NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

  “Zaid!!”

taƙira sunansa cike da tsananin mamaki haɗe da tashin hankali.

Jajayen idanunsa ya ɗago ya kalleta haɗe da sake rungumeta.

“Mom nakasa jurewa, bazan iyaba, please ki ciremin soyayyarta acikin zuciyata, koda zan samu nutsuwa na minti ɗaya acikin ruhi na!”  cikin matsanancin rauni yake maganar gaba ɗaya yazama abun tausayi yadawo saikace yaro ƙarami..

Ahankali Mom take shafa bayansa haɗe da jinjina kanta, tabbas da ace akwai yanda zatayi da ta cirewa Zaid soyayyar Zahrah acikin zuciyarsa, bazata iya jure ganin hawaye da kuma damuwar ɗanta ba.  

Kamasa tayi suka zauna akan kujera, kansa yaɗaura akan cinyarta yayinda ita kuma take shafa  tarin sumar dake kansa .

“Nakanji ciwo acikin zuciyata idan naganka kana kuka Zaid, bansan wani irin soyayya kakeyiwa Zahrah ba, amma kuma bamu da yanda zamuyi  Zahrah matar wani ce yanzu” Mom tafaɗi haka cike da lallashi.

“Mom  ki taimakeni, zafi nakeji acikin zuciyata, yanzu kenan bazan sameta ba?   shikenan har abada saidai naƙare rayuwata a haka babu ita?   bazai yiwuba Mom, dana sani tun farko daban yaudareta ba, dana sani tun farko dana aureta, duk nine najawa kaina ni da kaina na haramtawa kaina ita, nasan dabanyi mata fyaɗe ba dayanzu na sameta, nine fa nayi mata fyaɗe mom, meyasa nayi haka mom? kaicona yau nayi danasanin yi mata fyaɗe da nayi fiye da  ko yaushe!”  yafaɗi haka yana me sake fashewa da kuka kamar yaro..
Mamaki haɗi  da ruɗani dakuma tsantsar kaɗuwa su suka bayyana akan fuskar Mom, kallonsa kawai takeyi zuciyarta na tafarfasa.

“Kana da hankali kuwa Zaid? Fyaɗe fa kace, anya kuwa ƙwaƙwalwarka bata fara taɓuwa ba?”

Sai yanzu yatashi daga kan cinyarta, bayi da wani zaɓi wanda ya wuce yafaɗawa Mom ɗinsa gaskiya…  

“Ban haukace ba Mom, dagaske ne nine nayi mata fƴaɗe, nine nan na tozarta rayuwarta, nine nan na fara gurɓata mata rayuwa, na rabata da farincikinta da duk wani jin daɗinta, narufe idanuna naketa mata haddinta alokacin da take tsananin buƙatar taimakona,  nayi mata fyaɗe  mom nabiye son zuciyata nasan ban kyauta mata ba amma kuma babu yanda zanyi ne yazama dole……”

Tassssss      haka mom ta ɗaukesa da wani irin lafiyayyen mari,  marin daya matuƙar firgitasa ya ɗaiɗaita tunaninsa, tundayake yataso yayi wayo mahaifiyarsa bata taɓa sanya hanu ta mareshi ba sai yau, kai koda tsawa me ƙarfi bata taɓa yi masa ba,  bakinsa ya hangame haɗe da sanya hanunsa akan ƙuncinsa inda ta maresa yana kallonta.

Itakanta mamakin marin datayi masa take, sai dai kuma ranta amatuƙar ɓace yake..

“Kayi mata Fyaɗe? kacuceni Zaid, bantaɓa tunanin zaka iya aikata wannan rashin imanin ga wata ƴa  mace ba arayuwa, meyasa? meyasa? idan aure kakeso meyasa bakayiba?  kahalakar da rayuwar ƴar mutane, kaicon wannan gurɓataccen halin naka,   tabbas yanzu na yarda alhaki ne kawai ke bibiyarka, idan kuwa hakane to wallahi baka ga komai ba arayuwarka,  niba azzaluma bace kuma bana zama inuwa ɗaya da mutum meyin zalunci,  bansan zuciyarka tayi tauri harhaka ba, dahar kake tunanin aurenta, nayi danasanin tura mahaifinka nemamaka aurenta, ashe kai macucine agareta azzalumi, taya kake tunanin zata amince dakai?” kanta tashiga girgizawa haɗe da juyawa ta nufi matattakalan dake cikin falon ranta amatuƙar ɓace, sam batasan abun da Zaid ya aikata ga Zahrah ba sai yanzu, lallai da ita da kanta zata ɗaukawa Zahrah mataki.

