NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Chapter 13….

Yaune kwanaki ukun da Zaid ya ɗibar mawa Zahrah suka cika cif cif, don haka yau da wani irin matsanancin faɗuwar gaba ta wayi gari, haƙiƙa bazata yaudari kanta ba, tasani cewa ƙwarai zuciyarta ta aminta da Zaid to amma babban abun dubawa shine, shin Zaid ɗin yadace da rayuwarta kuwa? ko kaɗan bata hango dacewarsu da Zaid ba, duk da tasan cewa tana da kyawun da kowani ɗa na miji zaizo da ƙoƙon soyayyarsa gareta, amma bata tunanin haɗuwarsu da Zaid zaiyi dai dai, kallo ɗaya zakaima Zaid kafahimci cewa shiɗin mai tarin arziki ne, haka ma iyayensa, itakuwa bakomai bace face TALAKA ƴar TALAKAWA wacce talauci yabayyana tambarinsa ajikinta, sam bata mawa kanta adalci ba matsawar ta ɗauki kanta takai zuwa matsayin da bana taba, wasu irin hawayene suka shiga gangarowa daga cikin idanun Zahrah, yayinda zuciyarta keyi mata zafi, batasan menene so ba, domin bata taɓa yi ba, amma a yanda takejin Zaid acikin zuciyarta, yasa tafara kokonton cewa takamu da tsananin soyayyarsa, gaba ɗaya wunin yau a susuce tayi sa, damuwarta ɗaya idan Zaid yazo maizatace dashi ? idan ta furta masa kalmar ƙi to fa har abada bazata taɓa yafemawa kanta ba, domin ta cutar da zuciyarta, idan kuwa ta furta masa kalmar so, tofa ba makawa tajefa kanta acikin ɗauri ne mai wuyar suncewa…. Wunin ranar dai haka Zahrah tayi shi sukuku babu daɗi, fargaba ne fal cike a zuciyarta….koda tayi Sallan la’asar banɗaki tashiga tayi wanka , zama tayi akan katifarta, haɗe da ɗauko wata hand bag ɗinta, wanda ciki take ajiyar kayan kwalliyanta, duk da cewa dai itaɗin ba mace bace ma’abociyar yawan kwalliya,, hakanan ta tsinci kanta da son yin kwalliya a yau ɗin, hoda (powder) ta murza akan fuskarta, haɗe da shafa janbaki (lipstick) dark maroon colour, akan laɓɓanta, black eye pencil, tasanya acikin idanunta, haɗe da shafa mascara akan zara zaran gashin idanunta, take fuskar Zahrah tasakeyin kyau, duk da dama cewa itaɗin mai kyauce,, wata Arebian gown maroon colour tasanya ajikinta, sosai da sosai rigar ta amshi jikin Zahrah, tayi mata ɗas, duk acikin kayanta Zahrah tana matuƙar son rigan, domin kuwa maman khausar ce takawo musu, ita da khausar ɗin, daga Saudiya,, rigace mai kyau da tsadar gaske, uwa uba idan ta sanya rigar ita kanta tasan tanai mata kyau,, kan katifarta ta koma ta zauna, bayan tagama kimtsa kanta, jigum tayi tana tunanin waishin maiyasan yata yin kwalliya batare da wani dalili ba? “saboda Zaid zai zo, zuciyarta ta bata amsa, “idan kuma baizo bafa ?” tatambayi kanta, take wani irin faɗuwar gaba ya ɗarsu acikin zuciyarta, wanda batasan dalilin faruwan hakan ba,, abu kamar wasa, har yammaci ta rufa babu Zaid babu alamarsa, tuni jikin Zahrah yayi sanyi laƙwas,, hardai akayi sallan Isha, ba’azo daga waje ance anaƙiran Zahrah ba,, tuni ta wanke ɗan kwalliyan da tayi a fuskar tata ma, domin zuwa yanzu tacire rai da zuwan Zaid… Zaune take a tsakar gida, gabanta ɗauke da kwanon shinkafa da wake, a hankali take tsakuran shinkafan tana kaiwa bakinta, kallo ɗaya zakai mata kahango tarin damuwa acikin zuciyarta,, kamar daga sama wani yaro yashigo, yace wai anaƙiran Zahrah a waje,, wani irin farincikine ya lulluɓe zuciyar Zahrah, domin kuwa tana