NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 37 – 38

  *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_
                 *_Bilyn Abdull ce????????_*
                   *_[37➖38]_*   
…………..Da sauri Umma ta sha gaban Abba dake nufar Jiddah tamkar wani bajimi, ture Ummar yayi yasaka k’afa
ya tad’e Jiddah dake Neman guduwa.
       Fad’uwa tayi k’asa akan hannunta, dan haka ta fashe dakuka saboda zafin daya ratsata.
     Waya ya jefa Mata, “’Dauki wayar nan kikira Wanda aka d’aura miki aure dashi yanzunan kice ya sakeki”.
     Kuka Jiddah takuma fashewa dashi, ta d’auki wayar ta rik’e, da sauri Umma ta kwace tana fad’in “Bazata kirashinba, Kai mizai hanaka kiranshi kace ya saketan?”.
       “Yagana! Yagana!! Kina shigarmin hanci da yawafa”.
     “To mizai hana ka fyatoni ka huta, wlhy wannan karon duk abinda zakayi sai dai kayi amma bazan d’auki wannan masifar ba…….”
      A fusace ya d’aga hannu zai Mari Umma 
     “Wlhy karka sake ka ta6ata!!”. ‘Yaruwaiya dasuka shigo yanzu babu dad’ewa tafad’a a matuk’ar tsawace, dan sunji mafi yawan abinda ke faruwa’.
     Cak Abba ya dakata, bai marentanba baikuma sauke hannunsa ba.
     Zarah da Balu sukazo suka d’aga Jiddah dake kuka zaune, hannunta harya fara kumbura alamar taji ciwo. Itama Yaruwaiya zuwa tai ta janye hannun Umma suka bar Abba a wajen, yakasa motsi balle dogon tari.
       Hayawaye kawai Umma taji sun gangaro Mata, duk k’ok’arinta Na 6oye mugayen halayyar Abba ga danginta yau sai da ya tonama kansa asiri, shekaru ashirin suna tare bata ta6a Kai k’ararsa wajen iyayentaba idan yamata Abu, aganinta hakuri shine maganin komai, sannan yawan Kai k’arar miji gidanku ko gidansu tamkar zubarwa da kanku darajane, dan iyayenka zasu rage ganin darajarsa, idan kuma iyayensane suma zasu rage ganin darajarka.
           Zarah da Jiddah ma hawaye suketayi, ga hannunta dake Mata azabar zogi, shiru babu Wanda ya iya cewa uffan a cikinsu, kowa da abinda zuciyarsa take sak’awa.
       A tsakar gida kam kwafa Abba yayi yafita yanamai jin haushin Yaruwaiya, amma ko giyar wake yasha bai isa cigaba da abinda yay niyyaba, dan Yaruwaiya ba kanwar lasa baceba, kad’an daga aikints ta ketashi gaban y’ay’ansa.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

          Tuni zufa ta jik’e hajia Hindu saboda azabar da k’afarta kemata, k’arar data kwallane yasaka kalifa zuwa d’akin. 
     “Momy miya sameki?”.
     “Kalifa Abbanku ne ya karyamin k’afa”. Tafad’a cikin jin azaba. Gabanta yazo ya zube yana Kama k’afar dahar tafara kumbura, “Momy mikikai masa yay miki haka?”.
      “Babu abinda nai masa kalifa, dan kawai Na fad’a masa gaskiyane”.
     “Kiyi hak’uri Umma ALLAH ya saka miki, bara Na Kira direba mukaiki asibiti.

