SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Yariga daya gama yanke hukunci cewa ko da su Dad ɗinsa basaso saiya koma Nigeria, bazai iya zama anan ba, zafi yakeji acikin zuciyarsa marar misaltuwa idan haryatuna da cewa Zahrah’nsa tana can gidan wani, sai yaji gaba ɗaya nutsuwarsa ta gushe, wataƙila ma wannan banzan Doctor ɗin ya kusanci Zahrah’nsa, ae kuwa baisan sanda ya ƙwalla wata irin ƙara ba, azuciye ya ɗauki wani flower dake gefen gadon, yayi jifa dashi, take kwalbar flower’n ya tarwatse a tsakiyar ɗakin, duk da haka hakan baiyi masa ba, saida yataka ya ƙarasa gaban mirror, da hanunsa ya daki mirror ɗin, take mirror’n ya tarwatse har saida ya yanka masa hanu, amma saboda tsananin kishi’n dake cinsa, ko zafin ciwon baiji ba.
“Hakane ma, yakusanceta” wata zuciyartasa ta faɗa masa..
“No!!! it will never happen, i Know Zahrah will not do it, bazata taɓa iya bawa wani kanta ba bayan ni, because she know we love each other” yafaɗi haka da ƙarfi cikin wata irin murya, me ɗauke da tsananin ɓacin rai, durƙushewa yayi a ƙasa haɗe da sanya hanu ya dafe saitin zuciyarsa wacce take bugawa da sauri, da dukkan alamu dai ya tsokalowa kansa. Haki yasomayi tamkar wani wanda yayi gudu, tarine ya sarƙesa, take jini yasoma fitowa ta bakinsa, shi kaɗai yayi tarinsa harya ƙare, ya galabaita sosai da sosai, da ƙyar ya’iya jan jikinsa ya shiga toilet, wanke bakinsa yayi kana yafito daga cikin toilet ɗin, numfashi kawai yake maidawa cike da wahala,, wani ɗan abu yadanna, bayan kamar minti 1 saiga wata cleaner tashigo cikin ɗakin, nuni yayi mata da inda jininsa ya ɓaɓɓatata, babu ɓata lokaci ta sanya kayan aiki ta gyara wajen, tana kammala gyaran kuwa wasu likitoti su biyu suka shigo cikin ɗakin.. Duba lafiyar jikinsa suka sake yi haɗe da basa wasu magunguna, wata allura sukayi masa da take matuƙar sa bacci, domin kuwa gwaje gwajen da sukayi masa yasa sungano cewa baya samun wadataccen bacci.
Suna fita ya lumshe idanunsa, wanda tuni suka zama jan gauta, saboda tsabar tsananin kishi dake cinsa, jiyake ma kamar idan ya ƙara kwana ɗaya ba acikin Nigeria ba ya cutu, gwamma yaje ya ƙwace Zahrah tunkan wanda ya ɗauka bakomai ba ya ɗanɗana masa zumarta. (Hahhh guy ae ka makaro,yasin doctor yajima da ɗanɗanawa????) **** Mintuna kaɗan dayi masa alluran, bacci me nauyi yayi gaba dashi…
Dad ne ya nutsu haɗe da dawo da kallonsa ga Mummy. “Inaga abu ɗaya zamuyi masa yamanta da wannan yarinyar, kawai na yanke shawara aure zanyi masa.”
Shaye da mamaki Mummy take kallon Dad. “Aure fa kace Alhaji? wakake tunanin zata iya zama da Zaid, da irin wannan halinnasa? hmmm bana majin cewa Zaid zaiso wata mace bayan wannan Zahrah’n, ni nama fara tunanin cewa asirce masa zuciya tayi, amma inbanda haka taya lafiyayyen ɗa namiji kamar Zaid zai maƙalewa mace ɗaya kamar maye”
Murmushi Dad yayi haɗe da girgiza kansa, “itadai Safara’u haka take, idan ana magana me hankali saikuma tana sako wasu abubuwa kamar na wasa.” dad yafaɗi haka acikin zuciyarsa, afili kuwa gyara zamansa yayi haɗe da sake fuskantarta…
“A wannan karon dagaske aure zanyi masa, saboda aure ne kaɗai zaisanya Zaid dawowa cikin nutsuwarsa, bandamu da ko yanason matar ko baya sonta ba, nasan watarana ahankali zai sota ya manta da waccar”
“To Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, amma gaskiya nima banjin daɗin ganinsa acikin wannan halin dayake ciki yanzu,ko abincin kirki wallahi bana iya ci” Mum tafaɗi haka cikin tausayawa ɗan nata….. (Team Zaid kunji fa wai aure za’ayi masa me zakuce? wayaga Zaid da auren dole)
NIGERIA
Tunda ta kwanta bacci ba’ita ta tashi ba sai 11:30 am, ko tsayawa nemansa yau batayi ba tafaɗa bathroom, wanka tayi kana ta fito daga cikin bathroom ɗin… Mai kawai ta shafa kamar kullum sai kuma powder, itakam batason cika meckup akan fuskarta.