kyautata zaton cewa Zaid ne,, koda tashiga ɗaki don ɗauko mayafinta saida tasake murza powder a kan fuskarta haɗe da sanya kwalli a idanunta, Zahrah dai bata tsayananba hadda shafa jambaki,, wani rover hijab tasanya ajikinta, kalar maroon, wato kalar doguwar rigan dake jikinta, gaba ɗaya lufayar iyaka cinya ta tsaya mata, hakan kuma yayi nasarar bayyana surar jikinta, kasancewar lufayan mai rover ce, tayi kyau kuma balaifi, tamkar dai balarabiya, abunka da farar fata,, turarenta mai sauƙin kuɗi (TONY MONTANA) tafeshe jikinta dashi, take ta ɗau ƙamshi,, a hankali take taku harta fice daga cikin gidan nasu,, koda tafito daga gidan cikin nutsuwa take takunta, yayinda kanta ke duƙe a ƙasa, zuciyarta kuwa bugawa tashiga yi akai akai,, kaitsaye tanufi wajen da taga motarsa na fake,, tun da tafito daga cikin gidan, ya kafeta da mayun idanunsa, masu rikita mata, sosai yau ɗin tayi masa kyau, hakanan yaji sha’awarta ta ninku akan nada,, tana ƙarasowa wajen motar ta sa, taja ta tsaya, still kuma kanta na kallon ƙasa tana wasa da yatsun hanunta, a. hankali yabuɗe murfin motar tasa haɗe da ziro ƙafafunsa waje, take wani irin fitinannen ƙamshin turarensa yacika ko’ina na wajen, a hankali ta lumshe idanunta, domin kuwa bakaɗan ba ƙamshin turaren nasa ya tafi da’ita,, kallonta ya shiga yi tundaga ƙasanta harzuwa samanta, kafun ya saki shu’umin murmushinsa, “MY ZAHRAH !!” yaƙira sunanta da wani irin murya mai sauƙar da kasala, kasa amsa masa Zahrah tayi saima sake sadda kanta ƙasa tayi tana mai wasa da yatsun hanunta,, murmushi yakumayi a karo na biyu, “yau kuma tsayuwa kikeji da shi ?” yayi tambayar cikin nuna halin ko inkula,, jin haka yasanya ta gane mai yake nufi, jiki a sanyaye ta nufi ɓangaren mai zaman banza tabuɗe murfin motar haɗe da shiga ta zauna,, a hankali Zaid ya yi ƙasa da kujerar dayake zaune, ɗan zamewa yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran haɗe da lumshe kyawawan idanunsa, a hankali Zahrah ta ɗan saci kallonsa haɗe da cewa “Ina wuni !” jin muryarta da yayi ta ratsa kunnuwansa yasa sa ɗagowa, yazauna haɗe da kafeta da’idanunsa, yakai kusan 3 minute yana kallonta “kinyi kyau !!” yafaɗa in a unigue voice ɗinsa, wani iri Zahrah taji a cikin jikinta, wannan shine karo na farko a duniya da wani ɗa namiji ya fara faɗa mata cewa tayi kyau,, cikin salonta na kunya, ta ɗago idanunta takalleshi karab idanunta suka sauƙa acikin nasa idanun, wani irin shock taji ajikinta, da sauri tayi ƙasa da kanta, cikin salonsa ya ce ” Idan kinajin kunyana ta ya ya zaki iya nunamin zallar soyayyar danake buƙata a wajenki ? inasonki da duka zuciyata My Zahrah ina fata kema zaki soni kamar haka ko fiye da haka ? ” a yanda yayi maganar idan kakallesa zaka iya rantsewa cewa bashine yayi ba,, jitayi jikinta gaba ɗaya yayi laƙwas, wani irin zazzafar ƙaunarsa takeji yana huda kowani irin saƙo na jikinta, a hanakali ta ɗago manya manyan idanunta da suka cika da ƙwalla, ta sauƙe su akan kyakkyawar fuskarsa, cikin murya mai rauni tasoma cewa “bantaɓa soyayyaba, bankumasan ya akeyinta ba, ni marainiyace bayan Allah sai Baffana nakedasu acikin wannan duniyar, nasan kafi ƙarfin ajina, dan Allah kada kayaudareni da soyayyarka ” taƙare maganar lokacin da hawaye suka shiga sauƙowa a