NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaid kuwa yana shiga cikin ɗakinsa yafaɗa kan gado haɗe da lumshe idanunsa, kansa ne yake matuƙar sara mae, tun jiya yakejin ciwon kan, amma yau abun ya tsananta sosai,     wata tsuka yaja me sauti, haɗe da sake gyara kwanciyarsa, shi wannan auren ma da aka laƙaba masa kaɗai ya isa ƙara masa ciwon kai, shiba yaro ba, shiba bagidaje ba amma ankama anyi masa auren dole…


Tsaye take agaban dinning area, ta kafesa da manya manyan idanunta, yayinda shikuwa baimasan tana kallonsa ba, hankalinsa gaba ɗaya yana ga agogon dayake ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hanunsa..   Bakomai yasa take kallonsa ba, face kyawun da taga yayi mata,  shadda ne milk colour ajikinsa ɗinkin riga da wando, rigar ta tsaya iyaka guiwarsa, yayi kyau sosai yasha hularsa light brown wanda taƙarawa kwalliyartasa kyau..  Yana ɗago kansa suka haɗa idanu, da sauri ta kawar da idanunta daga kansa, haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa.

Murmushi yayi haɗe da takowa yaƙaraso inda take, hanu yasanya ya rungumota ta baya.

“Namiki kyau ne haka kiketa kallo na?” yatambayeta yana me shaƙan daddɗan ƙamshin jikinta.

Ɓata fuska tayi haɗe da cewa

“Namiji kuma dama yana kyau ne idan yayi kwalliya?”

Dariya maganar ta ta ta basa, juyo da ita yayi yazamana suna fuskantar juna.   

“Eh mana bakisan maza sun mafi mata kyau ba?”  ya faɗi haka yana me ƙarewa fuskarta kallo.

Idanunta ta waro haɗe da  cewa “Maza sunfi mata kyau? cab aikuwa nidai baka fini kyau ba”

Dariya yayi haɗe da ɗan jan hancinta.
“Nafiki kyau sosai ma, nifa banasa jan baki, bana shafa powder, bana sa kwalli, bana kumayin jagira, haka kuma bana wani shafa mai wanda zai sa fatata tayi kyau, komai nawa daga Allah ne, ku kuma mata kullum cikin shafawa da gogawa kuke, kinga kenan dagaske munfiku kyau” yafaɗi maganar yana me ɗan ƙara fito da idnunsa waje.

Duk da tana cikin fushi, amma sai da tayi dariya.  

“Kafaɗi komai ma, amma nidai bazan yarda cewa  wai kafini kyau ba”
tafaɗi haka tana me ƙoƙarin zame jikinta daga cikin nasa. 

Sake riƙeta yayi gam haɗe da cewa

“Dagaske namiki kyau? naga har wani kishi na kike”

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da shagwaɓe fuskarta.

“Idan nayi kyau kaima baka barina nafita, to me yasa kai kakeson yin kyau ako da yaushe? kana tunanin bazanji haushi bane idan wata ta kalleka!” kafun taƙare maganar ma tuni idanunta sun soma kawo ruwa.

“Eh kumafa hakane, harma kintunamin, akwai wata kuwa a asibitin mu, kullum saitace namata kyau, sannan kuma saitace wai ina matuƙar burgeta, gaskiya nima kuma tana burgeni dan a ƴan kwanakin nan harma na fara tunaninta, to mezakice akanta?” yaƙare maganar yana me ɗaga mata giransa ɗaya.

Baki kawai tasake tana kallonsa yayinda wani malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya. Da ƙarfi ta soma turesa tanason ƙwace jikinta daga nasa.   

Ganin haka yasanya yasake riƙeta  da kyau haɗe da cewa

“Mekikeyi haka?”

“Kafi kowa sanin abunda nakeyi,  inatunanin tsayuwan da kakeyi anan kana ɓata lokacin kane, domin wacce kake muradi tanacan tana jiranka, koba don itane kayi kwalliyar ba? ai bana tunanin ni inada wani amfani a wajenka, ka sakeni kaje tayaba kwalliyar taka banaso na ɓata bata gani ba.”

Dagajin yanda take maganar kasan kishine tsantsa kecinta, domin kuwa har hawaye sun gangaro daga cikin idanunta..

Dariya sosai yashiga yi batare daya sake ta ba.

“Kasakeni nace, ai nasan baka buƙata ta!” tafaɗi haka tana me yunƙurin ƙwace hanunta dake cikin nasa.

Da ƙyar ya iya tsagaita dariyan   nasa, yashiga dubanta da kyau, yasani dama da sannu zuciyar Zahrah zata nutsa acikin ƙaunarsa sosai, gashi kuma yafara ganin alama tunda har kishinsa ya bayyana acikin idanunta..

