SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Hawayen da suketa ambaliyan sauƙa akan fuskarta yashiga share mata, haɗe da ɓare wani sweet yajefa acikin bakinsa, kwantar da’ita yayi akan ƙirjinsa haɗe da ɗago fuskarta ya tura mata sweet ɗin acikin bakinta, harshensa yasanya yana meyi mata wasa da sweet ɗin acikin bakinta, lumshe idanunta tayi tana me sauƙe ajiyar zuciya, yayinda yake shafa mata bayanta ahankali,,har wani irin nannauyan bacci yazo ya ɗauketa….. Kafeta yayi da idanunsa aransa yana me godia ga Allah daya basa wannan mata me ɗauke da tarin ni’imomi na fili dana baɗini, kai yasha sweet fa yau harwani jin kansa yake a sama.Lol,,, batare da yayi aune ba shima bacci ya ɗaukesa bayan yayi musu addu’a yashafa mata… Good night angon me daɗi…
(???????????????? bani nayi typing ɗinba yau????????????????… Kada kumantafa kuzo cin cake????????)
22/January/2020
Fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI!!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed
CHAPTER 96 to 97
Tun da ta tashi tayi sallan asuba take ta ruskar kuka tamkar wacce aka cewa wani nata ya mutu, ita kanta batasan kukan me takeyi ba, amma dai hakanan takeji zuciyarta babu daɗi, gashi gaba ɗaya jikinta ciwo yake, “Gaskiya Doctor mugune.” tafaɗi haka acikin zuciyarta, gaba ɗaya ya gajiyar da ita, daga ƙasan zuciyarta kuwa wani abune yayi mata tsaye wanda kuma shine sanadiyar kukan nata, wannan wace irin rayuwa ce? wace irin ƙaddara ce wannan? rabonta da tayi farinci me tsayi tun kafun Zaid yashigo cikin rayuwarta, ada tana ganin rayuwar da takeyi acikin gidansu rayuwar ƙunci ce, ashe bata sani ba wannan rayuwar salama ce a gareta, SO baiyi mata adalci ba, so bai kyautawa rayuwarta ba…
Yajima tsaye akanta yana me ƙare mata kallo, mamakin yanda take kuka tsakaninta da Allah yake, a iya saninsa banda abun daya wakana atsakaninsu daren jiya baiyi mata komai ba, amma kuma sai gashi yanzu tana ruskar kuka, har a ƙasan zuciyarsa bayason kukanta, idan yaji kukanta jiyake gaba ɗaya nutsuwarsa ya ƙaura daga jikinsa,, ahankali yashiga takawa harzuwa inda take duƙe akusa da gado tana kuka, sam batamasan da shigowarsa ba kukanta kawai takeyi…. Hanunsa yasanya ya dafa kafaɗanta, da sauri ta juyo aɗan razane don bataji shigowarsa ba,, idanunsa ya ƙanƙance haɗe da waresu alokaci guda, zama yayi akan gado haɗe da ɗagota zuwa jikinsa…
“Me yasa Zahrah? me nayi miki? meyasa kike ƙuntatawa rayuwarki akan wani dalili naki? ban aureki don nazuba miki ido kita cutar da kanki ba, please ki daure zuciyarki kidaina wannan kukan banaso!” ya faɗi maganar cikin lallashi… Saurin ɗauke hanunsa dake kan wuyanta yayi, kansa yaɗan ɗafe haɗe da zaunar da ita akan gado, direct wani ɗan madaidaicin drawer yanufa, maganin da yasan zai sauƙar mata da zazzaɓi acikin mintuna ƙalilan ya ɗauko tare da ruwan gora ya dawo zuwa gareta. Maganin ya ɓalla ahanunsa tare da jawota jikinsa, bakinta ya buɗe ya jefa maganin aciki haɗe da bata ruwa, babu musu ta haɗiye maganin bayan ta rumtse idanunta, sai kace wacce aka bawa guba… Aje goran ruwan yayi haɗe da sake jawota jikinsa, kwantar da kanta yayi akan ƙirjinsa, yayinda yake shafa bayanta a hankali. Ajiyar zuciya haɗi da sheshsheƙan kuka kawai take sauƙewa. Shikuwa Dr.Sadeeq wani tunani na daban yakeyi acikin zuciyarsa, hakanan Allah ya halittamasa tsananin tausayin Zahrah acikin zuciyarsa, yana sonta sosai, bayason yaga tana cikin damuwa, bayajin akwai wani abu aduniyar nan da Zahrah zata nema agaresa matuƙar yana dashi tarasa, zai iya mallaka mata komai nasa, matuƙar zataji daɗi, za kuma tayi farinciki, bakinsa ya kawo daf da kunnenta cikin murya me sanyi yace
“Zahrah!”
