miki irin zamiyar da kikayi a jikin gawarshi ne ? Yadda nayi ya nunamin kina cewa wayyo Babana karka ka tafi ka barni tashi Babana baza ka mutu ba gani nazo , buɗe idonka kar kayi bacci uwar masu gida wayyo Babana yi murmushi hihihihihi yasha majina jeki……. Ya faɗa tare da so kamin wuƙa a kafaɗata wanda ba haka yaso ba zuciyata ya saita kuma a samanta yaso wuƙar ya shiga…

     Wani irin ihu nayi tare da haɗa hannayena wuri ɗaya ????????idona yana tsiyayyar da hawaye nace na roƙeka karka kasheni , wata “yar iskar rawa yayi da ƙugunshi yace ke kina tunanin zan barki ki rayu bayan nace miki nine na kashe Binna ? Cikin kuka nace ai banji ba , hihihihi yaja majina ƙazamin banza yace sai kin mutu……

     Ci gaba yayi da yankata ina gocewa yanka 3 yayi min a kafaɗa wuyana da bayana , ta ƙasan sa na sulɓe nayi waje da gudu ina ihu , biyoni yayi da wuƙar tsabar toshewar basira yana saina hallakaki nine ajalinki wallahi baki wuce yau sai kin mutu , masu ɗinki da suka fito suma tuni sun tara taron jama’a dan a kawomin taimako , jini sai zuba yakeyi a jikina ina gudu Bello yana bina , da gudu na shigo titi zan tsallaka road in da gidan Dikko yake fitowarshi kenan zai fita , ina dafe wuyana na fara ɗaga hannu dan motocin suna san su wucemu ne , wani irin ihu nayi nace Dikkkkkkkkow na tun kari motocin da gudu kai tsaye , wani irin burki Ashiru ya taka ni kuma na juya dan jin maganar Sultan shine fa Bello ya samu damar sokamin wuƙa a ciki yana cewa saina kashe ki , wani irin yunƙurin amai nayi kamar raina zai fita na ɗagawa Sultan hannu dan bana iya magana….

Da gudu Dikko ya fito daga cikin mota ya zaro idanuwanshi kamar zasu faɗo ƙasa yace me zan gani haka ? Shima Sultan da gudu ya nufo wurin , wani irin gurnani Dikko yayi cikin wata irin murya yace An mata , tare suka iso wurina dashi da Sultan , Sultan yana ƙoƙarin riƙeni Dikko yayi mishi wani irin halbi ya koma can baya wurin motarshi ya faɗi ƙasa , rumgumeni yayi a jikinshi ya riƙe hannu Bello tare dayi mishi wani irin kallo cikin kuka yace An mata me yasa haka ? Bana iya magana kwata² saboda ina tafiya wata rayuwa daban , cikin rawar murya yace riƙeni An mata riƙe Dikkonki ina tare dake babu abinda zai sameki riƙeni mana , ko motsin kirki bana iyawa Dikko kuwa cewa yakeyi daina kuka an mata ba gani nazo ba , yayi maganar cikin sigar tausayi.

      Riƙon da Dikko yayi ma Bello tsabar firgita yasa shi ya suma , jinjina kai Dikko yayi tare da cewa Ashiru ku ɗaukeshi ku shigar min dashi ciki idan na dawo saina tillashi cikin ruwa kada ta cinye shi , ƙasa sukaja banza har zuwa ciki , Dikko kuma ya ɗauki Sultana yayi mota da ita a baya ya zauna yana rungume da ita hawaye yana fita daga cikin idanuwanshi , da gudu Ashiru ya fito daga ciki bayan ya rufe Bello a ɗaki yazo ya shiga mota yaja suka ɓace daga wurin kamar walƙiya.

     Sultan kuwa dakel ya tashi ya shiga mota a wahalce yayin da yake tunanin meya haɗa Sultana da Dikko ? Mutumin da baida mutunci ya raina mutane baisan darajar kowa ba , bai damu da halin ƙunci da wani zai shiga ba kanshi kaɗai ya sani bai san kowa ba , tare da cikin wanda Sultana ta kawo ɗinki shagonsu Sultan ya ɗauki ɗaya sukabi bayan motar Dikko amma iyakar kokontonsu motar ta ɓace babu wanda yasan ta inda tabi ta wuce ,

       Tunda Bello ya tafi ya koma mota dakel zuciyarshi tana mishi wata irin babbakar babbaka kan ragon layya , yana tunanin maganar Bello { nine na tura yarinyar ka ta zama karuwar Binna } kai…… Yayi ihu tare da kaima sitiyari duka yace Allah ka rufamin asiri wannan labarin ya zama a bacci nakejin shi , na shiga 3 ƙanina ɗiyata ta zama karuwarshi wayyo Allahna tada motarshi yayi ya nufi gidanshi cikin tashin hankali , ko da yaje Hafsa bata nan daya tambaya mahaifiyarta tace tana ƙofar marusa gidansu.

