NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Raunannun idanunta ta ɗago ta kalleshi, wannan maganar daga cikin ƙahon zuciyarsa yake fituwa, tabbas ita kanta ta gamsu da ƙaunar da doctor yakeyi mata ɗari bisa ɗari,   ya cancanci tasakamai da farinciki ne bawai akasin haka ba..

“Ki kwantar da hankalinki, gobe Insha Allah namiki alƙawari zamuje dake ki zaɓi irin wayar da kike so,  shikenan?”

Kanta ta ɗaga tana ɗan murmushi, kamar da gaske maganar wayarce a cikin ranta.. Miƙewa yayi yafaɗa toilet, tanajin sauƙar ruwa aƙasa ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya,  bataso doctor yasan cewa Zaid yafara bibiyar rayuwarta. Sumu sumu haka ta fice falo. 

Tana zaune tayi jigum ya fito daga cikin ɗakin, sanye yake da blue ɗin wando kalan nata, sai dai nasa na maza ne babu ado kamar nata, saikuma farar polo shirt,  murmushi tayi domin kuwa yayi mata kyau sosai, shima murmushin yayi mata haɗe da kashe mata idanunsa ɗaya…

Ita da kanta ta zuba musu abinci, yanaci yanata zuba mata santi, har batasan lokacin da tarin damuwar dake cikin ranta suka kau tasoma ƙyalƙyalewa da dariya ba …


Zaid ne zaune agaban Dad ɗinsa ya sunkuyar da kansa ƙasa, magana Dad ɗin keyi masa amma kuma kwata kwata bayajinsa, hankalinsa da tunaninsa sunyi nisa sosai wajen tunanin Zahrah, muryarta dayaji ɗazu shiya kara rikita masa tunani,  baisauraran Dad dake yimasa bayani amma duk da haka yaji abun da Dad ɗin yafaɗa na ƙarshe, cike da ƙuncin rai haɗe da tsananin mamaki yake kallon Dad ɗinnasa cikin wata murya me ɗaci yace

“Aure fa kace Dad? ni ɗin, kuma da wata ba Zahrah ba?”

Cikin takaici Dad yake kallon Zaid ɗin, wato tunkan ayi nisa ma yafara nuna masa cewa hakan bazai yiwuba kenan.

“Natabbatar kajini, kuma aure babu fashi!” Dad yafaɗi haka a ƙufule, domin kuwa shima yafara gajiyawa da halayyan Zaid na rashin hankali, taya zaka je kana yiwa matar wani soyayya me tsanani irin haka.

Wani murmushi Zaid yayi me matuƙar ciwo haɗe da sanya haƙoransa ya ciji laɓɓansa.

“Bazan iyaba Dad, kaima kafi kowa sanin hakan, aduniyar nan mace ɗaya kawai nakejin zan iya rayuwar aure da ita, bakowa bace kuma Zahrah ce, saboda haka please Dad maganar wani aure na da wata kabarshi don banaso, idan kuma ka matsa shikenan, amma idan kuka tsinci gawanta nayi mata mugun illa kada ku zargeni kufara zargin kanku”  yana kaiwa nan azancensa ya tashi tsaye yafice daga falon mahaifinnasa.. Baki a wangale haka Dad yabi Zaid da kallo har yaɓacewa ganinsa..

“Lallaima kuwa Zaid ya ɗauko babban al’amari, amma kuma wannan karon sam bazai lamunta masa ba aure dole sai yayi masa, acikin satin nan ma kuwa” Dad yafaɗi haka acikin zuciyarsa…

Zaid kuwa yana fita a ɗakin Dad direct motarsa yashiga, dagudun gaske ya ja motar yafice daga cikin gidan,    tafiya yake akan titi amma zuciyarsa ƙuna takeyi masa, har wani ɗaci yakeji a maƙoshinsa, wayarsa ce tayi wani ɗan gajeren ƙara alamar shigowar saƙo (Message), da sauri ya ɗauki wayar ya duba, domin kuwa tun ɗazu dama saƙon yake jira, adireshi ne na gidan da Zahrah take aka turo masa.. Wani mugun murmushi naga yayi haɗe da ɗan dukan kan steering motar, lallai dole zai cimma burinsa ne kota halin yaya kuwa…

Faka motan yayi yana me ƙaremawa gaban gidan kallo, gidane me kyau da kuma aji, dagani kasan ankashe kuɗi wajen tsara gidan, amma Zaid dake kishi yacika masa zuciya sam baiga wani kyawun gidan ba, saima ji da yayi ya tsani gidan..  Idanunsa ya tsaida akan tankamemen gate ɗin gidan tamkar wanda yake karantan wani abu, a hankali ya buɗe murfin motar tasa yafito waje, cikin takunsa na isa yashiga takawa harzuwa wajen gate ɗin……. (????Anya zaishiga kuwa?hmmm inaga dai yau Zaid aƙasam kanta zai kwana????)

