NOVELSSANADIN LABARINA HAUSA NOVEL

SANADIN LABARINA CHAPTER 4

Sanadin

               Labarina

                     Free Page (4)

©®Hafsat Rano

** Tariq ne yake tuka motar Fauwaz na gefen sa,Baba a baya yana duba labarai a wayar sa jefi jefi suna hira da Fauwaz wanda shima rabin hankalin sa yana kan wayar sa yana duba wani pdf. Be fi sau biyu Tariq ya saka musu baki a hirar da suke ba har suka isa garin su Baban in da zasu dauko Hajiya Yaya
A kasan wata bishiya yayi faking kannen Baban dake zazzaune suna shan inuwa suka mike dukka suka yo wajen motar. Fauwaz ne ya bude ma Baba kofa ya matsa baya ya fito, ya shiga mika musu hannu suna gaisawa, kananan kuma suka russuna suna gaishe shi.

Cikin gidan suka dunguma suka shiga gaba daya, zuwa tsohon shashen Yayan kafin ta koma birni tun daga zuwa wani asibiti da tayi Baban yace tazo kenan, bata son birni sam amma babu yadda ta iya haka dai ta hakura bayan ya samu wasu daga cikin yan uwanta sun saka baki, duk da haka bata son zaman ta a cikin gidan sa dan ba wani shiri suke da Mama ba, ita Yaya dama bakin ta baya shiru bata gani bata tanka ba shiyasa tasu sam bata zo daya da Maman ba, tace Maman ta fiya isa da izza dan iyayenta wasu ne, shiyasa da Baba yazo mata da maganar auren Halima ta bada goyon baya dari bisa dari dan a ganin ta a lokacin ne zai auri daidai dashi.
Hayaniyar Yayan suka fara ji tana ta fada da sababi, muryar ta a sama sosai ta dage tana fada bilhakki da gaskiya, murmushi Baba yayi, ya girgiza kansa yayi sallama a tsakar gidan, muryar sa ta sakata yin shiru ta amsa sallamar tana jefar da sandar da yake hannun ta. Fuskar Tariq a hade dan shi ba kasafai ya fiya son hayaniya da shiga cikin mutane ba duk da Baba yana tirsasa masa shiga cikin yan uwan sa dan suna da matukar yawa, yanayin sa ne a hakan kamar Safiyya, su suko yo Mama dan itama bata cika son mutane ba sai wanda tayi mugun sabo dashi.
Shima kamar Maman ba shiri suke da Yayah ba, dan kullum yi masa korafi take bashi da sakin fuska, surutun ta shi yafi komai damun sa, dan idan ta fara magana baya jin ko hadiyar yawu tana yi. Fauwaz ne dan dakin ta da Amira, sune suka yo ta a surutu da kwashe kwashen mutane kowa nasu ne.
Tabarma ta dauko zata shinfida musu fauwaz ya karba ya tayata, ta zauna a gefen gadon ta suka gaisa da Baban sannan su Fauwaz din suka gaishe ta ta amsa tana ficewa taje ta kawo musu ruwa ta ajiye sannan tace

“Ashe zaku zo, na dauka fa sai wani satin wallahi, ban gama abubuwan da nake anan din ba.”

“Menene baki gama ba Yaya?”

“Em.. em akwai wani biki na yar Hajara nan kasa damu, babu dadi ace ban tsaya an yi bikin dani ba.”

“Ayya, sai a basu hakuri Yaya, kinga fa lokacin komawar ki wajen likita yayi har yana neman wucewa.”

“A ah gaskia ba zaa basu hakuri ba, sai dai a bani gudunmawa me tsoka na bata, sai kuma ka aiko matar ka itama tazo ranar bikin da gudunmawar ta.”

Tace tana yin kicin-kicin da fuska, murmushi Baba yayi yace

“An gama Yaya, sai kuma me?”

“Shikenan, sai mu tafi tun da kayi niyya, ni wallahi dan ba yadda zan ne, a kai mutum a ajiye shi waje daya haba!”

“Kiyi hakuri Yaya.”

“Idan ban hakuri ba ya zanyi toh? Fatan dayafi karfin ka ai sai ka mayar dashi wasa.”

Har Kawu Rabi'u ya kawo madara da kwan zabin da ya tafi karbo wa Baba bata daina sababi ba, magaanar ta kadai kake ji a dakin sai dai Baba yayi murmushi lokaci zuwa lokaci ya amsa mata, shi kam Tariq ji yake kamar ya fice amma yasan idan yayi haka zai gamu da fishin Baba, shiyasa ya hakura ya zauna kawai yana sauraron surutun ta wanda baki daya babu magaanar da za'a kama.

   Fita Baba yayi yace zai je waje ya zauna da yan uwan sa kafin Yayan ta gama shiryawa, yana fita Tariq da ya tabbatar ya kule yaja tsaki yana dafe kansa.

“Uwarka kake wa tsaki bani ba.”

