SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsaye tagansa daga shi sai 3 guater jeans ajikinsa, kallo ɗaya tayi masa tayi saurin ɗauke kanta, har yanzu bata taɓa amincewa yaga tsiraicinta cikin haske ba, sannan haka itama bata taɓa tsayawa takalli jikinsa acikin haske ba komai sunayinsa ne acikin rashin wadataccen haske, “Jikinsa yanada kyau” tafaɗi haka acikin zuciyarta haɗe da ɗan satan kallon 6 packs ɗin dake kwance akan cikinsa.
Raɓawa yayi ta gefenta yashige cikin bathroom ɗin fuskarsa ɗauke da wani irin murmushi.
Wata ƴar ƙaramar riga wacce ta tsaya iyaka guiwarta kawai ta sanya haɗe da sanya igiyoyin dake gaban rigar ta ɗaure cikinta, haurawa tayi kan bed ɗin ta kwanta.. Yana fitowa yakuma sanya wani 3 guater jeans ɗin haɗe da feshe jikinsa da turare.. Wutan ɗakin yakashe yakunna musu na bacci, hawa kan gadon yayi haɗe da jawota jikinsa, kwanciya ajikinsa yanayi mata matuƙar daɗi shiyasa aduk sanda yajawota jikinsa bata bijirewa. “Kinyi addu’a?” yatambayeta.
Kai kawai ta ɗaga masa alamar “Eh” addu’a yayi shima ya shafa kana ya lumshe idanunsa, ahankali yake shafa bayanta, cikin mintuna ƙalilan bacci ya ɗauke ta, sannu sannu shima bacci me nauyi ya ɗaukesa….
Washe Gari.
Ƙarfe 5 dai dai jirginsu ya sauƙa acikin Nnamdi Azikwe International airport.
A hankali yake taka matattakalan sauƙowa daga cikin jirgin, sanye yake da riga da wando irin na sanyi navy blue colour, hatta takalman dake sanye a ƙafafunsa navy blue colour ne, yayi kyau sosai yaƙara haske, sai dai kuma sosai rama ta bayyana kanta ajikinsa. Yana gama saƙƙowa daga kan matattakalan yanufi wajen da motocin da sukazo ɗaukarsu ke fake, 4matic yabuɗe yashiga haɗe da hakincewa agidan baya, bayasan damuwa shiyasa bayason shiga mota ɗaya dasu Dad ɗinsa.. Harsuka isa gida tunani yakeyi, maiya kamata yayi? sai kuma yanzu daya dawo yakeji gaba ɗaya Nigeria’n tayi masa ƙunci haɗe dayi masa duhu,daya kulle idanunsa Zahrah kawai yake gani… Yana fita daga cikin motar direct ɓangarensa dake cikin gidannasu ya nufa. Falo’n sa tsab-tsab yake tamkar wanda wani yake rayuwa aciki, bedroom ɗinsa ya wuce, yana shiga yaƙarasa gaban wani tangamemen hotonta da yasa aka masa kalanda (Calender) dashi yakafa ajikin bangon ɗakin, rungume ƙaton kalandan yayi haɗe da lumshe idanunsa.
“I really Miss you My Zahrah!”
ya faɗi haka cikin murya me sanyi da kuma tsananin rauni, hanu yasanya yashafa daidai saiti laɓɓanta dake jikin hoton calender’n.
“Bana tunanin zan daina kewarki Zahrah na, tunaninki yazama abincin ruhina, inasonki sosai, lokaci yayi daya kamata ki dawo gareni, muyi rayuwar auren mu cike da tarin farinciki, nadaina komai Zahrah shan giya, zina, duk na daina please ke nake jira har yanzu, ina fata baki bawa wanina kanki ba?” yanayin yanda yake magana da hoton idan ka gansa kaitsaye dasunan mahaukaci zaka ƙirasa, domin kuwa me cikakken hankali bazaiyi haka ba.. Wayarsa ya ɗauka yayi dialing number’n Abid, bugu uku Abid ya ɗauki wayar baijirayi abun da Zaid ɗin zaice ba yace
“Wow surprise kenan?”
Ƴar ƙaraman tsuka Zaid yayi cikin muryarsa me rauni yace “Inason ganinka Abid, yanzu agidan mu please!” baijirayi me Abid ɗin zaice ba ya katse wayar haɗe da cilla wayartashi kan gado, yasan Abid bazaiƙi zuwaba shiasa baijirayi amsar saba yakashe ƙiran. Zama yayi akan wata kujera dake cikin ɗakin, kan ɗan madaidaicin fridge’n dake aje cikin ɗakin ya maida idanunsa, jiyake kamar yatashi yaje ya ɗau wine ɗinsa yasha, sai dai kuma wata zuciyar tana gargaɗinsa da cewa, Zahrah bataso, tun randa ta gayamasa wata baƙar magana akan shan wine da yake, bai ƙara shaba harkuwa rana me kamar ta yau, duk da kuwa irin azabtuwan da yakeyi idan baisha wine ɗin ba, saboda yariga daya saba. Shiru kawai yayi haɗe da kama kansa ya rumtse idanunsa.. Abid ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo bakinsa ɗauke da sallama, ciki ciki Zaid ya amsa masa sallaman haɗe da watsa masa idanunsa da sukayi jajur dasu.. Cike da mamaki haɗi da tsoro Abid ya matso kusa da Zaid da ɗan sauri.
