SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ƙarfe 4 na yamma dai dai suka fito daga cikin lecture ɗinsu wanda shine na ƙarshe a wannan ranan, direct library ta nufa saboda akwai wani littafi da takeson dubawa, kasancewar akwai assigment ɗin da aka basu, idan ta samu littafin kuma sosai zai taimaka mata wajen yin assigment ɗin cikin sauƙi. Gaba ɗaya hankalinta naga littafin da take dubawa, sam bata damu da mutanen dake wajenba kasancewar kowa karatu kawai yakeyi. Tana zaro littafin daga ma’ajinsa ta saki murmushi, juyawa tayi daniyar tafiya idanunta suka sauƙa akan shi, waro manyan idanunta waje tayi haɗe da sakin littafin yafaɗi ƙasa. Jikinta ne yaɗauki rawa da sauri ta tsugunna ta ɗauki littafin haɗe da nufar hanyar waje, tsabar sauri har ƙafafunta harɗewa suke, batayi auneba saiji tayi ta buge mutum, da sauri taɗago don ganin waye ta buge, shiɗinne dai tsaye a gabanta yana me kallonta da jajayen idanunsa, da sauri taja baya, haryanzu jikinta rawa yake kamar wacce taga mutuwarta.
“ZAHRAH!”
yaƙira sunanta cikin wata irin murya me matuƙar rauni.
Kusan mintuna uku takasa amsa masa da ƙyar ta iya motsa bakinta,
“I..na..da au..re”
shine kalaman da suka fito daga cikin bakinta awawware batare kuma da ta shiryawa fitowar kalmomin ba.
Rumtse idanunsa yayi haɗe da dunƙule hanunsa. Cikin murya me ɗaci haɗe da bushewar maƙoshi yace
“Nasani!”
Bazata iya jurewa ganinsa ba da sauri ta bi ta wata hanyar ta wuce da gudu, ko takan littafinta daya kuma faɗuwa batayi ba.
Bayanta yabi da kallo haɗe da tsugunnawa yaɗauki littafin, juyawa shima yayi yafice daga cikin library ɗin. Sai dai ko daya fito, ko ƙyallinta bai gani ba.
Zahrah kuwa tana fitowa daga cikin library ɗin direct wani ɗan corridor wanda mutane basu cika yawan bi ba tanufa, kaitsaye ta tsinci kanta awani fili wanda bakowa acikinsa sai shuke shuke, zama tayi akan wani benci dake wajen, haɗe da fashewa da kuka, tashiga ukunta itakam, wannan wace irin jaraba ne, meyasa Zaid bazai barta ta huta bane, jitayi lokaci ɗaya ƙirjinta yayi mata nauyi kamar anɗaura mata gungumen dutse, wayarta dake ringing ta kalla, Dr.Sadeeq ne ke ƙira amma bazata iya ɗagawa ba, ahalin da take ciki yanzu ma batasan me zata ce masaba idan ta ɗaga. Da ƙyar ta’iya tashi tabi ta ƙofar baya tafice daga cikin makarantar gaba ɗaya, tana fita ta tare me taxi haɗe da gaya masa inda zai kaita, ko ciniki basuyi ba ta faɗa cikin motar haɗe da ce masa yaja suje.
Yana kawota ƙofar gida ta basa kuɗinsa haɗe da ficewa acikin motar ta kutsa kanta cikin gidanta.
Bata damu da duhun dake cikin ɗakin ba haka ta faɗa kan gado ko mayafin dake jikinta bata cire ba.. Zazzaɓine me zafin gaske ya rufeta alokaci guda..
Zaid kuwa yana fita daga cikin library ɗin direct wajen da motarsa ke fake ya nufa, buɗe murfin motar yayi, ya shiga ya zauna, kifa kansa yayi akan steering motar yana mejin zafi da raɗaɗi na ratsawa har cikin ƙwaƙwalwarsa, akaro nafarko daya yardarwa kansa cewa zai haƙura da Zahrah kenan, tabbas yazama dole ya yi haƙuri da ita koda kuwa hakan nanufin mutuwarsa ne, yau Zahrah da bakinta ta faɗa masa cewa tana da aure, maganar dayajita tamkar anwatsa masa tafasheshshen ruwan zafi, bayajin zai iya yin rayuwa idan babu Zahrah, amma kuma ayau yaɗaukarwa kansa alƙawarin cireta acikin zuciyarsa, duk da yasan hakan zai zamo kamar yaudaran kansa ne yakeyi, amma kuma dole zai jarraba….