Tanajinsa amma kuma saitayi sauri ta lumshe idanunta, tanaso ya ɗauka cewa bacci take.
Jin tayi shirune yasanya yashiga goga mata lallausan sajensa akan fatar wuyanta, yayinda yake yawo da hanunsa akan bayanta a hankali..
Luf tasakeyi acikin ƙirjinsa, tana jin saƙonsa yana tsarga mata hartafin ƙafarta, yayinda daddaɗan ƙamshin turarensa ke ƙara sanyaya mata jiki, batajin bacci ko kaɗan, amma kuma yazama dole ta ƙwaƙulowa kanta baccin dole, kodan ta samawa zuciyarta salama. “Ina laifin Dr.Sadeeq? mene bayi dashi wanda mace takeso tasamu ajikin ɗa namiji? miye laifin masoyin daya nuna maka haƙiƙanin so? ashe wani lokacin zuciya batasan menene halacci ba? me yasa SOYAYYA tazamo guguwa me hargitsa zuciyar ɗan adam tayi fatali da komai nasa?” itakam ko da a yanzu soyayya ta barta haka ta gama iya cutarta, cuta me muni ma kuwa.. Yajima yana shafa bayanta, harsai da ya ji sauƙar numfashin dake nuna cewa da gaske bacci ya ɗauketa. Kwantar da’ita yayi akan gado, haɗe da jawo blanket ya rufe mata duka jikinta, yasani sarai batason sanyi, don haka ya rage gudun A.C, kashe mata fitilan ɗakin yayi, kana ya jawo mata ƙofar ya rufe mata bayan yafita zuwa falo.. Laptop ɗinsa ya ɗauka haɗe da buɗewa, aikinsa ya shigayi cikin nutsuwa, ɗan kwana biyun nan da bai shiga office ba haryatara ayyuka masu yawa, gashi ansanar masa patients suna buƙatar taimakon sa, duk da ya ɗau hutu ma ashe bai tsira ba, ayyuka na nan akansa wanda yazamana dole sai shi zaiyisu…
GERMANY
Shikaɗai yake rayuwarsa acikin ɗakin, yau kwanansa ɗaya kenan baisanya komai na abinci acikin saba, yayi matuƙar ramewa alokaci guda, yayinda gashi dakuma sajen dake kwance akan fuskarsa suka ƙara yawa fiye da na da, duk da dama cewa shi mutum ne me yalwan suma, kallo ɗaya zakayi mai kasan cewa yana ɗauke da damuwa me tarin yawa acikin zuciyarsa, Zaid ɗin da dana yanzu sun banbanta, wan can Zaid ɗin zuciyarsa cike take da isa, ɗagawa, girmankai, rashin sanin darajan ɗan adam, Zaid ɗin da mashayine, mazinaci, wanda bai ɗauki zina abakin komai ba, haka kuma Zaid ɗin da, baisan menene damuwa ba, baisan menene rashi ba, samu kawai ya sani, sannan kuma baisan menene ƙunci da ɗaci ba, baikuma san menene wani abu waishi soyayya ba. Zaid ɗin daya kasance yanzu kuwa, wani mutum ne dayake cikin ƙunci, zuciyarsa tana cike da tarin damuwa, Zaid ɗin yanzu yarasa duk wani farincikinsa, yarasa jin daɗi, yarasa nutsuwar zuciya data ƙwaƙwalwa. “ko wannan baici yasa Zahrah ta tausaya masa ba? shin wai shi kaɗaine yataɓa aikata abun da baidace ba?” yatambayi kansa, abu biyune suke damunsa, zazzafar soyayya dakuma rashin nutsuwa da salama dake damunsa, yanzu shikaɗai yasan halin dayake ciki, baya iya bacci, baya iya cin abinci, bayajin daɗin komai nasa, gaba ɗaya duhu ya mamaye rayuwarsa, yanzu yafara zargin cewa zunubansa ma sunyi masa yawa, yasani ƙwarai, yasan abu me kyau da kuma marar kyau, amma saboda ruɗin duniya gaba ɗaya ya shagala. (Yawancin mutane yanzu rayuwarsu sukeyi saka ka, zasu aikata zina, zasu sha giya, zasu aikata duk wasu aiki dake jawo musu manya manyan zunubai, amma kuma yawancinsu sunfi gudun kunyar duniya data lahira, suna tsoron wani yakamasu suna aikata zina, amma basa tsoron kallonsu da Allah yakeyi, wasu sun maida zina manshafawarsu, suna ganin kamar hakan wayewace, bayan kuma suna sane dacewa aikata ta babban halaka ne, Ya ALLAH kaci gaba da karemu, kakuma tsaremu da sharrin zina, ka rabamu da zama da mazinata, Ameen Ya ALLAH!)