        Da k’yar Kalifa ya iya taimakama Hindu tafito suka shiga mota, Wanda aka aiko daga makarantar su kalifa danyaje da Abba ganin yanda jama’ar gidan suke kamar a tashin hankali saiya sulale ya koma makaranta Kai rahoto.
       A asibiti kam anduba hajia Hindu data samu targad’e a k’afa, nanda akaimata gyaran datasha azaba. Magunguna aka bata suka dawo gida.
      Saidaifa a k’asan zuciyarta tanajin bazata bar abinda Abba yay mata yatafi a banzaba, dolene saita rama wlhy. Tana zaune afalo tana cika da batsewa Abba ya shigo, harara tashiga watsa masa, amma ko kallon inda take baiyiba yay shigewarsa d’akinsa zuciyarsa nacigaba da tafasa, shi yanzu a ina zai samo wad’annan kud’ad’en yabama Alhaji garba? Kodai shawarar Hajia Hindu zaibi yabashi Zarah? To amma kuma shi Alhaji garban zai amince ne?, kansa yadafe cikin matsananciyar damuwa, gaba d’aya yama rasa miya dace yayine?. Yana cikin wannan halin wayarsa tashiga ruri, sharewa yayi tamkar bazai d’aukaba, saikuma yaja tsaki yana fisgo wayar saikace itace tai masa laifin.
     Daga makarantar su kalifa ne, a fusace ya d’aga, ko sauraren sallamar da akai masa baiyiba yace, “Minene?”.
        “Babu komai Alhaji, akan maganar yaronkane da muka turo da d’an rakiya, yadawo mana babu Kai babu yaron kuma”.
       “Kaga da ALLAH karku dameni, harma nawa kalifa yake dazai zauna fad’a dawani akan mace, nifa banason sharri, suje can sunema Wanda ya fasama d’ansu kai, Mtsoww aikin banza kawai”. K’itt ya yanke wayar.
       Yin haka dakamar mintuna talatin saiga mai gadi yashigo wai ga y’an sanda sunason ganin Alhaji.
     Da mamaki Hajia Hindu dake tule a zaune tace, “Y’an sanda kuma? To miya faru to?”.
      “Wlhy hajia bansaniba”.
      Kalifa ta kwalama Kira, yafito yana kumbura baki da k’unk’unin antasoshi yana hutawa, “Kaje kakira Abbanku yayi bak’i kazonan kana cunomin baki”.
     Tafiya yay d’akin Abba yana mangara Kai dacigaba da k’unk’uninsa. Babu jimasa suka fito tare, yanzuma Abba baiko kalli hajia Hindu ba yafice kalifa Na biye dashi.
       Koda suka fito kalifa yaga y’an sanda da Baban yaron dasukayi fad’a saiya juya zai gudu cikin gida, amma d’an sanda d’aya yay ram dashi.
      Haukace musu Abba yayi da masifa, ko kad’an basu saurareshiba suka tafi da Kalifa dake kuka. Hajia Hindu ma data rarrafo danjin masifar Abba da kukan kalifa kukan ta sanya tana rok’onsu su dawo Mata da yaronta, amma kobi takantama basuyiba.


       Abifa yayma Abba yawa????????????.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

