SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Wata tsuka me ƙarfi Zaid yaja haɗe da ture hanun Abid dake kan kafaɗansa… har abada bazai daina yiwa wanda yace yarabu da Zahrah kallon mahaukaci ba, wai Zahrah’nsa ake so yamanta ya daina sonta, sai yaushe mutane zasu gane cewa cire so bakamar cire takalmi bane? miƙewa yayi daga zaunen da yake haɗe da shigewa cikin bathroom ko sake kallon inda Abid ke zaune baiyi ba.. Ajiyar zuciya Abid ya sauƙe haɗe da gyara zamansa akan kujeran, yana nan yanajiran fitowarsa koda awa ɗaya zai share a banɗakin bazai tafiba saiyajirasa, Zaid bayason gaskiya wani lokaci, kuma kozai mutu saiya faɗamai gaskiya, ae soyayya ba hauka bane, son matar aure mezai jawo maka inbanda wahala da ƙarin zunubai….
Zaid kuwa yajima tsaye ruwa na fitowa daga shower yana dukan jikinsa…. Ɗaure da towel a ƙugunsa yafito daga cikin bathroom ɗin, kallo ɗaya yayiwa Abid yaɗauke kansa, Abid na kallonsa har yagama shafa man lotion ajikinsa…
“Saboda nace kamanta da Zahrah shine kake fushi dani? kai kanka kasan abun da kakeyi ba daidai bane Zaid sannan…..”
“Ya isa Abid!” Zaid ya katsesa aɗan kausashe.
Murmushi kawai Abid yayi haɗe da sa kai yafice daga cikin ɗakin, yasan Zaid ya hau sama bazai taɓa sauraransa ba, wanda yayi nisa bayajin ƙira.
Tun fitarsa ta shige cikin kitchine yau bataso ya sayo musu abinci tafiso ta girka musu da kanta, fried rice tayi wanda taji zallan tsokan kaza, da kanta ta haɗa shaka ta sanya acikin fridge, takammala komai yanzu saura kawai tayi wanka.. Ƙaran wayarta take ta jiyowa, da sauri tanufi ɗaki inda wayartata take. Wata number ce special ke yawo akan screen ɗin wayar, ɗan tsayawa tayi tana ƙarewa number’n kallo, har ƙiran ya katse bata ɗauki wayarba, wani ƙiranne kuma sake shigowa…. A hankali ta ɗaga wayan ta kara akan kunnenta.
“Zahrah!!!” taji wata murya wacce bazata taɓa mantawa da itaba ta ƙira sunanta, jikinta ne yasoma rawa yayinda bugun zuciyarta yaƙara tsananta shin dagaske ne kokuwa kunnuwanta ne basuji da kyauba, kusan mintuna biyar ba asake cewa komai daga cikin wayarba haka kuma itama bata ce komaiba..
“Wa….y..e?”
tayi tambayar cikin wararrun kalmomi yayinda tsoro ke sake ɗarsuwa acikin zuciyarta.
“Zahrah na! me yasa zaki barni? kin barni cikin ƙunci da tarin damuwa, yazanyi da soyayyarki ne Zahrah, bazan iya rayuwa ba idan babu ke, please ki taimaki rayuwata dakuma zuciyar da ta jima da matowa akan ƙaunarki!!”
Jikinta ne gaba ɗaya yaɗauki rawa harbatasan sanda wayar ta zame daga hanunta ba, take ta faɗi ta tarwatse a ƙasa. Itakanta batasan sanda ta zame ta durƙusa guiwowinta a ƙasa ba, hawayene suka shiga fitowa daga cikin idanunta. “Zaid” shine sunan da take ta nanatawa acikin zuciyarta, sai yaushene Zaid zai barta ta huta tayi rayuwar aurenta cikin nutsuwa? anya kuwa Zaid baisamu matsalan ƙwaƙwalwa ba? ta tambayi kanta, shiru tayi haɗe da lumshe idanunta ƙirjinta kuwa har yanzu bai daina bugawa da sauri ba.
Cikin tsananin mamaki yake kallonta, da sauri ya ƙaraso inda take durƙushe haɗe da tsugunnawa yaɗaura hanunsa akan kafaɗunta
“Meke faruwa?” yatambayeta cike da kulawa.
Da sauri tabuɗe idanunta da suke a lumshe, batasan yaushe yashigo ba.
Kallonta yakeyi sosai da alama amsa yakeson ji daga bakinta.