Riga da sket na atamfa tasanya, wanda yayi mata caras ajikinta, ɗan kwalin kayan kawai ta yafa akanta zuwa kafaɗarta. Direct falo ta nufa sai tashin ƙamshi take, kamar yanda tayi zaton zata ganshi a falo, sai taga saɓanin haka, domin kuwa babu shi babu alamarsa,, kallonta ta mayar kan dinning area saidai taga kan table ɗin wayam babu food flask ko ɗaya,, hahhh take idanunta sukayi raurau dasu, ɗan ƙaramin bakinta ta tunzuro haɗe da shafa cikinta, “Yanzu kenan Doctor da yunwa ya barta?” ta tambayi kanta…
Motsi ta soma ji daga ɓangaren kitchine, tsoro ne yaɗan kamata dan tasan Dr.Sadeeq da kansa kam bazai shiga kitchine ba, “to kodai basu kaɗai bane acikin gidan?” tasake tambayar kanta. Cikin sanɗa take takawa harta isa ƙofar kitchine ɗin, motsinne yasake tsananta, don haka cikin sanɗa ta tura kanta cikin kitchine ɗin.
“Kamata!!!” taji anfaɗa da ƙarfi. Wani irin ƙara ta ƙwalla haɗe da rugawa a guje ta koma cikin falo.. Dariya yashiga yi mata bayan yafito daga kitchine ɗin hanunsa riƙe da plate wanda yake ɗauke da soyayyen chips..
Zamewa tayi aƙasa haɗe da dafe ƙirjinta, nunfashi take fitarwa da ƙyar, da’alama ta tsorata sosai.
Zama yayi akan kujera har yanzu dariya yakeyi mata, yasan zata tsorata amma baiyi tunanin tsoron nata zai kai har haka ba.. “Yadai karfa ki sume min” yafaɗi haka yana me ɗan tsagaita dariyarsa…
Ɗan ƙaramin bakinta ta tunzuro gaba haɗe da miƙe ƙafafunta akan sofa, “Nidai Allah ka tsoratar dani, please kada ka ƙara zan iya mutuwa fa!” taƙare maganar cikin tsantsar shagwaɓa.
“Kindai tsorata kanki, ni bani na tsorataki ba ƴan mata, da wayace ki shigo kitchine ɗin cikin sanɗa?”
“To ba motsi naji ba, na ɗauka ko aljanine!” still cikin shagwaɓa takumayin maganar..
Kallonta kawai yashigayi yana murmushi, a garin gudu harta yada ɗan kwalin dake kanta bata sani ba, hakanne yabaiwa gashinta damar bayyana.
Jingina da kujera tayi, tana me sauƙe ajiyar zuciya, sai yanzu ta fara dawowa daidai.
Ƙaurin abinci yasoma ji da sauri yatashi ya nufi kitchine, aikuwa yana zuwa ya tarar da soup ɗin daya ɗora akan wutane yasoma ƙonewa, da sauri ya sauƙe haɗe da ƙwaɗawa Zahrah ƙira..
Saƙare tayi tana kallon yanda yake kwashe soup ɗin ƙwai da albasa yana sanyawa acikin wata ƴar ƙaramar kula, dariya ne ya ƙwace mata, cikin dariyan tace “Doctor dama ka iya girki ne?”
Hararan wasa yayi mata haɗe da cewa “Na bugawa a jarida ma kuwa”
Dariya ta ƙara kwashewa dashi, wai iya girkinnasa har na bugawa a jarida ne hmm. Ɗan matsowa tayi kusa dashi haɗe da leƙa tukunyar da akayi soup ɗin aciki, da sauri ta sanya hanu ta toshe bakinta, dariya ne yazo mata, gaba ɗaya cikin tukunyar yayi baƙi, soup ɗin yasoma ƙonewa..
“Miye wai kikewa dariya? yarinya zaki faɗa wa mutanen garinkune anjima, kin kuwasan daɗin girki na yafi na kowa ko” yaƙare maganar yana me ƙaƙalo ƙasan tukunyar daya ƙone zai zuba acikin kulan. Dasauri ta rike hanunsa haɗe da cewa “Idan kazuba wannan fa soup ɗinnan bazai ciwuba”
“Meyasa, ko hassada kikeminne?”
Yatambayeta yana me ɗage giransa ɗaya..
“Shikenan to, tunda kanaga kamar wasa nake ma, amma kuma idan kasa akan abincinka yayi ɗaci ni ba ruwana” tafaɗi haka tana me sake hanunsa.