kan fuskarta,, kafeta da idanunsa yayi harnatsawon wasu mintuna, shikaɗai yasan abun da yake saƙawa acikin zuciyarsa,, “Idan kin yarda dani to kibani soyayya da amincewarki, nikuma bazanci amanarki ba” yayi maganar cikin muryarsa mai sanyawa zuciyarta nutsuwa,, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da yimawa Allah godiya daya kawomata ma’agaji adai dai lokacin da ta ke buƙata, shirune yashiga tsakaninsu na ɗan wani lokaci, bayan Zaid yagama saƙa abun da zai saƙa acikin zuciyarsa, yasaki wani irin killer smile haɗe da mai da kallonsa ga Zahrah, “ya kamata ki kaini nagaidasu Baffa ko ” ya yi maganar yana mai kashe ma ta idanunsa ɗaya,, murmushi kawai zahrah tayi haɗi da cewa “banaje na sanar dasu to ” buɗe murfin motar tayi ta fice haɗe da shigewa cikin gida, bayanta kawai Zaid ya ƙura ma wa ido bakaɗan ba ya kwaɗaitu da yarinyar kuma insha Allah saiya cimma burinshi a kanta,, bawani jimawa Zahrah tafito daga cikin gidannasu, kamar dai ko da yaushe kanta duƙe yake a ƙasa harta ƙaraso garesa,, iso tayi masa zuwa cikin gidannasu, gaba ɗaya a takure take domin kuwa itace a gaba shikuma yana biye da’ita a baya, ahaka suka shiga cikin gidan,, cike da ƙyanƙyami Zaid yazauna akan tabarmar da Inna ta shimfuɗa ma sa a tsakar gidannasu, tunda yake a duniya yaune karo na farko a rayuwarsa da yafara zama cikin gidan talakawa, lallai idan yakama Zahrah ba zai mata da sauƙiba, da ƙyar ya’iya kai zuciyarsa nesa yagaisa dasu Baffa da suka ƙura masa ido, tamkar sunga baƙon halitta,, har rige rigen amsa gaisuwar tasa Inna da Baffa sukeyi, daganinsu kaga mayun ku ɗaɗe,lol, shirune yabiyo baya bayan sungama gaisawa, domin dai harga Allah Zaid bayi da abun cewa, saboda shi bai ma taba irin hakan ba, bayan iyayensa babu wasu wanda yataba gaisarwa da ladabi haka, sai gashi yau akan wata tatsitsiyar yarinya yazo yana kaskantar da kansa gaban talakawan unguwa, lallai yaci amanar jinkai dakuma ajinsa, amma yazaiyi tunda shiyake nema dole yayi biyayya,, ganin yayi shirune yasa Inna gyara zama hade da cewa, ” munagodiya sosai bawan Allah ga me da taimakon mu da kakeyi, Allah ubangiji yasaka da alkhairi, ” murmushi kawai Zaid yayi hade da mikewa tsaye, bandir din kuɗaɗe yaciro daga cikin aljihunsa, hade da ajewa akan tabarmar daya tashi,, tsadaddun takalmansa yasanya hade dayi musu sai anjima yafice daga cikin gidan, “bawan Allah harda dawainiya haka to to masha Allah, Allah yasaka da alkhairi ” Inna tafada tana mai washe baki,, Zaid yana ficewa daga cikin gidan, Inna da Baffa suka dakamawa kudin wawa, Zahrah dake tsaye a gefe kuwa idanunta ne suka ciko da kwalla, sam batajin dadin abun da Baffa da Inna sukeyi, suna nuna zalamarsu afili,, “Miye kika yi wani ƙasaƙe kina kallonmu bazaki bisa ba ” Baffa yafaɗa yana hararan Zahrah, jiki a sanyaye Zahrah tarufa mawa Zaid baya,,,, Zaid kuwa yana fita kaitsaye motarsa ya wuce, sosai yaji daɗin yanda ya hango zallan son kuɗi irin na Baffa da Inna, tabbas yanzu yasake samun ƙwarin guiwa akan burinsa, yanzu yasan cewa bazai wahala wajen samun galaba akan Zahrah ba,,, tana fitowa ya sakar mata kyakkyawan murmushinsa, wanda yake ƙara mawa kyakkyawar fuskarsa kyau aduk sanda yayi sa……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button