           Yau Aliyu a masallacin k’ofar gidansu yay sallar magriba saboda akwai majalisi da sukan shirya Na k’arshen kowane wata da akan gabatar bisa tsarin malam.
     Masallacin yacika taf da magidanta, samari, harma da tsofaffi, Ana idar da sallar isha’i Sheikh Aliyu yafara gudanar da wa’azi mai taken *DAMI MUKA SHIRYA TAFIYA LAHIRA?* , masallacin yayi tsait, daga muryar malam mustafa dake jan bak’i saikuma Sheikh Aliyu dake fassara cikin tsantsar ilimi da kuma fad’ad’a kowace aya domin a fahimta, lokaci-lokaci mutane kanyi kabbara, jikinsu dukyayi sanyi saboda tsoro, har zuwa k’arfe goma da rabi aka fara karanto tambayoyi.
      Kafin yabada amsar tambayar farko yacire gilas d’in idonsa yana gogewa da handky d’in hannunsa, cikin sanyin nan nasa yace, “Amin afuwa Zan amsa tambaya uku ne kacal acikin wad’annan tambayoyin, dan akwai tambayar danake da burin amsata anan wadda wani bawan ALLAH ya turomin, to Alhmdllh yace shi ma’abocin zuwa wannan masallacinne, sannan kuma wannan zaman baya wucesa aduk wata, to tambayarsa tanada muhimmancin data shafemu muduka, shiyyasa naza6i amsata anan domin mu farka daga sakacinmu, sauran tambayoyi kuma insha ALLAH zamu tsara yanda za a amsasu koda daga bayane”.
         Take kowa ya aminta da batunsa, dan haka malam mustafa ya karanto tambayoyi uku kacal Aliyu yabada amsarsu daganan Yakoma kan Sak’on da Maimunatu ta sanarmasa d’azun da safe.
         Saida ya maida siririn farin gilas d’insa sannan yace, “Mai sak’on yana magana ne akan matsala dayake fuskanta gameda rayuwar aure tsakaninsa da iyalansa irinta rauni wajen biyamusu buk’ata a shimfid’a, amma dukda yasan da hakan yaje Yakuma k’ara aure batareda yatashi yafara Neman maganiba. Lallai wannan sakacine mai girma, sannan akwai cutarwa ga iyalanka, tayaya baka iya gamsar da mace d’ayaba sannan kakuma tarkato ta biyu? Sannan babu wani mataki Daka d’auka akan hakan kafin ka k’aro d’in?, tayaya muke tunanin Matsaloli bazasu k’aruba?, ayanzu dukanku nan dazance wanene *Jarumin Namiji?* saikucemin Wanda ya iya rik’e gidansa daci da sha dadai buk’atu nayau da kullum ko?”.
        Atake suka bashi amsa da eh.
      Aliyu yay murmushi yana gyara zamansa, batareda ya kallesuba yace, “To lallai wannan bazamu kirashi cikakken jarumi ba gaba d’aya, sai dai dolene mu yaba masa wajen sauke nauyin dake kansa na wani 6angaren hak’k’ok’in aure. Jarumin namiji shine mai k’ok’arin tsare dukkan wani hak’i na iyalansa, ci, sha, sutura, wajen zama, ya kula da addinin iyalinsa, yakula da zamantakewarta da makwafta da zumincinta ta 6angaren danginta da danginsa, ya nuna mata soyayyar dazata saka zuciyarta kwanciya waje d’aya batareda y’an wasan kwaikwayo da jaruman littafi na birgetaba, a wajen shimfid’a yazama Oga kwata-kwata yanda za’a ringa kiransa maigida cikeda tsantsar girmamawa, ba yana magana ana kauda Kai da murgud’a bakiba”.
      Dariya suka Sanya, yayinda shima Aliyu yake darawa da kare fuskarsa da hannu.
       “ALLAH kuwa karkiji wasa, duk k’ok’arin mace wajen iya girki, tsafta da kwalliya daduk wata kisisina inhar batada nagartar kar6ar mijinta a shinfid’a zakaga Mijin baya kallonta da daraja, kuma duk yawan son da yake mata saiya gudu kaga babu komai, saigaka tarasa kansa, takuma rasa ina matsalar takene?. To haka shima namiji duk k’ok’arinsa na karema mace hak’k’ok’inta inhar bashida jarumtar biya mata buk’ata to wlhy zata daina ganin darajarsa da shakkar fad’a masa duk maganar datazo bakinta, da yawan rainin da matayenmu ke mana tushensa shine ragwantakarmu a shinfid’a, kabari basir da sanyi sun gama cinyeka amma kullum idonka nakan y’ay’an mutane, da yarinya tawuce kashiga lasar la66a da had’iye yawu kana mata kallon da addini ya haramta maka, amma matarka dake gidama baka iya biya mata 6uk’ata yanda ya kamata. Akulum matayenmu sunada k’ok’arin gyaran Kansu a kanmu, dan a hasashe babu wanda yakai matanmu k’ok’arin shaye-shayen magungunan nan na k’arin Ni’ima, dukda suma matan ina k’alubalantarsu dan basabin matakan daya dace wajen shan maganin. A mashayinka namai gida daga lokacin da kukai shekaru biyu da aure da matarka yadace kafara neman gyara kanka, danfa kafara komawa cus malam. Kai kanka kazauna ka k’iyasta da watannin farko na amarcinku irin nanuk’ema amarya da kakeyimana, kai abindama yakamata namiji yayi daga shekarar dayasan zaiyi aure yadace yafara dagewa da amfani da maganin sanyi dana basir, dan sune manyan abinda kemana lahani, bakuma komai ke kawosuba sai abincin da mukeci, mutum a yini saiyaci maka abinci Kala kusan goma sha dukshi kad’ai, kuma zaka samesu duk maik’one, tayaya basir bazaiyi ram damuba?, kafara gyara kanka malam tunkan amarya tashigo daga ciki, yanda idan tashigo tajika zam, kanayin magana zatace hakane Alhaji koda bakada ko sisi kuwa”.