“Zaid meke damunka haka? yaushe kuka dawo? yajikin naka?” duka waƴannan tambayoyin Abid yayiwa Zaid su a lokaci ɗaya kuma duk amsarsu yake nema idan zai samu..
“Abid nakasa mantawa da ita, itace nutsuwar tunani na, banajin zan iya kaiwa lokaci me tsawo batare da na sanyata acikin idanuna ba, Inasonta sosai kai kasani!”
Kallon Zaid kawai Abid keyi yamarasa me zaice masa.. Kallon ɗakin yashiga yi sai alokacin ya Lura da maka makan hutunanta dake manne ajikin bangon ɗakin Zaid ɗin,wasu zane ne wanda Zaid ɗin yayi wasu kuwa hotunanta ne. Wani irin tausayin Zaid ɗinne ya tsirga masa me tsanani, shidai bazaice baitaɓa soyayya ba, amma kuma baita ɓayin kwatan kwacin irin wannan son me tsanani da Zaid keyi ba. Zama yayi akan kujeran dake fuskantar na Zaid, hanun Zaid ɗin yakamo haɗe da cewa “Kazama jarumi Zaid, kada kamanta fa yanzu Zahrah matar wani ce kuma….”
“Ya isheka haka Abid!!” Zaid ya katse Abid cikin tsawa sosai.
“Matar wani, Matar wani, abun da kuke ta faɗa kenan, meyasa ni bazaku duba halin danake ciki ba? shikenan don tana matar wani sai nadaina sonta? kafun wanda kuke ikirarin matarsace yasota nine nan nafara sonta, kada kataɓa tunanin zan daina son Zahrah Abid, bakuma zan taɓa samun nutsuwa ba harsai Zahrah ta zamo mallakina, kataimakeni Abid kazo muje gidanta mu ɗaukota tazo nan mu rayu tare nasan itama tana sona!” cikin murya me tsananin rauni yake faɗan maganar..
Kai kawai Abid yake girgizawa azuciyarsa kuwa wutar tausayin Zaid ne ta kunno, So yamakantar da zuciyar Zaid yasanya harya kasa tuna cewa Zahrah a yanzu ta haramta a garesa, shi duk iskancinsa baya tunanin Zaiso matar da take da aure, dukansu shida Zaid sunsani cewa shangiya da zina duk haramunne amma kuma saboda son zucia irin tasu suke aikatawa, yanzu kuma ga wani sabon saɓon da Zaid yafito dashi, yana goya masa baya akan komai, amma a wannan karon kam baya tunnin zae goya masa baya yaci gaba da son matar aure, haƙiƙa Zahrah takai macen da kowani ɗa namiji zai sota, amma kuma tunda ayanzu tazama mallakin wani babu amfanin Zaid yata takura kansa akanta. “Zaid!” Abid yaƙira sunansa araunace. Kansa kawai ya ɗago ya kallesa batare dayace dashi komai ba.
“Kada kaga laifina Zaid, mun hau wani mataki da yanzu dole ne mufaɗawa kanmu gaskiya, menene ribar da zakasamu idan kacigaba da dakon soyayyarta acikin zuciyarka? tazarar dake tsakanin ka da Zahrah a yanzu yanada matuƙar yawa, tana tare da mijinta kuma nasan zuwa yanzu tajima da zama shi kuma shima yazama ita, me yasa to kowannan bai isa yasanya kacireta acikin zuciyarka ba, akoda yaushe kada kana tunanin cewa wai Zahrah zata dawo gareka, so ne yasa mijinta ya aureta, kaga kenan haka nan kawai bazai rabu da ita ba, kasa aranka ma idan ƙaddara ta rabasu babu yiwuwar Zahrah zata amince ta aureka, kai da kanka kasan haka amma zuciyarka tana yaudaranka, haƙiƙa nima shaidane akan cewa har yanzu Zahrah tana sonka, amma hakan bawai yana nuni da cewa zata iya kashe aurenta ta aureka ba ne, kai koma da ace tafito agidan aurenta to bana tunanin Zahrah zata amince ta aureka, kamanta da ita Zaid, kasawa zuciyarka salama, akwai mata da yawa acikin ƙasarnan dama sauran wasu ƙasashen kasamu wata kabawa ajiyar zuciyarka, na tabbatar watarana komai zai zamo labari!” Abid yaƙare maganar yana me dafa ka faɗan Zaid almar son ƙarfafa masa guiwa..