MADADI Page 101 to 110

Bayan Baba malam ya gama Baba talatu ta d’ora nata, Najaatu na kuka tace”Insha Allah ba zan baku kunya ba nayi al’kawarin zan zauna da mijina har karshen rayuwata sannan zanyi masa biyayya kamar yanda Allah ya umarce ni da nayi sannan ina kara rokon ku da ku yafe min abinda nayi muku a baya da yardar Allah wannan karon ba zan baku kunya ba.
Baba Talatu da baba malam sun ji mutukar dadi da maganarta, Baba malam yace.”Allah yay miki albarka ya baki zuria mai albarka.” Miqewa yay yasa takalmansa ya fita, Baba Talatu tace” Ki shiga dakina wajan gado zaki ga wasu kaya a cikin leda viva Hafsa ‘yar gidan Yakumbo ce tace idan kin shigo a baki ban dai bud’a naga ko menene a ciki ba.
A sanyaye ta miqe ta nufi dakin….Kayan ta d’auko a nutse ta shiga fito dasu kayan mata ne zuma cikin wata jarka sai tsumi shima a jarka sai kuma garin magani irin wanda akesha da nono ko madara roba kusan biyar ko wanne da nau’insa, Hasken wayarta ta kunna tana dudduba maganin gami da bayanin dake jikinsa, Murmushi tayi a hankali tace lallai akwai dirama bari na fara da wannan biyun.
Zuma ta dauka kawai ta bud’e bakin abin ta kafa kai tana kwankwad’a! sai da tasha da yawa tukkuna ta dauki jarkar tsumi din a maimakon ta samo kofi ta tsiyaya shima bude murfi kawai tayi ta kafa kai tasha yanda take so ta rufe….Tana kokarin mayar da kayan cikin ledarsu taji sallamar aunty Maryam, tace ashe bata tafi ba, tana jin sanda take tambaya baba ina take, tace mata tana cikin daki….Kafin ma ta gama mayar da kayan cikin ledarsu ta shigo dakin.
“Aunty Maryam baki tafi ba dama.”? Aunty maryam ta samu guri ta zauna tare da ajiye fulas din dake hannunta, Tace” saboda ke na dawo ai, ga kazar amarci nan ba zan tashi daga gurin nan ba sai kin cinye tas kin tsotse kashin.
Dariya tasa tace”Lallai aunty Maryam kema gudumawar da zaki bani kenan kinga fa wasu maganin da Aunty Hafsa ta Yakumbo ta kawo min.”
aunty maryam ta shiga duba maganin tana murmushi tace”Lallai ta gwangwaje ki sosai sai ki mayar da hankali kina sha a kai a kai! zasu taimaka miki sosai.”
‘Yar dariya tayi tace”Ni wallahi aunty maryam da kun barni haka sai yafi meye duk sai kun tashi hankalin ku nifa ina da ni’ima daidai gwargwago ba sai nasha wani magani ba.
Aunty maryam ta harareta tare da fadin “Mara wayo kawai to ko kina da ni’ima sai akace ba zaki ‘kara wata ba, okey da haka kike so kije masa babu gyara yaji ki lami! humm to wallahi ba kunyar ki zaiji ba zai iya barinki ya tafi inda zai samu gamsuwa saboda haka kiyi hattara da gyara kanki har wani cewa kike kina da ni’ima a’ina kikayi ni’imar mtwws! Najaatu ban san sanda zakiyi wayo ba wallahi, zaki zauna tsakanin kishiyoyi idan suka fiki kula da kansu kin shiga uku gwara ki san yanda al’amarin yake tun yanzu….Duk wata mace mutukar tana da kishiya to burinta ta fita a gurin miji kiyi kokarin ganin kin zama tauraruwa akan kishiyoyinki idan kuma kin zauna sakarci shikkenan
Najaatu jikinta yay sanyi Zainab ce kawai ta fad’o mata ta lura yarinyar nada wayo sosai dole ne ma ta zage damtse a kanta dan ta fahimci shima yana ji da ita ko ga yanayin yanda yake kula da ita da sauransu…..Fulas din gaban aunty maryam din ta janyo gabanta ta bude kamshi ya bigi hancinta kamshin tattasai dana magani amma dai maganin yafi yawa a ciki….Hannu tasa tayi bisimillah a nutse ta soma ci tana had’awa da ruwan roman
Najaatu tas ta cinye kazar ta shanye roman aunty Maryam ta rufe fulas dinta ta miqe tare da fadin”to ni zan tafi sai gobe idan munzo rakiyar amarya.
Najaatu mikewa tayi tana sud’e hannunta tace”Wai dan Allah da gaske gobe zan tare aunty Maryam wallahi bana so na tare gobe nafi so adan kwana biyu tukkuna.” Aunty maryam harararta tayi tace “Sai kiyi ai ni har gidan da zaki zauna ma na gani a waya….Gidanki daban mai kyau da burgewa babu abinda babu a ciki gaskiya yay kyau sosai wallahi.” Gabanta na faduwa tace”Wane unguwa ne ni wallahi daya sani ya had’ani dasu Aunty Halisan zaifi…..Aunty Maryam tace”Aa gwara ki zauna ke kadai yafi mutumci watakila shima yana da manufarsa akan hakan saboda haka ki kwantar da hankalin ki gidanki na rijiyar zaki wajejan massalacin jumaa na d’an sarari.” Najaatu shuru kawai tayi tana addua Allah yasa haka shi yafi alkairi amma dai da za’a bi son ranta to da tafi so ta zauna gida daya dasu Halisa……Aunty maryam na kokarin fita daga gidan Yaya Ramlatu ta shigo da Daddy a hannunta yana kukan a mutunce suka gaisa da juna kafin ta shige cikin gidan da sauri…. Najaatu na wanke hannunta tayi saurin karasawa ta kar’beshi da fad’in ”Ashe ya tashi lokacin dana fito na barshi a daki yana bacci.” Ya Ramlatu tace”Ai ina tunanin baki dade da fita ba ya tashi, na bashi costand ya’ki kar’ba nono kawai yake bukata….Baba Talatu ta fito daga kicin tare da fadin “Ai yay kokari ma ace yaro ya tashi a bacci sama da awa guda bai ci abinci ba ai dole yayi kuka ai sai ki zauna ki bashi yasha.
Da sauri ta zauna gefan tabarma ta fito da nono tasa masa a baki, aikuwa ya kama da sauri ya shiga tsotsa yana sauke ajiyar zuciyaÂ
Yaya Ramlatu tace” Bari naje sai kin shigo.” A sanyaye tace”Yaya Ramltu da kyar idan zan dawo wallahi kunya nake ji mutane tun dazu suke kallona.” Ramlatu ta bude baki tana kallonta cike da mamaki tace”To ai tuntuni kowa ya kama gabansa mu kadai ne a gidan
Shuru tayi tana nazari kafin tace”Allah kunyar hajia nake kice mata sai gobe zan shigo.” Ya Ramlatu tayi murmushi tace”Bakiyi laifi ba Najaatu dan dama dole haka zata iya kasancewa shikkenan bari na kawo miki abubuwan da zaki bukata ko.”