SANADIN LABARINA CHAPTER 3
“Tana bayan gida.”
Dagowa yayi jin abinda ta fada, sai a lokacin ya ganta, fuskarta fiki fiki, yar firit kamar ka hureta ta fadi saboda rama, mamaki ya kamashi ganin ta
“Wacece ke?”
Yace yana kafe ta da ido, sosai ta duburburce ganin yadda ya kafe ta da ido, idanun sa manya sosai masu ban tsoro
“Na’am?”
Tace cikin hada kalmonin
“Who are you? Daga ina kika zo?”
Ya sake tambayar ta har lokacin kallon ta yake,be taba ganin ramammiya karmashashiyar yarinya irin ta ba, shi ya zata ma aljana ce, saboda tsabar rama har wani rami ne a fuskarta ya shiga ciki. Bata san amsar da zata bashi ba, sai kawai tayi shiru tana wasa da hannun ta. Anty ce ta fito a daidai lokacin
“A ah, Yaya boss yaushe ka shigo?”
“Ban dade ba, ina kwana?”
Yace yana dauke kansa dga kallon yarinyar
“Lafiya lou, baku tafi ba ashe.”
“Eh Baba be gama shiryawa ba, shine nace bari na shigo mu gaisa,wacece wannan Anty?”
“Auw wai Jidda? Jiya na taho da ita yata ce, yar wana ce amma ta dawo hannu na da zama.”
“Ok.” Kawai yace yana tabe bakin sa, sai ya mike
“Nima gobe zan koma in sha Allah, zan dade wannan karon har sai na kammala sannan zan dawo.”
“Wai, Masha Allah, zamuyi kewa. Allah ya bada saa da nasarar abinda aka je nema.”
“In sha Allah Amin.”
Yace yana ficewa, d’aga murya tayi tace masa a dawo lafiya ya amsa daga chan ya karasa ficewa.
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK
4 BOOKS 4500
3 BOOKS : 3500
2 BOOKS : 2500
1 BOOK: 1500
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107