MIJIN MATACCIYA Page 1 to 10

~~~ *C* ikin dimuwa,damuwa da tashin hankali mai tsanani yasake damke hannayenta dake cikin nashi wani irin gumi na keto masa tamkar anyi masa b’arin ruwa aka, idanuwanshi jajur suke sannan kuma sun kankance mutuka,
Anata bangaren itama hakan take domin inbanda hawaye babu abinda take fitarwa, kwalla ce ke ta faman tsiyaya daga cikin kwayar idanuwanta,
“Wai wannan wanne irin shashanci ne haka….? Kai balarabe bazaka kyaleta ayi maza aje ayi mata aikin nan da za ayi mata ba?” Muryar wata yar dattijuwa ya karade wurin da suke, tamkar ansake fama masa wani Miki dake tare dashi haka yayi domin rikon da yayi mata yanzu har yaso yafi na dazu, cikin jarumta da dauriya gamida juriya irinta maza yayi mata wani basaraken murmushi mai tafiya da hankalin duk wata ya mace, cikin karfin hali da kokarinsa na hadiye kukan dake gab da balle masa ya saka kwayar idanuwanshi cikin nata sannan cikin sanyin muryarshi wadda ta hadu da yanayi na tashin hankali da yake cikin yace,
“Is ok my heart…..daina wannan kukan haka,insha Allah zaki shiga lafiya sannan zaki fito lafiya domin kullum addu’ar da nake yimiki kenan…. Allah yayi miki albarka yar aljannah insha Allah tare zaku fito da kyawawan twins dinmu masu kama dake…..”
Kawar da kanta tayi daga kallonshi tana zubar da hawaye,
“Kayya…..kayyah Rabin raina,bana jin zan sake rayuwa dakai acikin duniyar nan….nidai kawai ka yafe min,ka yafe min duk laifin da nayi maka a iya zaman mu sannan koda na mutu to ka sanyawa yaranmu sunan da kayi min alkawarin zaka sanya musu….ina tsananin sonka mijina….”
Bai kai ga buda baki ba yaga ta sake burkicewa ciwon haihuwa yadawo mata sabo fil fiyeda dazu babu bata lokaci ma’aikatan lafiya dake tare dasu sukayi azamar tura gadon da take kwance akai zuwa dakin da za ayi mata aiki wanda har lokacin yana rike da hannunta dukkaninsu suna hawaye amma sai dai shi nasa hawayen azuci yake yi ahaka aka shigar da ita cikin dakin shikuma dan dole yaja burki daga bakin kofa bawai dan yasoba.
Daga wajen da yake tsaye yagagara zama sai faman sintirin kaiwa da komowa yake yi yanata faman hade hannayensa wuri daya yana runtsewa gamida da runruntse idanuwa acikin zuciyarsa kuwa baida addu’ar da ta wuce,
“Ya Allah ka sauki Ramlat lafiya,ya Allah kafito min da abinda ke cikin cikinta lafiya……” Haka yaketa faman fada har tsawon mintuna talatin, Yakumbo mariya tayi tayi dashi akan ya nemi wuri ya zauna amma yakasa tamkar wani sabon soja haka ya dake yanata kaiwa da kawowa,zuwa can yajuya ya kalli wurin da yakumbo mariya ke zaune bayan ya duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunshi wanda ya nuna kimanin karfe 11:30 nadare,cikin sassarfa kamar kazar da kwai ya fashewa aciki yanufi wurin yakumbo mariya,cikin russunawa yace,
“Yakumbo bari naje nayi salla ina dawowa….”
“Ko kaifa,yawwa dan albarka, maza kaje kayi mata addu’a domin ita tafi bukata a wannan lokacin…”
Batare da yasake furta komai ba yajuya yatafi domin zuwa inda zaiyi sallar. Binsa da ido yakumbo mariya tayi tana girgiza kai domin tasan halinsa yawan magana ratataa baya cikin dabi’arshi da tsarinsa bare kuma yau da zuciyarshi ke cikin alhini da tashin hankali, wannan yaro dai ba asan adadin son da yake yiwa Ramlat ba sai shi sai ubangijinsa tunda shine yasan zuciyar kowa.
Tunda yayi alwala yashiga masallaci yake salla wadda yake jimawa cikin kowacce sujjada saida yayi salla raka’a hudu sannan yadaga hannu yayi addu’a bayan ya shafa ya mike a kasalance yana gyara kafar wandon jeans din dake jikinsa,haka kawai yaji ya nemi nutsuwa atare dashi yarasa gashi zuciyarshi tayi wani irin nauyi sai bugawa takeyi da karfi fat fat tamkar zata faso kirjinsa tafito,cikin mawuyacin hali da yanayi yafito daga masallacin yana dafe goshinsa wanda yadauki zafi haka siddan,jan kafarsa yarinka yi wacce tayi masa tsananin nauyi kamar jini irin ya taru dinnan sosai ahaka yanufi wurin da yabaro yakumbo mariya,
Hangota yayi atsaye da alama shi take jira dama cikin sauri ya karasa wurinta,
“Mu’azzam Ramlat ta haihu,anciro yara biyu mace da namiji amma macen bata zo da rai ba sai namijin kadai….”
