SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

*Happy New Month*
Saturday 1/January/2020
*Fatymasardauna*
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
CHAPTER 105
ZAID
Kwanansa biyu acikin asibitin kafun ya samu ya dawo cikin hayyacinsa, sai dai kuma tunda ya dawo hayyacinsa baice da kowa komai ba, ko su Dad ɗinsa da sukeyi masa ya jiki, da kai kawai yake amsa musu, shikaɗai yasan meyakeji acikin jiki da zuciyarsa.
Zaune yake akan gadon asibitin yayi jigum, babu wani abu dake yi masa daɗi acikin duniya, Matakin daya ɗaukarwa zuciyarsa yayi masa tsauri sosai, a haƙiƙanin gaskiya yasan yaudaran kansa yake, cire soyayyar Zahrah acikin zuciyarsa, ba abu bane me sauƙi, yana sonta so sosai, so irin wanda ba a misaltashi, so ne dayakai ƙololuwa, ko ina acikin zuciyarsa tambarine na ƙaunarta, rumtse jajayen idanunsa yayi haɗe da sanya haƙuransa ya ciji laɓɓansa, dai dai lokacin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, ko kallon bakin ƙofar baiyi ba, balle yaga waye ne yashigo cikin ɗakin.
Turus haka Afrah taja ta tsaya tana me ƙaremasa kallo, mugun tsoronsa takeji, yanzuma Momynsa ce tace tazo ta duba ya jikin nasa shiyasa ta shigo, amma da bazata shigo ba. Karambani irin na Afrah yasanya taɗan matsa kusa dashi cikin murya me sanyi tace.
“My Dear yajikin naka?”
Da sauri ya buɗe jajayen idanunsa ya watsa mata su, take jikin Afrah ya soma rawa, tsananin tsanarta tahango acikin ƙwayar idanunsa, yanayin yanda taga idanunsa sunyi ja shi kaɗai ya isa firgita mutum, da sauri ta juya tafice a ɗakin, zuciyarta cike tab da sabon tsoronsa, gani take kamar zai tsaidata ya jibgeta, aitana tsintar kanta a wajen ɗakin tashiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai…
Shikuwa idanunsa ya maida ya rufe, wani irin ɗaci yakeji acikin maƙoshinsa, yayinda ransa yakai ƙololuwa wajen ɓaci, hakanan shikam Allah ya ɗaura masa tsanar yarinyar dako sunanta ma baisani ba, anzo anwani ƙaƙa ba masa ita amatsayin mata. “Shegiya me ƙananan idanu, daganinta munafukace” yafaɗi haka acikin zuciyarsa, jingina kansa yayi da bango, yaci gaba da tunanin yanda zai samawa rayuwarsa salama…
Gyara zama Husnah tayi haɗe da miƙa duk wata nutsuwarta ga Zahrah.
“Kina mamakina ko Husnah? nasan dole dama zakiyi mamaki, amma kuma idan kika yi tunani me kyau tawani wajen baizama abun mamaki ba”
Zahrah tafaɗi haka da iyaka gaskiyarta, saboda ita yanzu tama daina mamakin kanta kwata kwata.
“Dole ne zanyi mamakinki Zahrah, wani irin so ne haka kikeyiwa wanda ya tozarta rayuwarki? bazan tuna miki abun da Zaid yayi miki ba, saboda na tabbata har kikoma ga Allah bazaki daina jin ciwon abun da Zaid yayi miki acikin zuciyarki ba, a gaskiya bana ma tunanin kinacikin hankalinki Zahra, saboda baidace ace kina da aure akanki, kuma kina zancen wani daban ba mijin kiba”
Husnah tafaɗi haka cikin yanayi dake nuna ranta ya ɗan ɓaci da jin kalaman Zahrah.
Wani irin murmushi Zahrah tayi haɗe da sanya hanunta akan kafaɗan Husnah.
“Nasan dole zakiji haushina Husnah, amma kafun ke kiji haushina ninafara jin haushin kaina, ada nayi tunanin cewa banda hankaline, amma daga baya nagane cewa so so ne, kinsani nima kuma nasani so bayashawartarka kafun yashiga zuciyarka, so baruwansa da anzalunceka ko kuma kazalunta, shidai so so ne a kullum haka yake baya tambayarka shawara idan zai saka ka aikata wani abu, hakanan baya kuma sanjawa, shi ɗinne dai akullum akuma ko da yaushe yana nan, nasan Zaid yacutar dani, amma kuma ina matuƙar jin tausayinsa acikin zuciyata, tabbas da ace inada iko ko wani hali dana sanjawa Zaid rayuwarsa nasan Allah zai bani lada” Zahrah taƙare maganar tana me cije laɓɓanta.