       Cikin tsananin tashin hankali ya fito yaci taya ya nufi ƙofar marusa , a halin tashin hankali ya samu Hafsa data farfaɗo daga suma sai tace wayyo Allahna Ba Binna saita koma luww , ita Hajiya bata san suna Binna ba ita Aliyu ta sani , Dady kuma shi yasan Binna , Hafsa na sake dawowa Dady yace Hafsa me Binna yayi miki ne ? Dady me yasa ? Ya akayi kuka bari duniya ya ruɗa Hajiya ? Kun watsa kan gidanku kun gurɓata familynku ƙani yayi tarayya da ɗiyar Yayanshi , Yaya kuma yana neman ɗiyar ƙaninshi kaico da wannan ahali tirr daku , mutuwa kizo ki tafi da Hafsatu ina zamu kai wannan abun kunya , tashi tayi da gudu ta nufi rijiya tana cewa saina faɗa wallahi saina faɗa dakel aka riƙe Hafsa , tana ƙwacewa tayi kicin da gudu ta ɗauko galan ɗin kalanzir ta ɗagashi taci gaba da kwankwaɗa shima dakel Dady ya kwaceshi bayan tasha ta ƙoshi layi ta farayi tana mutuwa kizo taho na shirya taho ki tafi dani wurin Ba Binna ,….

Tun tana layi har ta faɗi ƙasa tana cewa kai waccan Hajiyar ƙarshenki bazaiyi miki kyau ba tsohuwar munafika “yar gadon san abun duniya mai kwaɗayin duniya kuma wallahi saikin mutu mutuwarki bazai miki kyau ba , tirr da hali irin naki azzalimar tsohuwa tari Hafsa ta farayi ƙuhul׳ sannan tace tsabar maitar duniya tou idan baki sani ba Aliyun da kike magana shine yayimin ciki kwanakin baya….

      Wani irin juyi Dady yaji duniya tayi masa da gudu , cikin kuka Hafsa tayi dariya kamar mahaukaciya tace da nasan Ba Binna ƙaninka ne idan na bari an fitar da cikin nan Allah ya tsinemin albarka saina haifeshi idan namiji ne sunanka zan saka masa da mace ce sunan mayya Hajiya zan saka , wani irin ihu tayi tana cewa ni nafi san mutuwa dan Allah mutuwa kizo ina nan ƙofar marusa gidan Hajiya kizo ki tafi dani bana san rayuwar gaba , cikin kuka Dady yace ki daina kuka Hafsa bazaki mutu ba , girgiza kai tayi cewa mutuwa itace kaɗai natsuwa a gareni….

     Murmushi tayi mai ciwo cewa Ba Binna ɗan gayu wayayye dashi ɗan boko kisan farko amma tsabar mugunta kuka molaƙe tare da tamiƙe mishi rayuwa , bazan manta ba nace masa Ba Binna ciki gareni fa , yayi murmushi yace Doughter ya akayi kika yi ciki ? Ko ƙauye fa an waye a binni sai kawai kikazo kika kwanta kika kwashi ciki , yana cemin Doughter saboda “yar sa ashe ɗiyarshi ce ta gaskiya………..? Nace masa Baba yanzu ya za’ayi nima bansan yadda za’ayi ba , na tursasa masa akan a fitar da cikin ya nuna shifa ba ruwanshi bana san ɓacin ransa dan idan ya juyawa abu baya ya gama dashi ni kuma bana san rabuwa dashi shi , ku kuma gida da kuka gane ina da ciki kukaje kuka zubar dashi , Allah duk mai sa hannu a kisan Ba Binna ubangiji ka tagayyara mishi rayuwa…… Tari ya ƙwace mata sosai mimmiƙewa tayi kamar wacce ake zare ma rai ta sake somewa , ɗaukarta akayi itama aka nufi asibiti da ita.

