NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Nakasa daurewa ne, nakasa daure zuciyata, idan dai yana cikin wannan duniyar bazai taɓa barina ba, bazai barni ba harsai yakasheni sannan zai huta, naso namanta dashi amma nakasa, bansan meyasa ba kullum zuciya ta me rauni take kasancewa akansa, dan Allah kayi haƙuri banfaɗi haka agareka don na ɓata ranka ba, kawai dai nafaɗi abun dake zuciyata ne!” taƙare maganar tana sheshsheƙan kuka..

Rumtse idanunsa yayi haɗe da cije laɓɓansa, dama yasani duk duniya damuwarta bazata wuce akansa bane yajima da sanin wannan. Ɗagota yayi daga jikinsa yazamana suna fuskantar juna. Cikin wata irin murya yace..

“Ba iya miji bane ni agareki, ni ɗan uwa ne wanda baki da kamarsa, najima da sanin cewa har yanzu Zaid yana cikin rayuwarki, nasan Inasonki so me tsanani, sai dai kuma duk irin soyayyar danakeyi miki Zaid yafini sonki, da ace zan iya to da najima da mallakawa Zaid ke amma bazan taɓa iyawa ba Zahrah nima masoyinki ne na haƙiƙa kamar yanda Zaid yakejin bazai iya rayuwa ba idan babuke, haka nima nakeji ajikina, batun yauba nasan Zaid yana nan kwance aƙasan zuciyarki, bana yaudaran kaina nakan faɗi abu ne aduk yanda natsaya na fahimceshi, koda kuwa abun dana faɗa bazasuyimin daɗin ji acikin kunnuwa naba, duk da kuwa nina faɗesu, bana ɓoye gaskiya saboda biyan buƙatar kaina”

Kafaɗunta yakama da duka hannayensa. Ci gaba yayi da cewa
“Yanzu zanyi miki magana ne a matsayina na mijinki kuma wanda yake sonki, har yanzu duk da na aureki kina aƙarƙashin ikona bazan taɓa takuramiki ba, inamatuƙar son farincikin ki, idan har kinaji ajikinki cewa bazaki iya rayuwa ba idan babu Zaid shikenan zan iya…..” rumtse idanunsa yayi da ƙarfi ya kasa ƙarasa maganar, da sauri ya miƙe yafice daga cikin ɗakin.

Zahrah wanda tun fara maganarsa tayi saroro tana kallonsa, tana ganin ficewarsa ta fashe da kuka.

“Me doctor yake shirin cewa? badai zai haƙura da ita ba?” tambayar da tayiwa kanta kenan, sam haka bazai taɓa yiwuwa ba, wace irin banzace ita? taya ya zata iya jure rashin masoyi kamar doctor Sadeeq? kuka tashiga rerawa me tsuma zuciya, kaiconta tunda dai harta bari Dr.Sadeeq ya iya sanin sirrin dake cikin zuciyarta, yanzu da wani idanu zata kalleshi bayan yasan cewa akwai son wani maƙare acikin zuciyarta? lallai koda ace Zaid ubantane yakamata tayi ƙoƙarin mantawa dashi….

Dr.Sadeeq kuwa yana fita daga ɗakin falo yanufa, yanazuwa ya buɗe fridge haɗe da ɗaukan goran ruwa yakafa a bakinsa, saida yasha ruwan fiye da rabin gora kafun ya kai goran ƙasa, ajiyar zuciya kawai yake sauƙewa akai akai.

“Meyake shirin aikatawa ne haka?” yatambayi kansa. Girgiza kansa yayi haɗe da ware idanunsa, idan yace zai iya rabuwa da Zahrah to yayi ƙarya, amma kuma idan yazamana bashine zaɓin ranta ba, to fa tabbas yazama dole ne yarabu da ita, badon kowaba saidon samun ingantaccen farincikinta, yasani shima abune me wahala ya iya jure rashinta, amma kuma itama yakamata aduba zuciyarta, yakamata tasamu abun da takeso.
key ɗin motarsa dake aje kan ɗan ƙaramin stull dake falon ya ɗauka haɗe da sakai yafice gaba ɗaya daga cikin falon, motarsa yashiga ya fice daga cikin gidan, bayajin zai iya zama acikin gidan gaba ɗaya zuciyarsa a dagule take..

Zahrah kuwa tanajin alamar fitansa daga cikin gidan tasake fashewa da kuka, duk da kuwa zafin zazzaɓin dake damunta. Kuka tayi sosai amaimakon zazzaɓin nata ya ragu sai gashi ya ƙara hawa, to taƙi tabar zuciya da ƙwaƙwalwanta su huta…


Da ƙyar ya iya kai kansa gida, tsabar yana acikin wani irin yanayi har idanunsa soma rufewa sukayi, yazamana duhu duhu kawai yake gani, hanunsa dafe da saitin zuciyarsa yafito daga cikin motar, taku biyu yayi duhu ya mamaye duka idanunsa take wani irin juwa ta ɗebesa saigashi yashe a ƙasa bayako da numfashi, da gudu ma aikatan gidan sukayo kansa suna ƙiran sunansa
“Oga! Oga!!”
Oga baimasan sunayi ba, wani daga cikin masu bawa flowers ruwa ne ya ranta aguje yaje yasanarwa Mummy dama Dad na nan atare suka fito amatuƙar ruɗe.

