NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Da ruwan ɗumi tayi wanka, tana fitowa ta zura wata riga doguwa marar nauyi ajikinta, haɗe da faɗawa kan gado,  numfashi kawai take sauƙewa na gajiya, mintuna kaɗan bacci ɓarawo ya saceta,  koda Dr.Sadeeq ya shigo yasamu tana bacci baiyi yunƙurin tashinta, falo yakoma yayi zamansa….


Bayan kwana uku.

Yau kusan kwanansa uku kenan a guest house ɗinsa yake kwana, gaba ɗaya abubuwan duniyane suka haɗu sukayi masa yawa,  bayacin abinci a iya tsawon kwanakin nan, gashi ciwonsa ya dawo sosai, daga zaran yayi tari sai jini, magungunan nasa ma yadaina sha, addu’a yake Allah yasa wannan ciwon nasa yazamo ajalinsa ko zai samu sauƙin raɗaɗin dayakeji acikin zuciyarsa… 

Horn ɗin motarsa yake dannawa a ƙofar gidannasu  kamar zai tashi sama, da sauri me gadi ya wangale masa gate ɗin gidan ya tura hancin motarsa ciki,    ko kyakkyawan parking baiyi ba, haka yafito daga cikin motar yanufi ɓangarensa,   yana shiga falonsa yasoma ƙoƙarin cire rigar jikinsa,  dai dai lokacin wata ƴar mata shiyar budurwa ta buɗe ƙofar ɗakin dake kusa da bedroom ɗinsa ta fito,  tsananin mamakine yakashe Zaid, kallon tuhuma kawai yake aika mata dashi.

Yanda ta gansa sai da taji gabanta ya faɗi amma dayake  dama tayi masa farin sani yasanya taɗan wayance haɗe da sakar masa murmushi..

Kallonta yakeyi daga samanta har ƙasanta,  “wace ƴar iska ce haka da har tasamu daman shigo masa ɓangarensa har da kuma kutsawa cikin ɗaki?” tambayar da yayiwa kansa kenan.

“Wacece ke? Uban waya baki daman shigomin ɗaki?” ya tambayeta murya a kausashe.
Sai da taji tsoro amma kuma hakan bai hanata bayyana murmushi akan fuskarta ba.   Wani ƙululun takaici da baƙincikine suka cika zuciyar sa, badon komai ba sai don murmushin dayaga tanayi masa.

“Dan ubanki bamagana nake miki ba!” ya kuma faɗa cikin tunzura. 

Yanzu kam ta tsorata dashi sosai da sauri ta juya zata koma cikin ɗakin,  taku ɗaya yayi ya fincikota, yana juyo da ita ya bata kyakkyawan mari akan fuskarta wanda ya sanyata fasa wata uwar ƙara, sosai  zafin marin ya ratsata..

“Bazaki faɗamin mikikeyi a cikin ɗakin nan bako dan ubanki, inaga sainaci uwarki tukun zakimin bayani, banza me kama da fara!!” yafaɗi haka yana me ƙoƙarin zare belt ɗin dake jikin wandonsa, da’alama dai so yake ya jibgeta.

“Kada ka kuskura ka taɓa ta inagaya maka idan bahaka ba ranka zaiyi mummunan ɓaci!”

Muryar Dad da shigowarsa kenan yakaraɗe gaba ɗaya falon, aƙufule Zaid yajuyo yana kallon mahaifinnasa.

“Dole ne zan daketa matuƙar bata ficemin acikin ɗaki ba, taya ma zakubar wata kucaka tashigomin ɓangarena, dubeta fa ƙazama da ita, wata ballagazar mata,  kunfi kowa sanin bana buƙatar ƴar aiki, me yasa to zaku ɗaukarmin? kurasa ma wacce zaku kawomin amatsayin ƴar aiki sai wannan baƙar yarinyar!” Zaid yafaɗi haka yana me nuna ta cike da  ƙyama.

“Ba ƴar aiki bace matarkace, kuma wallahi kada kasake kace zaka saketa nafaɗa ma!” Dad ɗinsa yafaɗi haka  cikin ɓacin rai, baijirayi me Zaid ɗin zaice ba yasakai yafice daga cikin falon..

Tsananin tashin hankali ne ya bayyana akan fuskar Zaid, kalaman Dad ɗinsa sunyi matuƙar sanyasa cikin mamaki.

 “Matata?”

tambayar da ya yiwa kansa kenan, sake kallonta yayi, tana nan tsaye sai raba idanu take kamar mayya, dagani a matuƙar tsorace take..

“Da gaskene abun da Dad ɗina ya faɗa?” yayi mata tambayar babu alaman wasa akan fuskarsa.

