SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallonta ya ɗanyi haɗe da marerece fuska. “Yazanyi to Zahrah, banaso kitashi kinajin yunwa banbaki abinci ba, shine na soyamiki chips yanzu kuma gashi nayi soup ɗin kince wai ya ƙone bazai ciwuba, ko zamuje resturant ne?” gaba ɗaya fuskarsa ta sauya da alama shagawaɓa yakeson yi mata..
Wani irin tausayinsa ne taji ya daki zuciyarta Allah sarki, ashe duk akantane yaketa shan wannan wahalan.. “A’a basai munje resturant ba, zan ma iyaci a haka fa ai ba duka soup ɗin bane ya ƙone, kuma ma basai muci da tea ba!” cikin yanayi na kulawa ta ƙare zancen..
Cikin jin daɗi yace “Yauwa tawan to ɗauki soup ɗin kije, bana haɗa mana tea ko”
“A’a kabarshi ni dakaina zan haɗa mana” tafaɗi haka tana me ƙoƙarin fara haɗa musu tea ɗin. Hanunta ya kama ya sumbata haɗe da ɗaukan kulan da soup ɗin ke ciki yanufi falo… Mintuna kaɗan tafito da ɗan wani tray wanda yake ɗauke da kofuna biyu na tea ɗinsu.. Aje tray ɗin tayi akan sofa haɗe da maida kallonsa gareta, gani tayi ya kafeta da idanunsa, wanda suke daɗa sawa tanajin nauyinsa..
Ɗan shagwaɓe fuska tayi haɗe da cewa “To miye kake kallona!”
Murmushi yasakar mata haɗe da tasowa daga inda yake zaune, zama yayi akan sofan, dakansa ya zuba musu soup akan chips ɗin, loman farko Zahrah ta tauna wani Chips da bai gama soyuwa ba, kallonta yayi haɗe da cewa “Ya kikaji yayi daɗi ko? ai nasan ma zaiyi daɗi”
Murmushin dole tayi haɗe da cewa “Yayi daɗi sosai”
Hanu yasanya yashafi kumatunta, “Yauwa My Zahrah ae dama nasan saikin yaba”
Da ƙyar ta’iya danne dariyarta, loman farko da yayi ya ɗago kansa ya kalleta, itama kallonsa takeyi, saitaga ya ɓata fuska kamar zaiyi kuka, bazata iya riƙe dariyarta ba yanzu kam yazama dole saita dara, sake shagwaɓe fuska yayi ganin yanda takeyi masa dariya. Da ƙarfi yajawota jikinsa haɗe da murɗe mata hannayenta “Wakikewa dariya?”
Cikin dariya tace “Kayi haƙuri nifa badakai nake ba, dariyarce kawai tazomin”
“Uhhh aini ba yaro bane nasan ni kikewa dariya, to amma ai balaifi na bane laifin gas ɗinne da bai ratsa kaskon suyan da kyau ba, kuma ko kema ae nasan haka zaiyi miki”
Itadai dariya kawai takeyi masa, gaskiya wannan girkin nasa kam yacancanci abugasa a jarida kamar yanda ya faɗa, onion and egg soup ya ƙone dankali kuma bai soyuba.
Haka suka haƙura da dankalin suka sha tea tare da snacks kawai. Bayan sungama cin abincin ya jawota jikinsa, haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta, lumshe idanunsa yayi yana me sauƙe numfashi a hankali, wani abu yakeso daga gareta wanda yasan idan ya nema balallai yasamuba, kuma ma koda yasamu to ba a son ranta ta basa ba, shiyasani matuƙar zasu kasance waje ɗaya da’ita tofa har abada acikin sha’awarta zai kasance.. Jin yanda yake sauƙe mata numfashi akan wuyanta ne yasanya jikinta yin sanyi, ahankali kasala tasoma dirar mata, itama lumshe nata idanunta tayi, tana me yin wani tunani acikin zuciyarta.. Tsawon mintuna 15 suka ɗauka a haka babu wanda yace da ɗan uwansa ƙala, shi dai Dr.Sadeeq tsundum yake acikin kogin sha’awa, yayinda itakuwa take tsundum acikin kogin tunanin wani abu wanda bashida amfani a wajenta, wani abu wanda tunaninsa yazame mata jiki da jini, sai dai kuma tasan abun baidace da itaba, baidace da rayuwarta ba, ƙaddara ce kawai ta haɗasu, sannan kuma zuwa yanzu yakamata ace ta manta da babinsa, takuma daina tunasa, sai dai kuma duk yanda taso hakan yakasance abun yaci tura, dole zata haɗa da addu’a, saboda addu’a yafi gaban komai, duk da cewa dama tanayi amma dole zata ƙara akan wanda takeyi…
A hankali yajanyeta daga jikinsa haɗe da miƙewa yanufi ɗaki, da kallo kawai tabisa harya shige cikin ɗakin, “Meke damunsa?” tatambayi kanta a bayyane.