       Wata irin dariya sukeyi gaba ɗayansu suna cikin farin ciki tsakanin Jiddah da Mardiyya Al ‘ Ameen yake basu labari cewa yaufa an shafe labarinta a duniya , Mardiyya tace Uncle kana wurin ne ? Al ‘ Ameen yace bana nan Nabeela ta aikeni gidansu ƙawarta ina shiga goruba naga banzar ta fito guje kinji daɗin da naji ? Shi kuma ya biyota da wuƙa ina ta murna za’a kashe ta kawai sai naga mai gida ni kuma na ruga banma tsaya ba kar yace hadani , bayan na dawo daga inda zanje nake tambaya akacemin ai ta mutu…

     Cikin jin daɗi Jiddah tace damuwa ya ƙare , Mardiyya kuma tace Uncle mun goge ƙatuwar damuwa danni wannan matsalar ta gabana kallon ciki sati ɗaya nake mata , Jiddah bata san da ita ake ba ta rungume Mardiyya sukaci gaba da murna..

       Misalin 9:00pm Sultana ce kwance saman gadon asibiti bayan likitoci sunyi mata duk wani abu daya kamata na bata kariya daga yanka²n da akayi mata , su 3 ne a ɗakin Sultana Ashiru yana tsaye gefen gadon Dikko kuma yana zaune saman kujera gaban gadon ya kwantar da kanshi saman gadon yana tunane² , Ashiru ne ya matso kusa dashi ya miƙa mishi wayarshi cewa mai gida maman Sultana ke kira , ansa Dikko yayi ya kara wayar a kunnenshi bayan ya ɗauka.

     Cikin kuka Inna tace Dikko me ya faru ne ? Sai kirana akeyi Sultana bata lafiya ance ɗan gwamna ya tafi da ita me tayi mishi ne ? Me tayi mishi ? yaro mara mutunci tun ina tare da mahaifinta ya addabi rayuwar Sultana yanzu kuma meya sake dawo dashi cikin rayuwarta ? Sassauta kukanta tayi cewa ina Sultana……..?

       Murmushi Dikko yayi da gefen bakinshi yace Mama waye ɗan gwamna ? Ni ina zansan ɗan iska mara mutunci , kin taɓa ganinshi ne ? Kuma ya akayi kika san ya shiga rayuwar An mata ? Nima ban sani ba , ban sani ba tayi maganar tana sake fashewa da kuka , Dikko yace Mama me kike so ayima ɗan gwamna ne ? Ni ya fita daga rayuwar ɗiyata kawai , idan yace bazai iya ba ya zakiyi dashi ? Saima ya fita tunda ba tare aka haifesu ba dan ubanshi , jinjina kai Dikko yayi cewa to karki damu ina tare da ita a halin yanzu , kana ina ne ? Muna asibiti faɗa mata asibitin yayi tare da kashe wayarshi.

     Miƙewa Dikko yayi cewa Ashiru zanje gida zan dawo misalin 1:30am bana san kowa ya zauna duk wanda yazo yaga An mata kace ya tafi kawai asibiti bata buƙatar majinyata , jinjina kai Ashiru yayi alamar gamsuwa shi kuma Dikko ya fice daga ɗakin da sauri….

       Ba’a wani ɗauki lokaci ba Sultan ya iso dashi da Kaka da Mami sai Abba su kaɗai suka zo , dan yayyen Inna cewa sukayi Allah ma yasa ta mutu uban kowa ya huta da jinin katafi² , gaba ɗayansu sun tausawa Sultana , sun daɗe a asibitin ganin Abba da Mami zasu tafi yasa Ashiru yace Hajiya ai kin ganeni ko ? Eh na gane ka kaine ka maido Maryam gida , Ashiru yace yawwa tou kuyi tafiyarku gida nan suna da malaman jinya , gaba ɗayansu suka tafi amma nayi imani da ɗiyar wani ce a cikinsu babu yadda za’ayi su tafi su barta da wannan darjejen ƙaton a ɗaki.

         Yaya kace idan ina da buƙatarka na sanar dakai , Jiddah ce tsaye a gaban Dikko dake saka kaya take mishi wannan maganar wani irin kallo Dikko yayi mata cewa yanzu kina da buƙata na ne ? Eh , idan mace tana san kasancewa da mijinta ai bada baki take faɗa ba tunda ba magana bace da zaki faɗa na baki ansa , matsawa yayi ya kamota jikinshi yana cewa waye yace da baki ake neman miji ? Murmushi Jiddah tayi shima murmushi yayi dan Allah ya sani dama a takure yake baya so ne ya shiga haƙƙinta shi yasa ya ƙyaleta harsai ta buƙata da kanta , yana riƙeta ya aika mata da takardar neman yarjejeni babu ɓata lokaci Jiddah ta amince gado suka koma Dikko yaci gaba dayi mata sign……

       Bayan sati ɗaya  !

