Labarai

Sanyi!!Yin wanka kullum na iya janyo cutuka ga fatar dan Adam, Sabon bincike

Idan ka kasance kana wanka a ko wacce rana, kana yi wa fatarka illa ne maimakon inganta ta. Wani sabon bincike ya bayyana cewa yin wanka a ko wacce rana yana da matsala ga fatar dan Adam, Essence.com ta ruwaito.

Mu na yawaita yin wanka a kasar nan,” cewar wani likitan fata na Boston, Dr Ranella Hirsch.

Yana da muhimmanci ka samu fahimta. Yawancinmu dalilin da yasa mu ke yi shi ne saboda mun tashi mun ga kowa yana yi.

Gaskiya ne, iyayenmu, abokai da kuma kafafen sada zumuntar zamani sun gwada mana muhimmanci aski, shafa mai, wanka da kuma wanke kai tare da kasancewa cikin kamshi mai dadi.

Amma maganar gaskiya iya ce yin wanka a ko wacce rana yana busar da fata tare da cire wasu mayuka na musamman da ke jikin mutum.

Likitocin fata su na cewa iya yawan yadda kake wanka, musamman da ruwan zafi, iya yawan bushewar da za ka yi tare da cutar da fatarka.

Wanka yana dakyau wurin wanke kwayoyin cuta wanda ke taimakon fata sannan zai iya janyo kananun tsaga a fatar mutum wacce ka iya janyo cutukan fata.

Eh! Me kenan mutum ze yi don ya juyar da wannan illar? Likitocin fata sun bukaci mutum ya daidaita wankansa zuwa na mintoci goma a cikin kwana biyu zuwa uku da ruwan dumi.

Yanzu sau nawa za ka dinga wanka? Shin za ka sauya tsarin wankanka nan gaba?

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button