Ganin batada maibata amsa, baikuma dace ta zauna batare da taji damuwarsa ba yasanya ta bisa zuwa cikin ɗakin..
Kwance ta iske sa akan gado yayi ruf da ciki yayinda yasanya hanunsa ɗaya akan mararsa, sam bata fahimci wani abu game da hakan ba, ahankali taƙarasa wajen da yake, cikin murya meɗan sanyi tace “Bakada lafiya ne?”
“Lafiyana ƙalau, kawai dai bacci nakeji ne” yafaɗi haka ataƙaice, baison yayi magana me tsawo ta harbo jirginsa, tsakani da Allah bayason yasake takurata, jiyama da yayi, yauda safe da kuka ta tashi masa, saboda haka yanzu baison ya ɓallo liƙi gwamma yabari ko zuwa dare ne ma, amma kuma idan yatuno irin daɗin dayaji jiya, sai yaji kamar bazai iya haƙura ba.. Haurawa tayi kan gadon haɗe da kwanciya a bayansa, ƙurawa kwantaccen gashin kansa ido tayi, abubuwa da yawa nasa suna matuƙar burgeta, babu ma kamar idanunsa, idan yana kallonta harwani mutuwa jikinta yakeyi, babu ta inda Dr.Sadeeq ya gaza, komai nasa yayi 100%.
“Ɓacci bai isheki bane?” yayi mata tambayar batare daya juyo zuwa garetaba.
“A’a kawai dai ina hutawa ne” tafaɗi haka a taƙaice don talura kamar bayason damuwa.
Ƙarar wayartane ta karaɗe cikin ɗakin, da sauri ta ɗauko wayar dake aje kan ɗan ƙaramin drawer’n gefen gado.. Ganin Husnah ce me ƙiran yasanya ta ɗaga wayar da sauri, tana ƙoƙarin yin magana taji muryar Husnah tace “Gani a falo”
da sauri tatashi daga kan gadon haɗe da ficewa daga cikin ɗakin, ko bayani bata tsaya yiwa Doctor ba. Shikuwa da kallo kawai yabita harta fice daga cikin ɗakin, lumshe idanunsa yayi haɗi da sauƙe ajiyar zuciya.
Da gudu Zahrah taje ta faɗa jikin Husnah, rungume juna sukayi ƙam cike da kewar juna.
“Nayi kewarki sosai ƙawata” Husnah tafaɗi haka tana me ƙara rungume Zahrah.
Tureta Zahrah tayi haɗe da ɗan turo baki gaba. “Bawani nan ni ae nayi fushi, tunda ranan nan kin yaudareni kin gudu”
Dariya Husnah tayi haɗe da cewa “Yi haƙuri amaryar likita”
Dariya suka sanya su dukansu, saida Zahrah ta cikawa Husnah gabanta da su drinks kafun tazo ta zauna akusa da ita..
“Gaskiya dole ne nima acikin wannan shekaran nayi aure, kiduba kiga 2 days kacal amma gaba ɗaya sai wani shining kike” Husnah tafaɗi haka tana me ƙarewa Zahrah kallo.
Harara Zahrah ta wurgawa Husnah “Kinganki ko wallahi banason tsokana, ae ko a engine aka sani baici ace zuwa yanzu nafara walwali ba”
“Hahhh kedai faɗi gaskiya don da alama doctor madara na musamman yake shayar dake kullum”
Dariyane yakama Zahrah “wai madara” hmmm itasam bata fahimci inda kalaman Husnah suka dosa ba..
“Ke dai baki rabo da tsokana, wace madarace zatasa acikin 2 days kacal na sauya” Zahrah tafaɗi haka tana me duban skin ɗinta..
“Hahhhh madara mana irin taku ta masu aure, ae babe kawai ki manta, nasan kinbasa yasha kuma kema yabaki kinsha”
Sai yanzu Zahrah ta gano me Husnah ke nufi, duka ta ɗaka mata abaya haɗe da yin dariya. Husnah ma dariyan tayi, kana taɗauki drinks tasoma sha..
Hira sosai Husnah da Zahrah sukayi, duk da Husnah tace bajimawa zatayi ba. Bata jima ba kuwa tayi tafiyarta bayan tabawa Zahrah wasu ingantattun magunguna wanda Hajiya Shuwa ta bata tace takawo mata, har bakin gate Zahrah ta raka Husnah, cike da kewar juna sukayi sallama…
Kallon Dad ɗinsa yayi arikice gaba ɗaya idanunsa sun rufe, miƙewa yayi tsaye yasoma takawa ahankali, ganin zaifita daga cikin ɗakinne yasanya, Dad yayi saurin riƙosa, “Bazaka iya kulawa da kanka ba Zaid, badai Nigeria kakeso mu koma ba?” cike da kulawa Dad ya tambayeshi..