      Na samu sauƙi sai abinda ba’a rasa ba , kuma duk kwanaki bakwai ɗin nan Dikko yake kwana dani Ashiru kuma saiya tafi , idan safiya tayi Ashiru yake dawowa su yini da Kaka Dikko kuma sai dare yake dawowa ya kwana ,

     Hafsa kuwa saida aka saka mata wata roba a gefen cibiyarta ake fitar da dattin kalanzir in data sha dan ta ɓanɓameshi da yawa , ita kuma Amisty ke jinyarta idan Amisty ta yini sai Mom inta ta kwana.

       Ga hidimar aurena kuma babu abinda aka fasa har an gurzo katinan ɗaurin aure nima na ansa na ajiyewa Dikko nashi idan yazo da daddare zan bashi dan idan Allah ya kaimu gobe lafiya akace za’ayi sallameni kuma Inna itama gobe zata dawo idan Allah ya kaimu muna cikin masu rayuwa.

      Bello kuwa yaci duka na bala’e a wurin Dikko saida ya lalata mishi ido ɗaya sannan ya tambaye shi abinda ya haɗashi da An mata ? Bello yace ba komai , Dikko yace jin daɗi kawai kakeji ka kasheta ? Bello yayi shiru Dikko yace tou ko ka faɗamin abinda ya haɗaku har ka yayyakata da wuƙa ko kuma na jefaka cikin ruwa kada ta haɗeye ka banza ,

      Munafinci yayi ma Dikko yace wani Yayan Babanta yasa shi ya kasheta saboda tana ta tayar da hankali ta anshi gadon su shine ni kuma ya bani kuɗi yace na kasheta , waye Yayan Baban nata ? Inda Dady yake zama da number wayarshi Bello ya bada , Dikko yace aje a ɗaukoshi cikin mintuna biyar , motoci suka hau suka tafi ɗauko Dady dan tunda Bello ya suma daya farko yaga Dikko sai ya koma yauma abinda yasa bai suma ba Dikko yace kana sake somewa wallahi saina sa an rufe ka da ranka…..

        Bayan masu tafiya ɗauko Dady sun tafi Dikko ya kalli Bello yace dama kai ba wani ba inajin haushin ka dan ubanka yayi maganar yana yankawa Bello wani zaburarren mari harsai da haƙorinshi na ƙurya ya fita , Dikko yace ka ganeni ko ? Yayi maganar yana kai mishi wani irin halbi harsai daya fitar da jini daga bakinshi , duk kaine matsalata wai meme yasa bazan kashe ka ba…….?

     Da ido ɗaya ya kalli Dikko dan ɗayan ya daina gani kwata² cewa kayi haƙuri , Dikko yace ai dama ba yanzu zan kashe ka ba kana tunanin zaka mutu cikin sauƙi ka sokawa “Yar matana wuƙa ? Kayimin tabunna a jiki matata ? Ka san irin mutuwar da zakayi ? Bello yayi shiru , Dikko yace to kullum saina reɗi sokar jikinka ina ba karnuka harsai ka ƙare.

      A dai² lokacin da aka shigo da Dady , bayan an fiddoshi ne Dikko yaga mijin ƙawar Momy ne , ƙasa da sama ya kalleshi cikin kallon rainin wayau sannan yace ku tattarsu ku tafi dasu , jan Bello akayi aka sakashi a mota shima Dady mota ya koma suka tafi dasu daga gidan , shi kuma Dikko ya nufi asibiti….