Cikin matsanancin tashin hankali Dr.Sadeeq yadawo gida, yaje makarantar su Zahrah yanemeta sama da ƙasa bai ganta ba, gashi yaƙira wayarta bata ɗauka ba daya ƙara ƙiranta kuma yaji wayar akashe, hankalinsa atashe yake sosai, yana shigowa cikin ɗakin yadanna madannin ƙoyin wuta take haske ya gauraye gaba ɗaya ɗakin, wani irin ajiyar zuciyar dabai taɓa yin irinta ba ya sauƙe, haɗe da lumshe idanunsa, da sauri yaƙaraso gareta haɗe da sona ƙiran sunanta, jin shiru bata amsa saba yasanya yakai hanunsa jikinta, zafi zau yaji jikin nata, take tausayinta yakamasa, shidai yasan hakanan Zahrah bazata dawo gida bata jirasa yazo ya ɗauketa ba, sannan kuma haka nan bazata kashe wayarta ba. Zama yayi akan gadon haɗe da ɗagota ya kwantar da’ita ajikinsa. Mayafin dake jikinta ya zare haɗe da sanya hanu yashiga shafa kumatunta.
“Zahrah!” yakuma ƙiran sunanta cikin sassanyar murya.
“Na’am!” ta amsa masa cikin wata irin murya, dagaji kasan tanajin jiki.
Kanta yashiga shafawa ahankali, zuge mata zip ɗin rigar dake jikinta yayi, haɗe da cire rigar gaba ɗaya daga jikinta, kwantar da ita yayi akan gado, kana ya nufi wajen da ɗan ƙaramin drawer ɗinsa ke aje, maganin da zai sauƙar mata da zazzaɓi cikin gaggawa yaɗauko.
Dakansa ya lallaɓata tasha maganin, abun gwajinsa ya ɗauko yashiga gwadata, cutar dayaga tana damunta shiyayi matuƙar ɗaga masa hankali, wani irin zufane yashiga keto masa.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!!”
kawai yake ambata acikin zuciyarsa, duk sanyin A.C’n dake cikin ɗakin amma Dr.Sadeeq gumine ke tsastsafowa daga jikinsa.
“Taya akayi Zahrah takamu da wannan ciwon?” tambayar dayake tayi mawa kansa kenan…..
(????Wani ciwo mun banu????♀
Banyi editing ba idan kunga typing error kuyi haƙuri!)
Thursday 30/January/2020
Fatymasardauna
????????????????????????????????????????
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
*WATTPAD*
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
*CHAPTER 104*
Hanu yasanya akan goshinsa ya share zufan dake tsastsafo masa. Tashi yayi tsaye haɗe da tattara kayan aikin nasa ya ajiye a gefe. Direct bathroom ya shiga haɗe da sakar mawa kansa ruwa….
Tun shiga wankansa har kawo yanzu da ya fito yake shirya kansa tanajin sa,amma idanunta alumshe suke kamar meyin bacci.
Zama yayi akan gadon haɗe da ɗagota ya jawota zuwa jikinsa, kanta ya kwantar akan ƙirjinsa haɗe da soma shafa bayanta a hankali, still ɗaya hanunsa yasanya yana me shafa gashin kanta.
Cikin murya me ɗauke da nutsuwa ya soma cewa.
“Meyasa haka Zahrah? me yasa kika zaɓi ƙuntatawa kanki? tun bayauba nasha faɗa miki cewa ki daina yawan sanya kanki cikin damuwa, na faɗa miki kirage yawan tunani, har acikin zuciyata inamiki wani irin so wanda bansan iyakacinsa ba, bana so nagan ki cikin damuwa, ganin farincikin ki yafiyemin komai aduniyarnan, kinkuwa san meke damunki yanzu? damuwar da kike yawan sanya kanki aciki tahaifar miki da matsala wanda baikamata ace yarinya ƙarama kamarki tana ɗauke da wannan ciwonba, mekika nema kika rasa aduniyar nan? banaso ki ɓoyemin komai inaso kifaɗamin shin azamana dake ina cutar dake ne? ko kuwa inayi miki wani abu wanda ba kya so ne?”
Kanta tashiga girgizawa alamar “A’a” tuni hawaye sungama wanke mata fuska.
“To idan dai har hakane yakamata ki faɗamin damuwarki koda nima zanji sauƙi acikin zuciyata”
yafaɗi haka a gareta cikin tausasawa.
Kuka ta fashe dashi haɗe da sake rungumeshi cikin kukan tace.