Fuskarta yatallafo da tafukan hanunsa haɗe da sanya bakinsa yashiga lashe hawayen dake fitowa daga cikin idanunta.

“Bazan iya jure ganin matata tana kuka ba, ki kwantar da hankalinki kinji me daɗi na, babu wata mace da ta isa ƙwace miki doctor ɗinki,  ketawace ni ma kuma naki ne,  babu wata kuma danake tunani bayanke kiyarda dani!!” yafaɗi maganar cikin lallausan murya yana me ƙara riƙe fuskarta acikin tafukan hanunsa. 
Ajiyar zuciya ta sauƙe wanda harsaida ya bayyana afili, har cikin ranta taji daɗin maganganunsa, amma kuma afili bata nuna  hakan ba, ƙoƙarin ƙwace kanta daga jikinsa tacigaba dayi.

“Nine bakyaso ko? shikenan tunda bakyaso nariƙeki” yafaɗi haka yana me sake ta yanufi hanyar fita daga cikin falon.  Da sauri ta je ta rungumesa ta baya, wani murmushi yayi haɗe da juyowa  gareta yazamana suna fuskantar juna.

“Dan Allah kada ka ƙaramin irin wannan wasan, gashi duk kasa ma naji natsani komai!” tafaɗi haka a shagwaɓe.

Murmushi yayi mata haɗe da sanya hanunsa yaɗanja kumatunta. 

“Bazan sakeba, kiyi haƙuri kinji me daɗi na!”

Da sauri ta cusa kanta   acikin ƙirjinsa haɗe da sanya hanunta ta  mintsineshi acikinsa.  Da ɗan ƙarfi yace “Ahhhshhhh!”

Dariya tayi masa haɗe da yi masa gwalo ta wuce zuwa dinning domin dama abinci take haɗawa.
Biyota yayi kan dinning table ɗin suka shirya abincin atare,  acikin plate ɗaya sukaci abinci, gaba ɗaya yanzu doctor yagama shagwaɓata abinci ma shiyake bata abaki, har sai ta ƙoshi,   tana ajiye cup ɗin ruwan dake hanunta, ta ɗan saci kallonsa, ta lura tun ɗazu yaketa kallonta.

“Kaima nayi maka kyaun ne, kaketa kallona haka?” ta tambayeshi.

Murmushi yayi mata haɗe da cewa
“Ae ni dama kullum kinamin kyau,  ke mai kyauce ai ako da yaushe, amma kuma…” baiƙarisa maganar dake cikin bakin nasa ba yayi shiru.

“Amma kuma me?” ta tambayeshi da sauri domin atunaninta ta zaci zaice amma bata masa kyau sosai ne.

“Amma bakyason bani abun daɗi na, please yau ki tausayamin kinji, bazan iya bacci bafa yau idan baki bani ba!” yafaɗi haka cikin sigar shagwaɓa haɗe da ɗanyin ƙasa ƙasa da muryarsa.

Maganganunsa kunya suka bata da sauri ta sanya hanunta ta rufe fuskarta,   jawota jikinsa yayi haɗe da sanya bakinsa adai dai saitin kunnenta cikin muryar raɗa yace
“Bazan iya jurewa ba Zahrah, inaso akullum kina bani kanki sau ba adadi, inason kasancewa tare dake ako wani lokaci” bakinta yashafo da hanunsa haɗe da lumshe idanunsa.   “Nayi missing waƴannan lips ɗin amma yau zanyi musu sucking na musamman har ma….” bata jirayi jin ƙarshen zancen nasa ba ta ruga da gudu zuwa cikin ɗaki, bazata iya cigaba da sauraran waƴannan manya manyan kalaman nasa ba. Murmushi kawai yayi haɗe da miƙewa yafice daga cikin falon, dama sabiti zaije.

Tanajin fitar motarsa acikin gidan ta sauƙe ajiyar zuciya haɗe da lumshe idanunta, kwanciyarta ta gyara, tana me tuno kalamansa,    itakanta tana tsananin son taji ta ajikinsa, musamman idan fatarsu ta haɗe waje guda hakan na haifarmata da wani irin yanayi me daɗin gaske,  kallonta ta mayar ga agogon bangon dake kafe acikin ɗakin.   Ƙarfe 11 na rana yau take da lecture saboda haka tana da ɗan sauran lokaci, domin yanzu ƙarfe 10 ma batayi ba, wani English Novel  mesuna  ( Just A Friend)   tajawo haɗe da buɗe chapter’n da take ta soma karantawa, agurin wata ƴar class ɗinsu ta karɓo  shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button