“Suna ina yanzu yakumbo? Ina ita Ramlat din?”
“Muje ka gansu,Ramlat kuma ba afito da ita ba tukunna har sai nan da wani lokaci…”
Shuru yayi baice komai ba yabi bayanta zuwa inda tashiga,yara kam tubarkalla jajur dasu kamar shi sannan tun daga yanzu zaka gane tsananin kyawun da Allah yayi musu amma ita macen babu rai sai iya namijin kadai keta yan callare callaren kukanshi,
“Allah yasa haka shi yafi alkhairi, Allah ya raya mana namijin…..” Yakumbo ta fada tana karbar macen daga hannunshi,
“Amin Yakumbo….”
“Na kira su Zaid insha Allah nan bada jimawa ba zasu karaso….”
Jijjiga kai kawai yayi yafita bayan ya dauki namijin yaganshi. Tun bayan da aka gama yiwa Ramlat aiki har asubah bata farfado ba, karshen tashin hankali kowa dake wurin yashiga musamman ma shi uban gayyar dan dakyar ya iya zuwa yayi sallar asubah yana sallamewa ya fito yadawo wurinsu amma tun daga nesa ya fahimci kamar akwai matsala domin yanda ya hango mutane na rusar kuka sannan wasu sunyi cincirindo sun rufe gadon da Ramlat ke kai,jin kansa kawai yayi yana faman juya masa kamar fanka nan yazube ya fadi awurin,kinkimarsa akayi zuwa emergency domin bashi agajin gaggawa.
Tunda aka kwantar dashi ake faman yimasa karin ruwa wanda ake gaurayawa da wasu allurai aciki,bai tashi bude idonshi ba sai misalin karfe 5 na yamma, Cikin zafin ciwon da yake ciki ya yunkura yatashi duk da jikinsa babu wani sauran karfi,
Zaid ne yanufoshi cikin sauri yana fadin,
“Sannu yaya Khalil….tsaya jikinka babu karfi”
Kallonsa yayi da raunannun idanuwanshi sannan cikin sanyin murya yace,
“Zaid muje gida….kaini inga Ramlat…”
Zaid zaiyi magana suka hada idanuwa yasan babu abinda yayan nasa ya tsana irin gardama, lallabawa sukayi suka nufi gida wato family house dinsu tare da sauran yan uwa wadanda ke tare dasu,
Iske gidan sukayi cike dam da mutane babu masakar tsinke anata karbar gaisuwa,shi dai yasan tafiya kawai yake yi amma bazaice ga inda yake zuwa ba kai daga karshe ma gani yayi ganinshi ya dauke gaba daya saboda yagama tabbatar da cewa Ramlat ta rasu,dakin Zaid aka kaishi can aka cigaba dayi masa kare karen ruwa kowa shi yake tausayawa ganin halin da yashiga domin har yafi iyayen Ramlat din shiga rudu da dimuwa,duk wanda yazo gaisuwa idan najikine sai yashiga ya dubashi shi baima san inda yakeba.
Bayan kwana uku da rasuwar Ramlat ya farfado yasamu kansa hankalinsa yadawo gareshi tun da yabude ido kuma yake kuka kamar wani karamin yaro,kowa shi yake bawa hakuri amma angagara gane kansa, hajiya Raihan mahaifiyar Ramlat tare da Alhaji Tamim maihaifin Ramlat shiga wurinsa sukayi suna bashi baki tare da yimasa nasiha amma duk abanza,daga karshe yayan mahaifiyarsa wanda suke kira da Abban London shine yashiga wurinshi ya zauna gefensa cikin nasiha yace,
“Ibrahim kayi hakuri ka rungumi k’addara domin kowa da kagani na haka ne,kayiwa Ramlat addu’ar samun rahamar ubangiji sannan kayi hakuri domin duk abinda Allah yayi akan bayinsa to shine daidai….ba aja da hukuncin ubangiji,idan kaci gaba da irin haka to Allah zai iya yin fushi dakai domin baka karbi k’addara ba ko kamanta Allah yakan jarrabemu da rayuka? Yau ina mahaifinka? Ni ina nawa mahaifan? Mahaifinka ma ya mutu kuma kayi hakuri to meyasa yanzu zaka gaza? Dan Allah kadaina duk wadannan abubuwan ka daure kayita addu’a insha Allah zaka samu madadinta koma wacce tafita…..”