Zaid kuwa har Mom tagama haura step ɗin dake cikin falon, bai ɗauke idanunsa akanta ba, mamakine ya lulluɓesa matuƙa, sake shafa kumatunsa yayi inda mom ɗin ta zabga masa mari, baitaɓa ganin ɓacin ran mahaifiyarsa irin nayau ba tun dayake.  Miƙewa yayi yawuce ɓangarensa shi dai idan za amaresa sau million a basa Zahrah to bazai taɓa damuwa ba..

Mom kuwa tana shiga ɗaki wayar Dad taƙira tasanar masa komai,  ɓacin ran da  Mom tashiga  kaɗanne akan  wanda Dad ya tsinci kansa aciki, lallai Zaid yamaidashi mutumin banza, dayasan haka tafaru tsakaninsa da Zahrah da baije ne ma masa aurenta wajen Baffanta ba, wannan ma ai rashin ta ido ne,  amma zaiyi maganinsa ne, jibi jibin nan zai ɗaura masa aure kuma dolensa ne yazauna da matar, hukuncin da Dad ya yankewa Zaid kenan.


Tun jiya suka koma makaranta amma bata samu daman zuwa ba, doctor da kansa yace ta bari sai yau…   Buɗe ƙofar ɗakin tayi ta fito, dagani sauri take,  ta shirya tsab cikin riga da zani na atamfa ta rufa jikinta da wani ƙaton mayafi me ɗan kauri..
Kallonta yakeyi sosai, take yaji wani irin kishinta ya lulluɓemai zuciya,  duk da ba wani kwalliya tayi sosai ba, amma shikam baijin zai barta tafita ahaka,  kishi yake wani ya ganemai fuskar mata, ganin yanda yake kallonta ne yasanya taɗan shagwaɓe fuska haɗe da karyar da wuyanta gefe, don daganin yanda yake kallonta tasan akwai magana abakinsa.

“Banjin zan barki kifita a haka, maza je ki ɗauko hijab kisanya” yafaɗi haka cikin dakiya da’alama babu wasa a lamarin nasa.     Bata musa masa ba ta koma ɗaki, hijab ta ɗauka ta sanya wanda ya tsaya iyaka guiwarta,  tana fitowa yasake kafeta da idanu, har yanzun ma dai baijin zai iya barinta tafita ahaka, gaba ɗaya ma shi kullum gani yake tana ƙara yi masa kyau, nana gaba kaɗan zai hanata fita ne ma kwata kwata.

“Dan Allah yanzu kam kabarni natafi kaga fa zanyi latti!” tafaɗi haka cikin shagwaɓa.

Marairaice fuska yayi haɗe da sanya hanu yashafi sajen dake kwance akan ƙuncinsa, ba tare dayace komai ba yamiƙe tsaye yanufi hanyar fita daga cikin falon, ganin haka yasa itama ta rufa masa baya da sauri…

Tafiya suke amma yaƙi cewa da ita komai, kallon yanda ya haɗe fuska tayi, sai kawai tasaki dariya, wai ahakan shi fushi yakeyi da ita, sam yanayin fushi bayayi masa kyau akan fuskarsa.

“Meyasa bazaka kulani bane wai? idan makarantar ne bakaso sai ka maidani gida, amma kadaina fushi bakayin kyau kwata kwata idan kana fushi”  tafaɗi haka tanaɗan dariya.

Sai alokacin ya juyo da kansa ya kalleta.     “Ni ba fushi nake ba”  yafaɗi haka cikin cushewar murya. 

Murmushi kawai tayi batare da ta sake ce dashi komai ba, saima kwantar da kanta da tayi ajikin kujeran motar tana kallon yanda mutane suke ta hada hadan su.      
A dai dai inda yake ajiyeta lokutan baya yauma anan yayi parking motar tasa, buɗe murfin motar tayi zata fita, da sauri ya riƙo hanunta,  juyowa garesa tayi tana ɗan murmushi,  shima murmushin yayi mata haɗe da matsowa daf da ita, kiss ya manna mata akan kumatunta haɗe da cewa
“Ki kulamin da kanki” 

Tsadadden murmushinta tayi masa haɗe da jinjina kanta alamar zata yi yanda yace. Sai da yaga shiganta cikin hall ɗin da zasuyi lecture kafun ya ja motarsa yabar haraban makaranta baki ɗaya..

Tana shiga cikin hall ɗin suka ɗinke ita da Husnah sukaita hira, kafun lecturer yashigo….

Ƙarfe biyar na yamma suka kammala duk wani lecture  ɗin da suke dashi,  har bakin motar doctor ɗin Husnah ta rako ta..

Ƙoƙarin janta da hira yake amma tayi masa shiru, saboda gaba ɗaya agajiye take, dolensa shima ya ƙyaleta  harsuka isa gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button