      A asibiti ya samu Sultan , fuskar nan a haɗe ba ɗan sakin fuska ni bana san wannan ɗabi’ar kullum ran mutum a haɗe kamar an aiko da saƙon mutuwa gareshi , wani irin ƙazantaccen kallo yayi ma Sultan dole tasashi ya tashi daga saman gadon ya nufi kujera zai zauna amma Dikko ya janye kujerar da ƙafa ya matso da ita kusa da gadon ya zauna yana cewa kinsha magani ,

      Banza nayi dashi ban bashi ansa ba na kalli Sultan nace kazo ka zauna mana , murmushi yayi tare da cewa ai tafiya ma zanyi , nima murmushin nayi cewa karkaje yanzu ka tsaya , kallon agogon hannunshi yayi yana cewa dare yayi bara inje sai Allah ya kaimu Allah ya tsare hanya nayi masa yayi ma Ashiru saida safe ya fita , yana fita Dikko yace Ashiru saida safe , fita Ashirun yayi bayan yamin saida safe…

      Ashiru yana fita yaje ya rufe ƙofar da makulli ya dawo ya zauna kusa dani yace idan ina miki magana baki bani ansa saina ɓata miki rai “yar rainin hankali kawai , gyara zama nayi cewa ai dama saboda baƙar zuciyarka yasa bazan iya aurenka ba nayi maganar tare da ciro katin ɗaurin aurena daga ƙasan pilo na miƙa mishi cewa wallahi Dikko ina sanka amma bazan iya aurenka ba har abadan duniya ,

     Ansar katin yayi yana murmushi , ni kuma naci gaba da cewa kai a rayuwarka babu abinda ka sani sai zafin kai , doke² , ɗaure fuska gaka mahaukaci ga aljannu kamar iccen tsamiya ni taurin kai , kai kuma zuciya talauci da arziƙi basa zama wuri ɗaya dole idan ɗaya yazo ɗaya ya tafi , idan arziƙi yana nan talauci zai tafi , idan talauci yana nan arziƙi yazo dole talauci zai kama gaban shi , naji shi wannan ɗin kina sansan ne ? Eh ina sansa , tou ai ba akomai An mata nima da kika ga na kafe kai da fata na aureki bawai dan ra’ayina bane ba a , a muradin zuciya ne itace ta tirsasa amma farin cikinta a kullum bai wuce ta ganki cikin farin ciki ba , duk yadda take sanki dole zata kulle ne idan taga kin samu inda zakije kiyi farin ciki , kin gane ko ? 

      Kallona yayi da kallonshi mai tayar da tsikar jiki yace ina miki fatan alkairi ubangiji yasa alkairi ya baku zaman lafiya ai da kin faɗamin tun a gabanshi dana mishi Allah sa alkairi kuma saina riƙe hannunshi in jinjina masa cewa ina tayaka murna namiji mai sa’ar rayuwa.

     Faɗamin yanzu me kike so na baki gudumuwa a matsayina na babban abokin amarya ? Yayi maganar cikin ƙarfin hali damuwa kwance a idonshi , bana san komai domin babu abinda ba’ayimin ba a gidanmu , murmushi mai ciwo ya sakeyi cewa yi haƙuri ai badan sun gaza ba abokin amarya fa…..? 

     Nace bana so , da hannunshi ya nune cewa to , to yi haƙuri ya canja maganar da cewa maganar wasu kuɗin gado da kike ta wahalar da kanki ba dare ba rana kiyi haƙuri ki daina maganar kuɗin ki faɗamin adadin miliyoyin da kike buƙata na baki ki bawa “yan gidanku a rufe matsalar , kallonshi nayi cikin idona nace ko naira ɗaya ne saina ansa domin wannan gadon shi zaisa na tabbatar cewa shima Babana yana da galihu , ganin na hasala da yawa ya miƙe yana warware kafet cewa bazance komai ba amarya tsautsayi gareta lallaɓa ta akeyi , a dai² lokacin daya dawo ɗaukar wayoyinshi na watsosu ƙasa ina kuka , baimin magana ba ya duƙa ya ɗauka ya koma saman kafet ya kwanata yana latse²nshi a waya.

      Da gudu na sauko daga saman gado na koma wurin Dikko ina kuka , juyamin baya yayi ya sargafa bluetooth a kunnenshi fuskar nan babu wasa a cikinta yaci gaba da abinda ya shafeshi , gabanshi na koma cikin kuka nace bana sanka , murmushi yayi da gefen bakinshi hawaye kwance a idonshi yana kallon wayarshi amma baiyimin magana ba ,

      Gemunshi na fizga cikin ɓacin rai , wata “yar ƙara yayi kaɗan cikin salon ɗaukar hankali wani abu naji yanamin yawo a jiki , gyara gemun yayi yana cewa saina dakeki zakije kiyi bacci ko ? Cikin kuka nace ka dakeni da Allah dakeni Dikko na ƙarasa maganar ina shiga jikinshi , da sauri ya fizgi wani irin numfashi ya fitar dashi ta bakinshi tare da lumshe idanuwanshi ya sauke ajiyar zuciya a wahalce cikin murya mai sa mutum ya shiga yanayi yace An mata fita daga jikina don Allah , bazan fita ba , yi haƙuri An ma fita kinji “Yar matana yayi maganar cikin sigar lallashi ƙara riƙeshi nayi ina kuka da ƙarfin bala’e ya ɓanɓareni daga jikinshi ya mareni , da sauri na tashi na koma saman gado na kwanta ina kuka , tsoki yayi ya koma ya kwanta cikin ɓacin rai yana magana ƙasa².

