A Jamhuriyar Congo Al’ummar Shasha Na Neman Fitsarin Ɗan Adam Ruwa A Jallo

Shasha, wani kauye ne dake cikin yankin Masisi, mai tazarar kilomita talatin kudu maso yammacin birnin Goma, babban birnin Kivu ta Arewa a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
Noma ya kasance daya daga cikin manyan ayyukan al’ummar yankin Shasha a nan, amma a fagage da dama kasar na kara samun raguwar noma.
Lamarin ya haifar da raguwar kayayyakin noma da ake nomawa a cikin gida, wanda ba zai iya biyan bukatun abinci na cikin gida ba, yayin da a baya kauyen ya kasance yana wadata manyan garuruwa kamar Goma da kayan masarufi.
Domin shawo kan wannan matsala, yawancin masu gonakin noma suna sayen fitsarin ɗan adam daga maƙwabta ko wasu mazauna ƙauyen, wanda suke yin amfani da shi a matsayin takin gargajiya.
Paul Kanyama, manomi ne kuma daya daga cikin wadanda suka fara amfani da (fitsarin dan Adam) a matsayin taki a garin Shasha.
“Muna farawa da sanya igiyoyin shuka a gonakinmu, sannan mu rika fesa fitsarin dan Adam, wanda bayan an yi wata daya yana da karfin kashe duk wani kwarin da zai iya afkawa shukar, daga nan kuma sai mu sanya iri a gonakinmu kafin a yi feshi a karo na biyu. Wannan hanya ce da ke aiki da kyau kuma albarkacin noman gonakinmu ya sake karuwa.” Kanyama ya shaida wa wakilinmu.
Lallai wannan wata mafita ce da mazauna garin suka ce tana aiki sosai da kuma kara yawan amfanin gona a wasu fannonin mazauna kauyen.
Yayin da a bangaren manoma, wannan al’ada tana kara habaka amfanin gonakinsu, ga sauran matasan Shasha, hanya ce ta samun kudi ta hanyar sayar da fitsari a gwangwani mai cin lita 20 a kan kudin kasar Kongo, Congolese francs 12,000, wato dalar Amurka 6.
Kahindo Lubuto Mwajuma, tana daya daga cikin matasan kauyen da suke sana’ar sayar da fitsari ga manoma.
“Wasu ‘yan kungiyar ACTION FOR THE DEFENSE OF HUMAN RIGHTS (ADPDH) ne suka wayar da kan mu da abokaina,” inji ta. “Sun nemi da mu samar musu da gwangwanin fitsari da za su yi amfani da su wajen takin gonakinsu a kan kudi Congolese francs 12,000, wannan wani abu ne da na jima ina yi kuma yanzu na yi shi a yau”
Biyo bayan bukatu mai karfi daga manoma wadanda saboda rashin samun takin zamani suke amfani da wannan hanyar, wannan fitsarin dan adam yana kara karanci kuma farashinsa na iya tashi nan da kwanaki masu zuwa.
Bangaren noma na DRC na daukar sama da kashi 60 cikin 100 na ma’aikata na Kongo kuma ya ƙunshi kashi 19.7 na GDP, a cewar hukumar ciniki ta ƙasa da ƙasa ITA.
Daga Jaridar alkiblah
[ad_2]