Dasauri tashiga goge hawayenta haɗe da tashi tsaye, kallonta yakeyi harta shige cikin toilet, idanunsa yasauƙe akan wayarta wanda ta tarwatse akan tiles gaba ɗaya ma screen ɗin wayar ya fashe, mamaki haɗi da ɗaurewar kaine matuƙa suka kamashi, “Meya faru? yaganta tana hawaye gakuma wayarta daya gani aƙasa a tarwatse” yayi mawa kansa tambayar cike da son sanin amsa. Tattare wayar yayi haɗe da komawa kan gado ya zauna zuciyarsa cike fal da tarin tambayoyi..
Zahrah kuwa tana shiga cikin toilet ta soma sauƙe ajiyar zuciya akai-akai, meta aikata hakane, gashi yanzu yazo ya ganta acikin halin damuwa, tasan dole ne shima saiya sanya kansa a damuwa, yanzu idan ya tambayeta metasan zata ce masa, wasu hawayenne suka kuma zubowa daga cikin idanunta, da sauri ta sanya hanu ta share.. Haka tayi wanka duk tanajin zuciyarta babu daɗi, ɗan ƙaramin towel ta ɗaura ajikinta, wanda yatsaya a iyaka cinyarta. A hankali ta buɗe ƙofar bathroom ɗin tafito, karaf idanunsu suka haɗe waje guda, da sauri ta kawar da kanta gefe, haɗe da nufar wajen drawer.. Kallon santala santalan cinyoyinta da suke bayyane a fili yashiga yi, wani iri yaji acikin jikinsa, da sauri ya ɗauke kansa..
Ganin da tayi cewa baya kallonta ne yasanya tayi saurin zura dogon wando na pencil jeans haɗe da wata farar top shirt me kyaun gaske ajikinta, yaune karo na farko da ta fara sanya irin waƴannan kayan ajikinta, ita kanta saitaga ta burge kanta domin kuwa hips ɗinta sunfito acikin wandon sunyi ɗas dasu kamar wanda aka zana.. Kasa daurewa yayi saida ya kafa mata idanunsa, sosai tayi masa kyau baitaɓa ganinta acikin irin wannan shigar ba, ta ɗau hankalinsa ƙwarai lallai Zahrah macece har mace komai nata me kyau ne… Tana tsaka da shafa turare ajikinta taji yaƙira sunanta. Tsayawa tayi cak daga abun da takeyi haɗe da juyowa sai dai bata kallesa ba ta amsa ƙiran dayayi mata.
“Zonan!” yace da ita ata ƙaice.. Ahankali tashiga takawa harzuwa inda yake, tana ƙarasawa garesa ta durƙusa a ƙasa haɗe da sunkuyar da kanta tana me wasa da yatsun hanunta.. Hanunta yakamo haɗe da jawota jikinsa ya zaunar da ita akusa dashi, cike da kulawa haɗi da lallami yashafa kumatunta yace “Kinyi kyau”
Tsintar kanta tayi dayi masa murmushi kawai…
“Meke damunki? Sannan menene dalilin dayasa naga wayarki a fashe gaba ɗaya kuma tatarwatse?”
Kanta tashiga girgizawa alaman babu
“Kinsan banason ƙarya, menene dalilin da yasa zaki ɓoyemin damuwarki? kada ki manta yanzu bake kaɗai kike iko da kanki ba, nima nan inada iko dake, saboda haka na cancanci ki sanardani damuwarki, ni mijin kine bazan taɓa son naganki acikin damuwa ba!” cike da lallashi ya ƙare maganar.
Mezata faɗa masa? tace masa Zaid ne yaƙirata a waya ko me? ko kuma tace masa hawayen da takeyi duk akan Zaid ne?
“Dagaske nake bakomai, na ɗaga wayar hanuna da kumfa shine ta suɓuce ahanuna tafaɗi” tsintar kanta tayi da basa wannan amsar, duk da cewa ƙarya ba ɗabi’arta bane amma yazama dole yau tayi, saboda sanar dashi gaskiyan lamarin daya faru bashida wani alkhairi saidai ma ransa ya sosu.
Ajiyar zuciya yasauƙe haɗe da jinjina kansa “Naji amma meyasaki kuka?”
Jitayi gabanta ya faɗi amma saita dake tace “Kuka nake saboda na fasa wayata”
Ɗan guntun murmushi yayi sam bai gamsu da maganganunta ba, amma kuma yazaiyi tunda ta ɓoyemasa gaskiya bazai tursasata ba..
“Saboda wayarki ta fashe kawai shine kike kuka? har yanzu dai ke yarinyace ƙarama Zahrah, amma mene abun kuka, idan kikace na saya miki wata kina ganin bazan saya miki bane?”
Kanta ta jinjina alamar “A’a”
“To indai hakane miye na kukan tunda kinsan zansaya miki wata wadda ta fita, kitaimaki zuciyata ki daina sa kanki acikin damuwa please, inasonki banason naga wani abu ya ɓata ranki!”