BAKAR WASIKA 6

Page -6️⃣
Bakincikin mutuwa, da damuwar rasa rai, wani irin bakinciki ne da yake ma kansa muhalli a zuciyar bawa, baki yayi kadan ya bayyana yadda zuciyata take ji, haka zuciya ma ba zata iya daukar abun ita kadai ba har sai da taimakon idanuwa da gangan jiki.
Taya Aminatu zata fadawa kowa yadda take ji? Taya zata rasa yayyu biyar maza kuma ta kasa kuka? Taya za a maida garinsu da gidansu kamar kufai kuma ta kasa kuka? Taya za a keta haddi mahaifiyarta a gaban idonta kuma ta kasa kuka?
A tsakanin rasa yan’uwanta da kone musu abinci da keta haddin mahaifiyarta bata san wani yafi wani zafi ba. Anya zata iya dauka?
“Duk ni kadai?”
Ta furta wasu hawaye mazu zafi na sauko mata, kana ganin yanayinta da kuma jin kalaminta kasan bata cikin hayyacinta, ruwan hawayen dake mata zuba har ya canja launin fatar idonta, ya kumbura mata ido, kwayar idon kuma ta mata ja sosai.
“Auta dan Allah ki yi hakuri, haba kowa ba yana da tabon mutane nan a garin nan”
Anty Aina’u matar Bashiru ta fada tana kai hannu ta dafa ta. Aminatu ta kalleta kamar tace mata shiga zuciyata ki gani, sai kuma ta dauke kai ta hadeye yawu.
Har aka yi gaisuwar kwana uku aka watse Amintu bata daina kuka ba, kukan da ta sha ko Inna bata yi ba, domin Inna ta bar komai a zuciyarta ne, idan ta yunkurin kukan ma baya zuwa mata, sai dai bata iya komai ko bandaki zata zagaya sai an rikata. Idan kuma ta zauna ta sanda kai kasa bata iya dagowa sai an rika kan nata an dago da ita. Kana ganinta ka san kukan zuci take wanda ya fi na ido illa.
Washe garin Ranar da aka watse Aminatu na tsakar gida tana wanke wanken kayan abincinsu, sai kawai ta fashe da kuka, rayuwarsu take tunawa kwana hudu zuwa biyar da ya wuce, a da idan tai wanke wanke kowa zubawa ake, amman yanzu daga ita sai Isah da Inna da Baba kawai suke ci, ba kamar da ba. Tunawa da tai da maganganun da mutane suke mata cewar ta yi hakuri ko dan ta karfafawa mahaifiyarta guiwa yasa tai saurin share hawayen. Ta cigaba da wanke wanke bayan ta gama ta dauki kayan ta kai a inda suka saba ajewa ta aje. Sannan ta fara sharar gidan, tana yi tana ta ganin inda aka aje gawarwakin yan’uwanta, ta kasa daina ganin abun a idonta.
Bayan ta gama sharar ta dauko tabarma ta shimfida daga bakin kofar sannan ta shiga ciki ta riko Inna dake kwance.
“Inna muje waje ki sha iska”
Daman zaman dakin ya fara isarta, sai ta yunkura, Aminatu ta taimaka mata ta mike tsaye tana takawa a hankali har suka fito, Aninatu ta zaunar da ita a hankali, sannan ta koma ciki ta dauko filo ta jingina mata a jikin ginin na kasa, ta jinginata. Take Inna ta sauke wata irin sanyayyiyar ajiyar.
“Allah ya miki albarka”
“Amin”
Aminatu ta amsa hawaye na sauko mata ganin yadda rayuwata ta sauya mata ita da mahaifiyarta a lokaci daya. Inna ta sakar mata murmushi sannan ta soke kai kasa. Madafa Aminatu ta nufa ta kunna wuta ta dora tukunya ta zuba ruwa. Sannan ta koma ta auko shimkafar da yayanta Bashiru ya siyo musu ta fara tsinta.
“Ji dan Allah ko tsintar shimfar bata iya ba…”
Ta lumshe ido da sauri tunawa da yayanta Sunasi da tai, yana yawan tsokanarta komai take sai yace bata iya ba. A hankali ta daga kai tana kallon ginin da yai domin yana daf da aure shi da Isah. Duk yadda ta so ta tana kanta hawaye sai ta kasa, hannunta ta saka ta share hawayen tana jin kamar wani nauyi a zuciyarta.
“Ashe haka ake ji idan aka rasa rai”
Ta furta a hankali tana kokarin tsayar da kukanta, sai kuma tai murmushi da yafi kuka ciwo.
