NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 55 & 56

*_NO. 55 & 46_*

…………A gajiye ta shigo cikin Barrack ɗin, dan jan motar take tamkar wata ƴar koyo, tai horn ɗaya daga sojojin dake tsaron gidan nasu ya buɗe mata gate ta shiga, tunda tai fakin idonta ya
sauka akan motocin Amaan, hakan ya tabbatar mata ya dawo gidan, dan kusan kwana uku kenan yana mai-duguri.
     Da hanzari ɗaya a cikin sojojin ya zo zai karɓar ƙatuwar rigarsu ta lauyoyi data fiddo a sit ɗin baya da handbag ɗinta, kanta ta girgiza masa tana ɗan dafeshi da hannu, dan kanta ke mata ciwo saboda fafatawar da sukai yau a kotu da wani shegen lauya mai masifar naci, amma dukda haka ta nuna masa *Mai laya kiyayi mai zamani* dan an yanke hukuncin kuma tayi nasarar kwatoma yarinyar da akaima fyaɗen haƙƙinta.
      Amaan dake jikin Window yana kallonta ya fito cikin takunsa na bajinta da lafiya, yanda take tafiya kamar mara ƙashine yasa harya fito bata ƙaraso ƙofar falonba, gabanta ya tsaya yana maijin tausayin jarumar matar tasa.
     A hanki ta ɗago idanunta da sukai mata nauyi, hannu ya buɗe mata ta shige jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, shima nannauyan numfashi ya sauke yana sumbatar kanta, jikinta ringim da zazzaɓi kuwa.
    “Sannu da zuwa Sweet Fodio na, shine baka kirani ka sanarmin zaka dawo yau ba?” Ummukulsoom ta faɗa a hankali tana ɗagowa daga jikinsa.
    Baice komaiba ya janyeta a jikinsa yana amsar kayan hannunta, itama ya kama hannun nata suka shige ciki.
      Saida suka shiga bedroom ɗinsa da suke amfani dashi ya zaunar da ita sannan yay ɗan durƙuso a gabanta yana kafeta da mayun idanunsa, “Beauty ki ɗauki hutu haka mana”.
    Fusaka ta narke masa, “Dan ALLAH Yaa Amaan kayi haƙuri kaikace haka, idan na aikata haka cases ɗin mutane fa? Ni yanzu ciwon jikine kawai ke damuna, suko jikkunansu da zukatansu duk ke ciwo, karka kalli halin dani nake ciki dazai zama naɗan lokaci, ka kalli su yanda suka tsinci kayinsu”.
     Numfashi ya sauke yana mikewa, kusa da ita ya koma ya zauna ya jata jikinsa ya rungume, hawayen da take maƙalewa tuni sun fara gudu a fuskarta, bai hanata ba, baikuma ce mata komaiba, sai bayanta da yake ɗan bugawa kaɗan-kaɗan, saida tayi mai yawa sannan ya ɗagata ya cire mata kayan jikinta, da kansa yay mata wanka, ta ɗauro alwala suka fito.
     Tunda cikin ya bayyana bata iya girki, dan ko tayi bata iya ci, Amaan kuma ba zama sosai yake a gidaba, tafiye-tafiyansa yayi yawa, hakan yasa Maman Ahmad ta juri kawo musu a kowanne lokaci, yau ɗinma itace ta aiko ma Amaan abinci.
      Fita Ummukulsoom tai zuwa kicin ta haɗo musu fruit salad, dan tafi ƙaunar shansa fiye da komai, saiko tuwon Amala ko na dawa, a cikin firij ɗin dani ta saka ta wuce ɗaki danta gabatar da sallar la’asar, dan Amaan ma ya fita sallar.

