NOVELSSANADIN LABARINA HAUSA NOVEL

SANADIN LABARINA CHAPTER 1

Sanadin
              Labarina
                   Free Page (1)

©®Hafsat Rano

****Gudu take a cikin ruwan da ake tsugawa kamar da bakin kwarya, kokari take ta kai gidan kafin duhun magriba ya sakko, duk da shekarun ta ba zasu wuce sha hudu zuwa sha biyar ba, amma haka ake aikenta har gaba da  in da taje a yanzu,ba yau ne karo na farko da ruwa ya fara tare ta ya zane ba, ba kuma shine zai zama na karshe ba, duk da haka har yau ta kasa sabawa da dukan ruwan, duk sanda ya tabata toh fa sai ta kwanta rashin lafiya amma hakan ba zai hana idan wani hadarin ya sake hadowa a sake aiken nata ba. Daidai wajen wani shago tazo wasu manyan mutane da suka fake a wajen suka ce tazo ta fake, kallon su tayi kawai ta cigaba da gudu a cikin ruwan dan idan har ta yarda ta fake din toh bayan dukan ruwan za’a kara mata ne da dukan gaske, shiyasa ta gwammace ruwan ya dake ta akan dukan Iya Lami wanda a duk sanda ta dake ta sai ta sha matukar wahala, bayanta duk shatin dukan ta ne da kafafun ta, shiyasa take matukar tsoron abinda zai hado su da ita.
   Tana cikin gudun takalmin ta ya tsinke, ta durkusa ta cire su dukka ta rike a hannu ta cigaba da falfala gudu. A zauren gidan nasu ta tarar da iya Lami tana hura wuta, wani kallo tayi mata wanda ya saka hantar cikin ta kadawa, tayi saurin cewa

“Wallahi ita ta tsaida ni, sai da aka samo chanji kafin nan kuma har an fara ruwa.”

Ta fada tana rawar sanyi hakoranta na hadewa waje guda.

“Bani.” Tace tana mikowa hannu, hannun na rawa ta mika mata ta warta tana hararar ta

“Shegiya me zubin mayu, wuce kije ki cire kayan nan kizo nan,kin tsare ni da shegun idanuwan ki kamar na kura.”

Da sauri ta shige ciki tabi gefe ta shiga dakin ta, ta cire kayan ta shanya su akan kofar langa-langar dake dakin sannan ta saka wasu, har cikin kashin ta take jin wani irin masifaffen sanyi, amma haka ta sake fitowa ta koma zauren, ta samu gefe ta durkusa ta hau tankad’e, tana yi tana gyara wuta, ta gama ta rud’a sannan ta koma gefe ta hade kanta da guiwarta zazzabi na neman rufeta.
   Ji tayi an duma mata dundu, ta dago da sauri tana kallon Iya Lami akanta

“Dan ubanki shine zaki yi min talgi ruwa ruwa, ki hade kai da guiwa kina ji har ya soma zubewa dan rashin mutunci kiyi kamar baki sani ba?.”

Da sauri ta kalli wajen tukunyar, ta mike da sauri ta hau gyarawa tana rage wutar baya, kwafa tayi ta sake ficewa lokacin ruwan ya tsagaita sai dan yayyafi da ake yi, a gaban wutar ta zauna dirshan har ta gama tuwon ta kwashe, ta maida ruwa akan tukunyar da zata gasawa baffanta kafarsa.
   Tana zaune ruwan yayi ta kwashe kwanukan tuwon ta shigar dasu dakin iya Lamin sannan ta samo baho ta juye ruwan ta dauka ta shiga dakin Baffan da sallamar ta, yana kwance akan yar katifar sa, ransa babu dadi tunda aka fara ruwan yake ta tunanin ta, ganin ta yanzu ya sakashi sauke ajiyar zuciya

“Bongel…”

“Na’am Baffa “

“Kin dawo ashe, ruwa ya taba ki ko?”

Girgiza kai tayi

“A ah yayyafi ne kawai.”

“Alhamdulillah, ina ta tunanin ki tunda naga an soma ruwan nan, kiyi hakuri kinji?”