      Kuka naci gaba dayi ni ba kukan marin nake ba kukan rabuwa da Dikko ne jibi kamar yanzu ina gidan Sultan , cikin kuka nace kuma ko rarrashin mace baka iya ba , ban iya ba kuma bazan iya ba , tunda kin samu wanda zai lallashe ki sai kije ya lallasheki , ai dan bayanan da kaga yadda ake tarairayar mace , waye yace namiji sai a gaban mace zai tarairayeta ki kirashi a waya yanzu ba kina da number shi ba ? Kirashi yasa ya miki natsuwa sakaran banza mai baƙuwar soyayya , bazan kira ba , sai Dikko da kika raina…….? Mtsw kimma ja ma kanki bara in sake jin ko tarinki kikaga yadda zanyi sukuwa samanki “yar yarinya kawai dake.

      Shiru nayi tare dajan bargo zan lulluɓe yace sauka ki kashe mana waccan fitilar da kika kunna ma mutane , murguɗa bakina nayi ban sake ko motsi ba har bacci ya ɗaukeni kuma ban kashe fitilar ba , shi baya san kwanciya da fitila yace idan fitalar ɗaki yana a kunne wai ƙwalwa bata daina aiki , idan aka akashe shine itama kwalwa zata huta , Dikko kuwa jin Sultana tayi shiru ya tabbatar mishi da tayi bacci tashi yayi cikin damuwa yazo gaban gadon ya ƙurawa An mata ido a zuciyarshi yace wannan “yar yarinya Allah yayi mata tsatstsagar masifa , Allah yasa mijin naki yayi haƙuri da yarintarki ubangiji yasa ya riƙeki da amana Allah ya wadata mishi zuciyarshi da tausayinki An mata , haka Allah ya hukunta bani ne nake da rabo akanki ba saboda rashin haƙuri na cinye nawa rabon tun bisa titi…

        Ina sanki ׳ Allah ka bani haƙuri da dangana akan rashin An mata , a bayyane yace haƙuri ma ai ya zama na dole haka Allah ya ƙaddara yadda da ƙaddara kuma imani ne , kashe fitilar yayi ya koma ya kwanta yana ta maimaita kalmar Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un , a wannan dare har garin Allah ya waye Dikko baiyi bacci ba yana cikin tashin hankali.

      Misalin 11:09am aka bamu sallama , Sultan yazo ya ɗaukeni Dikko yayi mishi fatan alkairi tare dayi mishi nasiha wai An mata yarinya ce ya lallaɓata idan kuma tayi mishi laifi yazo ya faɗa mishi shine kaɗai maganinta , murmushi Sultan yayi yace ai baza tayi ba , Dikko yace ina san haka kuma a kula ta riƙa shan magani akan lokaci Sultan yace insha Allah har zamu tafi Dikko ya dakatar da Sultan yace inzo fita nayi naje wurinshi gefe muka matsa wurin motarshi yace An mata nasan kina da rufin asiri kuma duk wanda ya rufawa wani asiri Allah zai rufa mishi duniya da lahira dan Allah karki sake kiba kowa labarin abinda nayi miki ki rufamin asiri don Allah kinji ? Fashewa nayi da kuka ina ƙoƙarin rungumeshi yaja baya yana cewa mijinki yana kallonki jeki Allah yasa alkairi ngode.

      Cikin kuka na koma mota Dikko ma ya shiga tashi yaja shine gaba mune baya , yana fita ya ɗauki hanya da tuƙinshi na ganganci kafin na ƙetfa ido tuni ya ɓace ko ƙurar motarshi babu , ci gaba nayi da zubar da hawaye yanayin Dikko yana burgewa komai nashi nidai yayimin Dikko yana da shiga rai sosai yana da farin jini amma matsalarshi zafin kai.

     Har muka isa gida kuka nakeyi , ina fita daga mota nacema Sultan ya bari inyi wanka in dawo yace to….

pls click on our ads



(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button