★★★★

      Yanda take shan fruit salad ɗin hannu baka hannu ƙwaryane ya saka Amaan kallonta cike da tausayawa, ya amshi spoon ɗin yaci gaba da bata da kansa yana faɗin, “Beauty yunwa kikeji, amma bazakiji abinci ba sai baƙin tuwo, ni wannan Friendy n nawa bansan da wane salo tazo ko yazo ba” yay maganar hannunsa akan cikinta daya fara tasowa.
     Murmushi kawai tai masa ta zare cokalin tana cigaba da shan kayanta ganin yana ɓata mata lokaci.
        “Sweet Fodio kasan wane tunani nakeyi kuwa akan zancennan na basiru?”.
        Kallonta yay ba tare daya amsaba, amma hakan yana nufin hankalinsa na a kanta. Ta haɗiye abinda ke bakinta tana kuma dai-daita murya, “inaga ya kamata mu fidda maganarnan duniya ta sani, mutumin nan ɗan siyasa ne, bazaiso sunansa ya ɓaciba, da yaji zancen zai karaɗe duniya zai fara ƙokarin binne case ɗin, mukuma ta wanna hanyarne zamu kamashi dumu-dumu”.
      Kansa ya shiga jinjina mata idonsa kafe a kanta, tabbas ya aminta da zancenta, dan abubuwansu na kamanceceniya da juna musamman ta fannin bincike. Ganin ya fahimceta saita ƙara faɗaɗa masa bayani akan shirinta, a daren ranar kuwa suka saki bayanai ta hanyar wani abokin Amaan baban ɗan jarida dake da gidan tv nasa na kansa.
       A safiyar washe gari kuwa labari ya fara fita


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

         Hankali tashe Meenal da taci karo da zancen a social network ta samu mom nasu, dan matakin farko dasu Ummukulsoom suka fara bi kenan, sanin mafi yawan al’umma sun raja’a da social network yanzu, a take Momin su Meenal ta kira dadinsu dake can yana fafutukarsa ta ƴan siyasa, dan an kadashi ne a wannan zaɓen bayan ya kammala shekara huɗunsa, zuwa yanzu kuma soyake ayi hannun karɓa tsakaninsa da gwamnan daya kadashi bayan ya gama burin yin shekara takwas, daganan ya fito takarar shugaban ƙasa.
     Lamarin ya girgizashi, a take ya nema wani alƙali amininsa akan ayi duk yanda za’ayi case ɗin basiru ya canja salo zuwa wani abun daban, dan shifa har zuwa yanzu bai taɓajin zai yafema basiru ba saboda dukan da yayma meenal wanda ya barmata ƙaton tabo a fuska da duk sanda suka gani sai sun tuna da abinda yayi.
      Dama idonsu Ummukulsoom akansa suke, dan haka sukai amfani da wannan damar wajen yima baba mahaifin basiru jagora ya shigar da ƙara a wata babbar kotu dake nan kaduna da taimakon Abba da Dad.
       A daren ranar aka miƙama mahaifin Meenal sammaci daga kotu, sannan aka saka police binciko dukkan prison dake cikin katsina neman basiru.
          Har dai washe gari babu wani labari dangane da samun basiru, sai da akabi wasu manyan matakai kafin ai nasarar ganosa cikin gaggan ɓarayi, a yanda shirin mahaifin Meenal yakema saura kwana ɗaya kacal a kashe su basiru.
       A yanayin da aka ɗakko basiru daga jail abun babu daɗin gani, dan dolema aka zarce dashi asibiti daga nan, ashe dukan tsiya yaci hannun gayun da suke tare a daren jiya.
     Su Ummukulsoom suna lagos aka sanar musu da samunshi, dayake dukkan komai hannun Abba da Dad ya koma, dan hakama Abba yace Ummukulsoom tabar maganar shiga case ɗin a nemi kwararren lauya daya daɗe a aiki, amma sai Ummukulsoom taita roƙonsu akan zata iya.
     Ummi ce ta bada shawarar su barta kowa ya bita da addu’ar samun nasara, kar a sare mata gwiwa.
       Inna da baba sosai hankalinsu ya kara tashi ganin yanda ɗansu ya koma, ko mai fama da ciwon HIV iyakar lalacewar da zaiyi kenan, banda ƙwala-ƙwalan idanu babu abinda kake gani a jikin basiru, ya rame iyakar ramewa, fuskarsa kam tayi baƙi duk ya koje tayi tabbuna na raunikan duka saikace wani tsohon ɗan daba, ga wasu ƙuraje da duk suka bata masa jiki harma fuskar masu shegen wari dan ƙazanta, duk mai imani ya gansa saiya tausaya masa.
      Kwana biyu da samo basiru Ummukulsoom da Amaan da Attahir harma da a maman Ahmad suka dira kd da daddare, dan washe garine za’a fara shiga shari’ar su basiru.
      Kallo ɗaya Ummukulsoom ta iyama basiru dake barcin wahala ta fito abinta, jarumta sosai ta nuna wajen danne kukanta dan kar zuciyar Amaan ta sosu saboda kishinsa data gama fahimta akan lamarin, dukda da yarjewarsa take komai hakan bai hanashi yawan nuna ɓacin ransa ba idan ya ga ta cika yawan magana akan case ɗin, dan haka saita iya takunta, dan ita harga ALLAH bada wata manufa take hakanba, sam babu wata soyayyar basiru a ranta tun shekarun da suka shuɗe kafinma tasan kanta, tausayin iyayensa ne kawai ya jagoranci damuwarta akan lamarin.
           