(Kuyi haƙuri dan Allah kwana biyu kunjini shiru wallahi neighbour ɗitace tarasu ranan friday da dare shiyasa kuka jini shiru, naji mutuwar ajikina wallahi sosai shiyasa nakasa koda yin typing ɗinne ma, please kusata a addu’anku Allah ubangiji yayi mata rahama, yasa aljanna tazamo makoma a gareta Ameen thumma Ameen. Ina me ƙara neman afuwarku sosai ????????????)

     Tuesday 28/January/2020

           Fatymasardauna

????????????????????????????????????????

      SHU’UMIN NAMIJI !!

     Written By
Phatymasardauna

Dedicated  To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

            WATTPAD
      @fatymasardauna

Editing is not allowed????

        CHAPTER 100 to 101

Tsayawa yayi  yana me ƙarewa gate ɗin kallo, idan da zaibi son zuciyarsa ne, to tabbas da shiga cikin gidan zaiyi, amma kuma saidai wata zuciyar tana gargaɗinsa da kar ya shiga cikin gidan, bawai kuma don yanajin tsoro ba, kawai  dai yana me tausayawa kansa ne, yasan idan yaga Zahrah dole sai ciwonsa yasake motsawa, duk da yanzun ma bawai ciwon nasa ya kwanta bane,   komawa yayi cikin motarsa yazauna, haɗe da Kifa kansa akan steering motar, lumshe idanunsa yayi sai kawai ga hawaye suna fitowa daga cikin idanun nasa, wai yau shi Zaid ke kuka akan mace, lallai rayuwa juyawa take, gashi shikam tajuyo masa da saɓanin tunaninsa…  Ƙarar motar dayaji shi yasanya sa ɗago kansa yakai kallonsa wajen gate ɗin gidan, ko ba a faɗa masa ba yasan motar RIVAL ce (wai  Dr.Sadeeq ne rival ɗin nasa) balle ma kuma yagansa acikin motar, wani irin abune yazo ya tokarewa Zaid maƙoshinsa, baƙinciki, haushi, takaici, da kuma tsanar doctor ne duk suka haɗe masa waje guda. Ji yake kamar yafita acikin motar yaje ya shaƙo sa kozaiji salama acikin ransa.. Har motar doctor tashige cikin gidan  bai ɗauke idanunsa akan gate ɗin ba,   da sauri ya rumtse idanunsa lokacin da motar tagama shigewa cikin gidan aka kullo gate ɗin gidan, da ƙarfi ya danne lips ɗinsa haɗe da buga steering motar,   yanaji yana gani wani  zai yi masa rayuwa da Zahrah’nsa.     “Yanzu Allah ne kaɗai yasan shigarsa mezaiyi mata, wata ƙilama rungumeta zaiyi, wataƙila kuma har kiss zaice zaiyi mata”    wata zuciyar tafaɗa masa haka.  Da ƙarfi ya shiga dukan steering motar,  yana me jijjiga kansa,  ƙwaƙwalwarsa bazata iya ɗaukar masa wannan tashin hankalin ba, jiyake komai na duniyan nan najuya masa,   Allah yasa abun da zuciyarsa ta faɗa masa bahakanne zai kasance ba,  bazai taɓa iya jurewa ba,  hanunsa ya ɗaura adaidai saitin zuciyarsa haɗe da sake rumtse idanunsa, zafi yakeji haɗe da zogi acikin ƙirjinsa,  da ƙyar ya’iya tada motar  ya cillata kan titi a zafafe, gudu sosai yakeyi akan titi babu ruwansa da waƴanda suke gabansa ko suke bayansa, idanunsa sun rufe sosai.. Ikon Allah ne kawai yakawoshi gida, amaimakon yawuce ɓangarensa sai ya wuce ɓangaren mom ɗinsa..

Hajiya Safara’u ce tsaye agaban dinning table tana shirya abinci,  batare da sanin shigowarsa ba saiji tayi anrungumeta ta baya,  ƙamshinsa kaɗai taji tagane cewa tilon ɗanta ne,    mamakine tsantsa ya bayyana akan fuskarta yaushe rabon Zaid yazo ya rungumeta haka?     kansa ya ɗaura akan wuyanta haɗe da sauƙe ajiyar zuciya,  wani abu me ɗumi da taji yana sauƙa akan wuyanta ne yasanya tayi saurin juyowa garesa,     batayi mamakin ganinsa ahaka ba amma ƙwarai tayi mamakin ganin yanda hawaye ke zuba daga cikin idanunsa. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button