Shiru tayi kawai, ta jawo tsumman da take gasa masa kafar ta soma danna masa kamar yadda iliya ya koya mata. Ta gama ta fitar da ruwan sannan ta dawo ta zauna a gefen sa, cikin tsananin tausayinsa, tun bayan da akayi masa aiki a kafar ya zamana duk damuna kafar na tashi har ta hanashi takawa kwata-kwata, ita take kula da fiye da rabin dawainiyar sa Iya Lami babu abinda take sai yi masa fada da masifa kullum ita ta gaji da dawainiya dashi da yar sa, baya tanka mata dan yana tsoron tace zata tafi, abubuwan zasuyi musu yawa shi da yar sa, shiyasa yake lallabawa baya taba mata musu ko yayi jayayya da ita.
   Shigowa tayi dakin dauke da kwanukan tuwo da miya, da sauri ta tashi ta karbe ta, ta ajiye a gefen baffan sannan ta raba ta fice daga dakin, ta nufi dakin ta, ta kwanta akan tsohuwar katifar ta, ta lulluba da wani zanin mahaifiyarta, duk da haka bata daina jin sanyin ba, amma babu yadda ta iya, haka ta cigaba da rawar sanyin har dare ya soma yi sosai, kafin ta samu bacci me nauyi ya dauke ta.
     Da safe ta tashi da ciwon kai, duk da haka sai da tayi duk ayyuka kanta, ta koma dakin bayan ta gama ta kwanta kenan Iya Lami ta leko tace ta tashi, tazo ta debo ruwa, ba musu ta saka wani tsohon Hijab dinta, ta fito ta dauki bokitin ta fita. Dakin da baffan yake ciki Iya Lami ta leka, ya kalle ta yace

“Lami nace a daina saka yarinyar nan dibar ruwa dan Allah.”

“Idan bata debo ruwa ba kai ne zaka debo? Eh?”

Shiru yayi ganin ta harzuko masa

“Da me zan ji? Da wahalar ka ko tata? Ko ni kake so na debo ruwan da kaina ne!?” Ta cigaba da fadan tana fita tsakar gidan

Be amsa mata ba, ta dinga sababi har sai da yaji dana sanin yin magana, haka yana ji yana gani sai da ta cika gidan tas sannan Lamin ta kyale ta, ta sake komawa dakin ta kuma kwanciya kanta na sake matsa mata sosai, ga wata mura da tazo ta chunkushe mata hanci da makoshin ta.
Har wajen azahar Jiddan na kwance bata fito ba, tasan dukan ruwan ne ya sakata zazzabi amma tayi biris kamar bata sani ba,ta cigaba da sabgar ta bata damu da halin da zata shiga ba, ko dubo ta batayi ba har sai da Saude ta shigo dauke da kanin ta Muhusin a kafardar ta, ta gaida Iya Lamin sannan tace

“Inna ce dama tace muzo muji ko lafiya Jidda bata leko yau ba?”

“Jeki dakin ta ki dubo.”

Tace tana yin gaba ta cigaba da sabgarta, dakin ta shiga ta sameta a kanannade ta chure waje daya, ta lulluba da tsuman zanin ta.

“Jidda, jidda?” Tace tana janye rufar.

“Sanyi nake ji Saude, rufe ni.”

Maida mata rufar tayi, ta zaunar da Muhsin a gefenta sannan ta fita, taje ta sanarwa da Babar tasu sai gasu sun dawo tare, a zaure Iya Lami ta tsaida su.

“Lafiya Asabe?”

“Lafiya lou, Jidda nazo dubawa Saude tace min tana kwance bata da lafiya.”

“Me zaki mata toh? Ko tsabar kinibibin da kika saba ne, salon a cigaba da zagi na a gari ace bana kula da ita.”

“Kina kula da ita din ne? Kiji tsoron Allah wallahi Lami, Allah kuma sai ya tambaye ki wallahi,

“Abinda naga dama shi zanyi a cikin gidan nan, kamar yadda babu shegn da ya saka miki ido akan gidanki haka nima babu shegen da zai zo min da iyayin banza da wofi.”

“Kinsan mutumin da be haihu ba, ba lallai yasan daraja da zafin d’a ba,kuma dole naje naga halin da yarinyar mutane take ciki dan ke bakar azzaluma ce baki san rayuwa ba.”

Magaanar tayi mugun yi mata zafi, tayi kokarin warto rigarta da nufin su daku amma ta goce tayi shigewarta dakin da Jiddan ke ciki, ta taimaka mata ta mike tsaye, ta riketa suka fito, bayan su ta biyo tana huci kamar zakanya tana zage-zage amma tayi mata banza sai da suke fice daga gidan.
Gidan ta, ta kaita ta dora ruwa ta sakata tayi wanka, ta bata kayan Saude ta saka sannan ta bata abinci da paracetamol ta sha, ta kwanta lamo abin tausayi, duk wanda ya rasa uwa yayi kuka dan tabbas yayi babban rashi a rayuwa.
Yamma likis zazzabin ya sake rufe ta, ta saka aka samo machine a chan hayi yazo ya dauke su tare, ya kai su chemist din cikin garin,akayi mata allura aka bata magunguna sannan suka dawo, ko da suka dawo bata barta ta koma ba,tace tayi kwanciyar ta anan har sai ta samu sauki, ta aika Saude ta fada wa baffan zata kwana a gidan su, yayi godiya dan hakan yafi masa sauki kuma hankalin sa yafi kwanciya.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button