★★★★★★

         Duk da ta tashi babu jin daɗin jiki haka ta nuna jarumtarta wajen dannewa aka shiga kotun, a wannan zaman maida kanta sakara tayi a kotun, lauyan da ke kare baban Meenal yanata murna akan ashema shashasha suka samo, danshi kam gaba ɗaya ya rainama Ummukulsoom wayau akan shari’ar, gashi dama a haife zai iya haifarta, danshi shirinma ritaya yakeyi nan kusa kaɗan.
      Jikin su Abba saiya fara sanyi akan yanda Ummu ta nuna sanya a kotu, shiko Amaan dama baima halarci shari’ar ba sam, sai Attahir ne kawai yaje.
          Ummukulsoom guduwa tayi, dan kar kowa yay mata maganar abinda tayi a kotu, dan ita tasan minene a ranta, batason kowa ya shigar mata aiki koda Amaan ne kuwa.
      Dad ne yake sanarma Amaan abinda ya faru a kotu yau, Amaan yay shiru yana nazari, har Dad ma yazata bazai samu amsa ba sai yaga ya nisa yana gyara zama, “Karku damu Dad, kubita a haka kawai, dan Ummukulsoom nada matuƙar wayo, karku ɗauka dan bata jima da fara aiki bane bata gama kwarewa ba, ni nasan tanada dalilin bama wancan lauyan damane, kuma zakace nina faɗa maka”.
      Kai Dad ya jinjina cike da gamsuwa da zancen ɗan nasa. Koda Amaan ya dawo sashensu baima Ummukulsoom maganarba, yama isketa har tayi barcin ta, shima kwanciya yay gefenta bayan yay shirin nasa barcin, ya daɗe yana kallonta tare da shafar cikinta kamar yanda ya saba a kowanne dare har barci ya ɗaukesa.

        Alƙali yabada damar jami’an tsaro su cigaba da tsare basiru, kuma Ummukulsoom ce ta bada wannan damar ta hanyar maida kanta sakara datai a kotu, lauyansu Meenal ya bada hujjoji masu karfi akan kisan kai Basiru ya aikata. Tayi hakanne saboda basiru ya samu tsaro, duk kuma abinda ya samesa a halin yanzu mahaifin Meenal za’a zarga kai tsaye. Shi kansa lauyan su Meenal saida aka fito ya harbo jirgin Ummukulsoom, dan haka hankalinsa ya tashi, wato wanan yarinyar shegen wayone da ita. Sam kasa barci yay a daren, yanata ƙulla dabaru na gaba ta yanda zai bada damar korar ƙarar ma.
     Itako Ummukulsoom da kowa ke ganin bazata iya komaiba bayan  Amaan da yay mata ƙyaƙyƙyawar fahimta barcinta ta kwasa hankali kwance harda munshari, (yo tasan ta gama fafe gorarta harda tanajin murfi, to mizai gagareta aranar tafiya? Idan ance ta fito????????‍♀️).
         Washe garima tunda safe ta fita a gidan, bata dawoba sai kusan 11, harma Momcy ta rufeta da faɗa saboda ko breakfast batayi ba ta fita, aiko itace da kanta ta zaunar da ita ta bata abinci, sai da taci ta ƙoshi sannan Momcy ta barta, shi dai Amaan yana zaune a falon yana jinsu da kallonsu amma uffan bai ceba, sai dai harga ALLAH sun birgesa, yanda kowa ke nuna kulawarsa ga matarsa yana tsintar kansa a farin ciki sosai.
       A ranar da daddare suka koma lagos, sai lokacin da aka ɗibarma shari’ar yayi zasu dawo.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