Kanta ta jinjina masa alamar “Eh”

Wannan wani irin cin fuskane Dad ɗinsa yayi masa? aure batare da saninsa ba auren dole fa kenan?  ae kuwa yau zataci ubanta ne,  matsowa yashiga yi daf da ita hanunsa yasanya ya damƙi gashin dokin da akayi mata kitso dashi, yawun dake cikin bakinsa ya tofa mata akan fuskarta, cike da tsananin takaici ya tureta gefe, take ta ƙwalla ƙara domin kuwa kan table na glass tafaɗa daya tureta,   baiko saurareta ba ya shige cikin bedroom ɗinsa,    yanashiga cikin bedroom ɗin ya buɗe cikin fridge ɗinsa ya ɗauƙo kwalbar alcohol me matuƙar sanyi,  da ƙarfi ya ɓalle murfin alcohol ɗin yakafa kwalban abakinsa, saida yasha fiye da rabi kafun yayi wurgi da kwalban gefe, wani irin haushin kansane yakamasa, baisan da yaushe yaɗau kwalbar giyan yakai bakinsa ba,  yanaso yadaina aikata duk wani abu dayasan Zahrah bataso amma kuma yau baida wata mafita wacce ta wuce nashan alcohol ɗin,  takaicine yasake cika masa zuciya,   duk waccar shegiyar yarinyarce tasa sa shan alcohol ɗin don haka dole itama sai ya horata, yanzu idan Zahrah tasan yasha alcohol bazata taɓa jin daɗi ba.. Ɗaukar sauran alcohol ɗin yayi yafice zuwa falo, tananan ƙudundune ajikin kujera sai maƙyarƙyata takeyi, matuƙar tsoron Zaid takeyi, ko yanzu dataga fitowarsa saida gabanta yafaɗi..

Direct wajen da take zaune ya nufa,  gashinta yakuma damƙowa haɗe da jawota zuwa tsakiyar falon,  bakinta yakamo da hanunsa ya matse haɗe da tura mata kwalbar giyan acikin bakin nata,  kuka take tana girgiza kanta amma yaƙi sakinta, adole wai saitasha alcohol ɗin, cikin rashin imani irin na Zaid haka ya danne yarinyar mutane ya ɗura mata giya acikinta da ƙarfin tsiya,  sai da yatabbatar ragowan giyan dake cikin kwalbar yajuyemata shi acikinta kafun ya hankaɗata gefe,  ganin yanda take kuka kamar ranta zaifitane,  yasanyasa fashewa da dariyan mugunta,  lokaci guda kuma ya tsume haɗe da kawar da kansa gefe,  miƙewa yayi yafice daga cikin ɗakin, azuciyarsa yace “anjima kaɗan wanka zanmiki da ruwan ƙanƙara dan ubanki…..”

(????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀ Allah yajiƙanki yarinya kinshigo hanun mugu)

  Wednesday/29/January/2020

          Fatymasardauna
????????????????????????????????????????

      
     SHU’UMIN NAMIJI !!

  
     Written By
Phatymasardauna

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

            
            WATTPAD
      @fatymasardauna

Editing is not allowed????

      CHAPTER 102 to 103

Kuka sosai  Afra keyi, wani irin miji ne haka iyayenta suka aura mata? duk da cewa da amincewa da kuma yardanta akayi mata auren, amma sam bata tsammaci mugunta da shuɗewar hankalin Zaid har yakai haka ba, tun da take arayuwarta bata taɓa kwatanta koda shan codine bane ballantana uwa uba giya,   iskancinta baije can ba, duk da cewa itama tana da  nata wayewar.     Wani irin amai tashiga kwarawa atsakiyar falon,  lokaci ɗaya ta harar da duk wani abu dake cikinta, jingina bayanta tayi da jikin kujera tana me da numfashin wahala..

Zaid da shigowarsa falon kenan, yayi saurin toshe hancinsa haɗe da kawar da kansa gefe cike da bala’i yace
“Ke dan ubanki duk girman gidannan kirasa inda zakiyi amai sai a cikin falon nan?  ki share wajennan yanzu kafun infito kokuwa idan nafito nasamu baki shareba nasa ki lasheshi yakoma inda yafito, ƙazama kawai, wai ahakane zanyi rayuwa dake mcheeww!” cikin ɓacin rai yaƙare maganar haɗe da shigewa cikin ɗakinsa..
Jikin Afra na rawa ta ɗauko moper tashigayin mopping ɗin wajen, ƙaramin aikinsa ne idan har yadawo yasamu bata gyara wajen ba yasata ta lashe aman, tabbas tasan zai iya, yau kaɗai tafuskanci cewa shiɗin tsananin mugu ne, wanda babu kamarsa, tana gama gyara wajen ta gudu cikin ɗakin da aka sauƙeta, ɗakin dake kusa da nasa, tanashiga ɗakin ta murza key, haɗe da faɗawa kan gado, tasaki wani irin kuka,  danasani kawai takeyi acikin ranta,  itafa tayarda ta auri Zaid ne saboda dama tuncan yana matuƙar kasheta aduk sanda tagansa sai taji inama dazai zamo nata, sannan kuma gayen akwai kuɗi uwa uba aji, duk da cewa ita ɗinma babanta me kuɗi ne amma baikai na baban Zaid  dashi kansa Zaid ɗin ba,   lokacin da babanta yazo mata da maganan auren Zaid, daɗine yakusa kasheta ganin irin damar da Allah yabata, ashe bata saniba gidan mutuwa takawo kanta, ita da har jinkanta tasomayi, har ɗagawa takeyiwa ƙawayenta, ita adole ta auri namijin duniya, batasan cewa wahala zata ruska ba, ta ɗauka cewa holewa zatayi,  harta fara tunanin ƙasashen da zata sasa yakaita, sai gashi haɗuwarsu ta farko ma da lafiyayyen mari ya tarbeta…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button