“Mutuwa bakin takobi mai raba uwa da daya, ta raba yan’uwa ta raba mata da miji, kin maida mana gida kamar kufai”
Ta damki shimkafar a hannunta wasu hawayen na sauko mata kamar ba gobe, a dole ta aje gyaran shimfara saboda hawaye ya hana ta ga komai.
“Auta…”
Ta juyo da sauri jin kamar muryar Inna ta kirata, sai dai ganin kanta a noce ya tabbarta mata ba kiranta tai ba, muryar dai ce take jin kamar ta Inna. A take ta fashe da kuka ta bar gaban murhun ta mike tsaye wanda hakan yai sanadiyar barewar shimkafar da ke jikinta ta nufo inda ta gudu ta fada jikinta tana kuka. Sai Inna tai saurin lumshe idonta da sauri tana jin kukan Aminatu har cikin ranta, tana son tace mata yi hakuri amman bakinta ya mata nauyin da take jin kamar maganarta ta kare a duniya, sai kawai ta daga hannunta ta dora a jikin Amimatu tana shafata alamar rarrashi.
“Miyasa wani zai ji bakinciki da farinciki mu? A kauye muke zaune amman muna jindadi rayuwarmu, miyasa za su ruguza farincikinmu? Na kasa saba da rashin Yaya Sanusi Inna, Inna yanzu waye zai sake tsokanata? Yaya Amadu mai min fada baya nan, yaya musu mai bamu abinci baya nan, sun kashe Yaya Rilwanu da Yaya Iro…”
Inna ta bude idonta ta saka hannu ta kama fuskar Aminatu.
“Zan tafi na barki Aminatu, yar Autana, ina son ki saba da hakuri, akwai kalubale a gaba, mace da ta tashi a cikin gata da soyayyar uwa da uba da yan’uwa irin ki, duniya ta sauya mata lokaci daya? Dole zata ji ba dadi kuma zata fuskanci kalubale, amman zan fada miki wani abu, ina son ki rike ki rika maimaitawa, a duk lokacin da kika tsinci kanki a damuwa ko kika ga wani abun tashin hankali bakinki ya saba da furta Innalillahi Wa’inna Ilaihirraji’un, ri rike wannan kin ji”
Aminatu ta kalli Mahaifiyarta hawaye na sauko mata.
“Inna idan kika mutu kuma zai ki yi tsammani ni zan rayu? Wannan wace irin magana ce?”
“Zaki rayu Autarta, dan na mutu ba shi yake nufi ki mutu ba, Allah be raya wani dan wani, kuma be kashe wani dan wani, da ya bar yayana dan ni, ko kuma ya bar su dan ke, yadda ya so haka yake”
“Inna maganar da kika fada min yanzu, ta fi min ciwo fiye da rasa rayuwar yan’uwana, kada Allah ya nuna min ranar da zaki tafi ki bar ni, sai dai ni na tafi na barki”
Ta fada cikin kuka sannan ta rumgumeta. Inna ta sake runtse ido tana jin wani kololon bakinciki yana mata yawo a zuciya. Suna haka Baba ya shigo rike da yar ledarsa ta dawo (Fura) ganinsa yasa Aminatu ta tsagaita kukanta ta daga jikin Inna tana fyace hancinta.
“Kukan dai ne be kare ba”
Ya fada yana zaunawa kusa da Inna kana ya aje mata ledar furar.
“Ga fura Auta ta dama miki na san ba iya cin wani abua kike ba”
Kallon furar kawai tai ta dauke ido.
“Baba sannu da zuwa”
Aminatu ta fada da muryarta ta kuka, wai Baba yai mata murmushi irin na su na manya domin shi kansa juriya kawai yake irin ta maza amman ya ji zafin mutuwar yayansa, da kuma keta haddi matarsa. Hannu biyu Aminatu ta saka ta dauki ledar furar ta nufi gurin da suke aje ruwa ta dauko kwanon ruwa ta zuba furar ta fara damawa da nono. Daga Inna har Baba kallonta suke, ta ba su baya amman hakan be hana ta jin abunda suke tattaunawa.
“Ko ya rayuwa zata kasancewa Aminatu idan bana raye?”
Baba ya kalleshi da sauri jikinsa yayi mugun sanyi, Aminatu kuma ta juyo ta kalli Inna hawaye na bin fuskarta.
“Rayuwa zata kasance mai wahala Inna, zan zama marar gata marar yanci, dan farinciki da yai saura a rayuwata zai tafi ya bar ni, iskar da zan shaka ma sai na yi kamar na mutu sannan na same ta, Baba dan Allah ka yi mata magana ta daina irin wannan maganar”
Ta karasa tana duban mahaifinta, Baba ya kasa cewa komai domin jikinsa yayi sanyi sosai idonsa har sun cika da hawaye, Inna ta kalleshi tana murmushi ita ma hawayen ne a idonta.