         Dad nidai da zakuji shawarata wlhy da kun janye batun kisannan da kuka ƙaƙabama basiru, gara ku fiddo gaskiyar maganar abinda ya faru ayi shari’ar nan a kansa, ina tsoron karfa shari’arnan ta canja salo muzo mu afka ciki……..”
      “K dalla rufema mutane baki, ke mi kika sani ne? Duk ma abinda ya faru ba kece kika jama mutane ba, inda baki kawo ɗan matsiyatan nan ba a matsayin mijin aure har wannan abun ya farune?”.
     Baki Meenal ta zunɓura tana matsawa daga kusa da yayanta daya katseta a tsawace tamkar zai maketa.
     Shiru falon yayi, sai gungunin Meenal kawai, shima bawani fita yakeyiba.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

      Ɓangaren su Suhailat kam sunji komai daga bakin meenal, sai dai suma fa ba haka sukaso lamarin ya kasanceba dan basuso Abban Meenal ya juya zancen zuwa wai kisankai Basiru yayiba, a ganinsu gamma ai shari’a akan abinda ya akata musu a zahiri bawai a sakko wani zance daban ba da sam babushi a tafiyar, hakan tamkar zalintar basirunne kuma. Amma abinda suka sani koma dai miza’ayi gaskiyar zance zai fita suma har a nemosu.


*_BAYAN SATI HUƊU_*
  
             Bayan sati huɗu aka sake zama shari’ar basiru, sai dai fa a wannan karon salon Ummukulsoom ya bama kowa tsoro, musamman data kawo zancen auren Meenal da basiru, dan saida ta gama bincike tsaf akan dukkan aure-auren da basiru yayi hatta da abokansa su Najeeb.
     Ta nemi alfarmar alƙali na ganin Meenal, hakan yasa Meenal tasowa ta tsaya inda ake tsayawa. Wasu irin tambayoyi masu ruɗa tunani Ummukulsoom takema Meenal, har lauyansu yay magana, amma kasancewar tambayoyin Ummukulsoom nakan tsari sai alƙali bai karɓi ƙorafinsa ba aka bama Ummukulsoom damar cigaba da yima Meenal tambayoyi.
       Meenal fa ganin za’a ƙureta saita zurma bisa ga ƙafa da Ummukulsoom ta bata nayin talala a tambayar data jefa mata ta ƙarshe.
      Gyan-gyan gyan gyan, zancen Meenal fa ya tabbata, dan shari’a ta canja salo, cikin hikima da dabaru na Ummukulsoom ta dawo da shari’ar ainahin kan hanya na batun dukanta da basiru yayi, bawai batun kisan kai da akace yayi a farko ba.

★★★★★★

      A can ɗilau kuwa labari nata yawo cewar Ummukulsoom tazama alƙaliya????????, wai itace kema basiru shari’a bayan mijinta ya ƙwatoshi hannun ƴan shan jini, shima basirun ashe ɗan shan jini ya zama shiyyasa yay kuɗi yaketa auren ƴaƴan masu kuɗi (sharaton kenan sunan wata ƙarya????????????⛹????‍♀️)

          A wannan zamanma ba’a yanke hukunci ba, dan alƙali ya buƙaci ganin matayen da duk basiru ya aura a tsawon rayuwarsa.
      Wannan zance ya hargitsa hankalin Meenal, dan abinda bata taɓa saniba kenan koda a mafarkinta, ashe kafin ita Basiru yama zauna da wasu matan a matsayin rayuwar aure?.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button