Tace tana hararar sa, kallon ta yayi idanun sa na yin kasa sosai yace

“Ni ba dake nake ba.”

“Ko ma da wa kake, mutum sai kuncin tsiya ba yar fara’a haba.”.

“Yaya Ya Tariq fa shine angon ki, ki dinga lallabashi.”

Fauwaz yace yana kokarin sake rura wutar fadan, buga cinyar ta, tayi tana daga murya

“Allah ya kiyashe ni da aikin dana sani, na auri mutum irin wannan ai na kade har ganye na, matar sa ta shiga uku wallahi.”

“Idan kun gama ni ina waje.”

Yace yana mikewa, ta rakashi da Allah raka taki gona ya fice kawai ya bar Fauwaz yana kyalkyala dariya, da gaske dariya suke bashi musamman Tariq da ya kasa gane wasan Yayan irin wanda ake yi na tsakanin jika da kaka, da gaske yake daukar komai duk da ba kasafai ya fiya nuna fushin sa ba amma zaka ga sam baya sakewa da ire-iren wasannin.
   Shi ya taimaka mata ta karasa hada kayan ta sannan ya daukar mata jakar, suka fito ta dinga shiga waje-waje tana musu sallama tun yana bin ta har ya gaji yace yana mota. A kwance ya samu Tariq din ya kwantr da kujerar side din me zaman banza fuskarsa rufe da hular da ya saka, booth ya bude ya saka kayan Yayan sannan ya dawo ta side dinsa yayi masa magana, mikewa yayi ya fita ya bashi wajen ya koma mazaunin driver.

“Har yanzu ka kasa gane wace Yaya.”

“Haka aka ce maka?”

“Ai naga kamar abun yana damunka, banda yawan maganar ta she’s very nice and fun to be with, zatayi ta saka dariya ne.”

“Ni kuma sai aka ce maka dariya nake so nayi ko? Bani da aikin yi sai dariya ko?”

“Ba haka nake nufi ba, yawwa gata nan ma ta fito, case closed.”

Yace ya ja bakin sa yayi shiru.

“Ni zan bude kofar da kai ne kenan?”

“Afwan Hajiya Yaya, wane mutum ya bar sarauniya da bude kofa?”

Ya bude mata da sauri ya taimaka mata ta shiga, sannan ya rufe mata kofar.

“Ranki ya dade.” Yace yana dariya

“Kafi oo sau dubu, Allah dai ya baka mata ta gari me hankali da sanin ya kamata kamar kai.”

“Amin.”

Yace yana cigaba da dariya, Baba ne yazo ya shiga motar kusa da Yaya, sannan suka sake sallama dasu Kawu Rabi’u, Tariq yaja motar suka fita daga kauyen.

Gudu ya soma yi sosai bayan sun hau babban titi, salati Yaya ta fara yi tana salallami.

“Tariq, rage speed din nan.” Baba yace yana kokarin kwantar mata da hankali

“Anya kalou yaran nan yake? Ba zaa kaishi ayi masa rukiya ba kuwa?”

Tace bayan ya rage tafiyar sosai, ta cikin rear mirror ya kalle ta, ya maida kansa gaba ya cigaba da tukin sa yana jin Baba da Fauwaz suna dariya

“Ba abin dariya bane wallahi, dole ma a nemo Malam Na Allah yayi masa rukiya gaskia.”

Yana jin su yayi musu shiru tukin sa kawai yake yana fatan su isa lafiya ya tattara ya bar garin gobe dan yasan tunda ta dawo ba zata kyale shi ba sam.
   Har suka isa gida magana daya take, aikuwa yana gama parking yayi saurin fita ya dauki kayanta a booth yayi cikin gidan da sauri. Anty ce a bangaren Yayan tana karasa gyara mata sashen, ya dire jakar yana jan siririn tsaki.

“Ya akayi?” Tace masa cike da kulawa

“Kai na ke ciwo.”

“Kaje akwai panadol a kan fridge ka dauka ka sha, sannu.”

“Ok.” Yace yayi saurin barin wajen dan baya so suzo su tadda shi, part din Antyn ya shiga, babu kowa a falon ya dauki paracetamol din ya nufi kitchen zai dau ruwa marar sanyi dan shi a rayuwar sa baya shan ruwan sanyi sai idan ana tsananin zafi.
    Tana tsaye a jikin drawer din kitchen din tana gyaran kayan miya, kafarta ya kalla a ganta kamar kara, ya dauki ganin sa zuwa wuyanta da yayi masa kama da murkin lema, mamaki ya sake kamashi ganin tana aikin cike da kuzari, a yadda take da ramar nan be yi tunanin ko numfashi tana yin sa daidai ba, gani yake kamar ko kwakkwaran motsi tayi zata iya karyewa. Gyaran murya yayi ta juyo a tsorace, ya dauke ganin sa daga kanta ya dauki ruwan ya fice.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button