Ganin da suka mawa Zaid yashe a ƙasa yafi komai ɗaga musu hankali, da taimakon ma’aikatan wajen Dad yasanyasa amota direct suka wuce asibiti Mom sai kuka take.

Emergency aka karɓesa, Lallashin duniya Dad yayimawa Mom akan tayi shiru ta daina kuka amma taƙi, duk da cewa tana fushi dashi amma bata ƙaunar taga ko taji wani abu yasameshi, yanzu idan akace ya mutu yazatayi da rayuwarta?

Sama da 1 hour likitoti suka kwashe akansa suna bashi taimakon gaggawa. Ɗaya daga cikin likitotin ne ya kalli Dr.Bilal haɗe da ɗaga masa kai alamar wai Zaid ɗin babu rai ajikinsa. girgiza kai Dr.Bilal yayi alamar bai yarda cewa babu rai ajikin Zaid ɗin ba..

Hmmm likitotin nan sunsha matuƙar wahala kafun suka samu numfashin Zaid ya dawo dai-dai. Dukansu haka suka fito suna gumi domin kuwa da fari harsun cire rai dashi, sun ɗauka dagaske ya mutu.

Da gudu gudu sauri sauri Dad yataho wajen Doctor Bilal, hanun Dad Dr.Bilal yakama suka wuce office ɗinsa…..

“Yajikin nasa doctor? dan Allah kafaɗamin wani hali yake ciki a yanzun?” Dad yatambayi Dr.Bilal cikin yanayi na matuƙar ruɗewa.

“Ka kwantar da hankalinka Alhaji, yau Zaid ya hau matakin ƙarshe wanda da taimakon Allah muka samu da ƙyar muka shawo kan matsalan, amma bazan taɓa ɓoye maka ba idan har yasake shiga cikin yanayi irin wannan to fa tabbas wata ƙila saidai haƙuri, ba’aja da ikon Allah amma kuma fa da matuƙar wahala idan zai sakeyin numfashi, dama wannan shine matakin ƙarshe kuma gashi yakawosa idan irin haka tasake faruwa kuma to saidai dukanmu muyi haƙuri, haka Allah dama yake abunsa, duk wani me rai mamaci ne, koda ciwo ko babu ciwo, watarana dole mutum saiya mutu idan lokacinsa yazo, haka kuma gaba ɗaya zamu zama tarihi, saidai aba da labarin mu kamar yanda aka bamu na waƴanda suka shuɗe kafun zuwanmu iyaye da kakanninmu kenan!” Dr.Bilal yafaɗi haka yana me tattara nutsuwarsa ga Dad.

Gumi kawai Alhaji Ma’aruf ke sharewa sai ambatan
“Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!” yakeyi gaba ɗaya ji yayi duniyar tayi masa nauyi.

“Doctor menene mafita?” Dad yatambayi Dr.Bilal cikin sanyayewar guiwa.

“A yanzu kam dai bamu da mafita Alhaji Ma’aruf, sai dai mujira muga me Allah zaiyi, wataƙila Zaid zai iyakaiwa kwana uku batare daya farka ba, wataƙila kuma ko nanda kwana biyu ya farka, amma yazama dole ku kula dashi, yanzu bakamar da bane, yanzu abu kaɗan na ɓata masa rai zuciyarsa zata hau zafi, sannan kuma idan ya yawaita yin tunani to fa akwai babbar matsala, yazama dole ku tsaya akansa ku lura, akwai magungunan dazan rubuta muku, idan yatsaya akansu insha Allah zasu taimaka masa sosai.”

Sai alokacin Alhaji Ma’aruf ya ɗanji sanyi acikin ransa.

“Nagode ƙwarai Dr.Bilal kuma Insha ALLAH zamu kiyaye sosai!” Dad yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye. Musabaha sukayi da Dr.Bilal kafun ya fice acikin office ɗin.


A daddafe ta tashi tayi sallan isha. Tana kan sallayan bata tashiba yashigo cikin ɗakin, idanunta ta zuba masa, bada kayan da yafita ya dawo ba, yanzu rigane da wando na jeans ajikinsa, kallonsa takeyi kamar wani wanda bata taɓa ganinsa ba, shima kallonta yayi haɗe da yi mata murmushi, ya wuce cikin bathroom, mintuna kaɗan yafito daga cikin bathroom ɗin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button