    Nanma dariya mutane keyi, samari damasu kunya nata sunkuy dakai, shima kansa malam Aliyun kansa a k’asa yake baya kallon kowa, dama malam bayanan yamayi tafiya.
        “Ina muku wannan maganarnefa akan gaskiya y’an uwana, domin wlhy sakacin gyara kayinmu yana bada gudunmawa wajen saka matayenmu a masifu Na mad’igo da zinace-zinace ko amfani dakansu wajen samun biyan buk’ata, wata badan kud’i take aikata wad’annan fasik’ancinba, saboda kawai mijinta baya iya gamsar da itane, mace tadage tasayi kayan gyaran kanta tasha babu ko sisisnka Alhaji, kuma dan kawai ta burgeka, buk’atar mijinta ta taso Mata amma dayazo bazai iya gamsar da ita yanda ya kamataba saiyaja gefe, tayaya muke tunanin bazata nemawa kanta mafitaba?, ga masifu da kafafen social network d’innan sukazo mana dasu iri-iri, matarka taje tashiga taganoma kanta masifar dazata dameta kai baka kusa da ita, koma kana kusa bazaka iya biya Mata buk’atartaba Yaya kake ganin za’a k’are? Wlhy inda zaka zama jarumi wajen bata kulawa da kare mata duk wani hak’k’inta a shimfid’a ko soyayyar da suke gani a finafinan banzarnan bazaiyi tasiri agaresuba, dan mace kota gani saitaga ai shirmece, wadda mijinta ke Mata tawuce wannan, tayaya ta film da hikayoyin marubuta zata birgeta balle har tadinga kokwanton anya akwai irin wannan soyayyar kuwa a duniya?. To tasaba Nata Mijin daga mazurai sai matsalar Neman kud’i yasani, wanima saiyakai k’arfe sha biyu a majalissar da ba’a komai saisurutan banza da wofi da nad’oma kai zunubi, lokacin dazai shigo gidan tajima dayin barci, saidai cikin barci taji yana Neman tausheta. Mufa mazan hausawa ko d’an soyayyarnan kafin biyan buk’atama ba iyawa mukaiba, kana zaune mace bazata ra6u da jikinkaba saikunzo kwanciya, data zauna kusa dakai kace batada kunya, wanima ko a wajen kwanciyar dayasamu biyan buk’atarsa to matar tana gabashin gado shikuma yana yammaci, burinka kawai ka kashe gobarar gabanka kakoma gefe. Haba tayaya mace zata yarda akwai soyayya a duniya inba ta film da littafiba? Addininmu babu abinda bai koya manaba, babu Wanda yakai MANZON ALLAH iya soyayya ga iyalansa, miyasa bazamuyi koyi dashiba domin samun farin ciki a gidajenmu, mudaina d’aukar matanmu bayinmu komasu kula mana da gida da yara kawai, ba haihuwa da raino da bautar cikin gida bane kawai aikin mace, baka bata ci dasha da sutura kawai bane yadace dakai, ka nuna Mata soyayya da kulawar dazata ringajin itad’in macece wadda ta isa hamshak’iya, babu birgewa a garemu ace da zarar mun aure mace tayi hauhuwa d’aya shikenan saimuce soyayya ta k’are, waya gaya maka soyayya takare malam? To komin tsufanku soyayya bata tsufa, soyayyar gaskiyama ana girmane tana Kara girma, tomu matsalarmu yawancinmu shawa’a ke kaimu ga aure ba soyayyaba, shiyyasa kwanaki naja matsalolin gidajen aurenmu Na k’ara girma da bunk’asa, amma kullum idanunmu nakan matan waje, kakasa gyara wadda ka ajiye tayaya wadda take a waje bazata birgekaba?. Dan ALLAH yakamata mu gyara, akwai abubuwa da yawa dasuke gyara namiji shima, ba Mata bane kawai keda wad’annan magungunan, akwai wad’anda idan kasha kaikanka zasu motsama jarumtarka ta yadda zaka gamsar da iyalinka, amma maganar gaskiya mu maida hankalinmu wajen Neman maganin basir dana sanyi a farko, insha ALLAHU namuku alk’awarin Baku wasu sirrika a zama nagaba dazai taimakeka wajen gamsar da iyalinka, abinda muka fad’a dai-dai ALLAH kabamu lada, Wanda mukayi kuskure ALLAH ka hafe mana baki d’aya……………….✍????



*_Dadai nace bazanyi posting ba, amma ganin nagama typing da wuri nace bara nayi muku kawai_*.





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button