Kallon baki da hankali Husnah tashigayiwa Zahrah.
“Ki sanja masa rayuwa fa kikace, anya kuwa kina cikin hankalinki Zahrah?” Husnah tafaɗa cike da mamaki.
“Inacikin hankalina Husnah ban haukace ba, ada nima nayi tunanin ko na haukace ne,sai kuma nagane bahaka bane” hanunta ta ɗaura akan hanun Husnah..
“Zaid bai taɓa tunanin haka zata kasance dashi ba Husnah, yayimini fyaɗe ne bisa bin umarnin zuciya dakuma gangar jikinsa da yayi, yamin fyaɗe ne saboda yanaji ajikinsa cewa sha’awata ce ke damunsa, Allah ba azzalumin kowa bane saidai wanda yazalunci kansa, ada nayi kuka sosai Husnah, nayi nadaman sanin Zaid acikin rayuwata, sannan kuma naji ƙunci da ciwon abun da ya aikata a gareni, ada inatunanin cewa fyaɗen da Zaid yayi mini yatashi abanza, saboda banida wani wanda zai tunkaresa, har yaƙwatarmin haƙƙina a wajensa…” ɗan tsagaitawa da maganar tayi haɗe da sakin wani murmushi, cigaba tayi da cewa.
“Nasani ko badaɗe ko bajima Allah zaimin sakayya, amma kuma bansan tawani hanya zai saka minba, ashe tahanyar da Zaid yabi ya yaudareni ta hanyar Allah zai sakamin, kinsan wace hanyace?” Zahrah ta tambayi Husnah.
Cike da zaƙuwa Husnah ta girgiza kanta alamar “A’a”
“SO! naso Zaid so me tsanani, shine namijin dana fara bawa soyayyata tunda nazo duniya, haka kuma shine namijin da na aminta dashi ɗari bisa ɗari, bantaɓa tunanin cewa ze iya rumtse idanunsa yaketamin haddina cikin rashin tausayi da imani, hadda wulaƙanci ba, nayi kuka harnagaji alokacin da Zaid ya lalatamin rayuwata, Zaid yayi amfani ne da soyayyar da nakeyi masa wajen cutar dani, Allah daya tashi sakamin Sai yasanya masa soyayyata me tsanani acikin zuciyarsa, yakuma nesantashi dani, tsananin soyayyar da Zaid kemin shine sakayyar da Allah yayimini, sannan kuma alhakina, na bibiyarsa sosai, Zaid yana sona, son da bazaiyi mishi amfani ba, nayi masa nisa tayanda bazai iya samuna ba, inada tabbacin cewa ayanzu yana cikin tsananin halin nadama wacce bazata amfaneshi da komai ba”
Ɗan numfasawa Zahrah tayi haɗe da duban Husnah.
“Kina ganin Zaid yacancanci samun mace mai hankali da nutsuwa, wacce zata gyara masa rayuwa ko a’a?” ta tambayi Husnah.
Harara Husnah ta wurga mata haɗe da taɓe bakinta…
“Mazinaci, fasiƙi, ɗan giya, ta’ina ya dace da mace me hankali da nutsuwa, ae sai dai ko yasamu wata daga cikin karuwan ƴan matansa ya aura, sai su ƙare rayuwarsu a haka, amma wace me hankalince zata yarda ta aureshi” Husnah tafaɗi haka da iyaka gaskiyarta.
Murmushi me ciwo Zahrah tayi haɗe da cije laɓɓanta, kanta ta girgiza kana tace….
“Zaid bai cancanci zama da karuwaba Husnah”
Dasauri Husnah takalleta haɗe da cewa.
“Meyasa kikace haka?”
“Sauyin rayuwa yake buƙata, dole yana da buƙatar wacce zata tsaya akansa ta basa kulawa, zuciyata tanayimini wani hasashe na daban” Zahrah tafaɗi haka tana me kafe Husnah da idanu.
Harara Husnah takuma wurgawa Zahrah haɗe da taɓe baki, cikin takaici tace.