NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Amma dai kinsan mazinaci sai mazinaciya ƴar uwarsa ko, taya zakina haɗa kamilar mace da wani taƙadarin ɗan iska Zaid, cab hmm gwamma ma kisake tunani, me kuma zuciyarki take hasasho miki akan sa?” Husnah ta kuma tambaya.

“Kece zaki iya Husnah, banda wata wacce ta wuceki, banda wata ƙawa sama dake,  amma bansan yazaki ɗau abun ba amma nasan…..”

“Mekike son cewane wai Zahrah? naga kinata wani kwalo kwalo, ki faɗi abun da kikeson faɗi kai tsaye” Husnah tafaɗi haka ta hanyar katse Zahrah daga maganganun da takeyi.

“Ke yakamata ki auri Zaid Husnah, ko saboda nima, zaki samu lada sosai ba ɗan kaɗan ba….”

Cikin tsananin mamaki Husnah tamiƙe tsaye daga zaunen da take, wani irin kallo tashiga yimawa Zahrah, cikin wata irin murya dake ɗauke da tsananin ɓacin rai da takaici tace.

“Ni” tanuna kanta da ɗan yatsarta. “Allah ya sauwaƙemin, bantaɓa tunanin zaki zomin da irin wannan zancen ba Zahrah, ashe dama bakyasona, bakya ƙaunata? nagode ƙwarai da kikanunamin hakan adai dai wannan gaɓan,   amma inaso kisani idan mafarki kikayi cewa ni Husnah na auri ɗangiya mazinaci to kigaggauta yin sadaka!”  taƙare maganar cike da ɓacin ran abun da Zahrah ta gaya mata…
Haka Husnah ta suri jakarta tayi tafiyarta Zahrah naƙiranta ko waiwayowa batayi ba, balle ta tsaya sake sauraranta.

Jingina bayanta tayi dajikin wata bishiya wanda suke zaune a ƙasanta,  wasu siraran hawayene suka gangaro takan kumatunta.

“Kowa kallon mahaukaciya yakeyi mata, to sai yaushene wasu mutanen zasu gaskata cewa soyayya ba ƙarya bane? sai yaushene wasu mutanen zasu gane cewa ita soyayya babu ruwanta da illa ko aibin mutum? menene laifinta don taji tausayin Zaid? So baƙarya bane, kuma duk inda so yake akwai tausayi, haka kuma akwai tsananin sha’awa.”     Ƙaran wayartane ya katse mata tunanin da takeyi,  dasauri ta share hawayenta haɗe da ɗaukar wayar takara akan kunnenta..

“To” kawai naji tace haɗe da jefa wayarta ta acikin jaka, tashi tayi daga inda take zaune haɗe da gyara mayafinta,   jakanta ta ɗauka ta nufi inda Dr.Sadeeq ke jiranta. 

 
Tun daga nesa daya hangota yaketa zuba murmushi, komai na Zahrah’nsa me kyaune, tafiyanta ma kaɗai abun ɗaukar hankali ne, duk da cewa ba dagangan take hakan ba, haka asalin takunta yake ɗauke da nutsuwa, bawai ita ta ƙirƙiri hakan saboda burgewa ba.

Buɗe murfin motar tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama,   lumshe idanunsa yayi haɗe da kamo hanunta yasanya acikin nasa hanun cike da nutsuwa yake murza ƴan yatsunta.

“Nayi missing wannan kyakkyawar matar, nayi missing wannan kyakkyawar fuskan, haka kuma nayi missing wannan daddaɗan jiki me laushin, nakumayi missing wannan tausassun laɓɓan masu daɗin sucking,  kuma ma nayi missing wasu abubuwana wanda suke sani nishaɗi sosai suke kuma..”  da sauri tasa hanu ta toshemasa baki haɗe da shagwaɓe masa fuska..

“Ni dai dan Allah kayi shiru!” tafaɗi haka a sangarce.

“Ni dai gaskiya naƙi wayon bazanyi shiru ba saina ƙarisa!”  yafaɗi haka cikin yanayi na  kwaikwayon maganarta.

Ɗan ɓata fuska tayi haɗe da sanya hanu ta shafi ɗakalallen cikinta. 

“Yunwa nakeji sosai fa, rabona da abinci tun breakfast”

Ɗan waro kyawawan idanunsa dake ɗaukar hankalinta waje yayi. 

“Meyasa kikeson barin kanki da yunwa ne? kinsan fa bazan yafe miki ba idan har kika cutarmin da unborn ɗina” yayi maganar yana me kafeta da idanunsa.

Zaro idanu Zahrah tayi haɗe da kai hanunta kan cikinta da sauri, ta shafa wai ko zataji tudu.

“Unborn fa kace? badai ajikina ba?” tayi tambayar cike da zaƙuwar jin amsarsa da alama taɗan tsorata da kalaman nasa.

“Yes Unborn ɗina dana sa miki daren jiya mana, banaso wani abu yasameshi seriously!”

Wani ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da jingina bayanta da jikin kujeran motar, gaba ɗaya ya faɗar mata da gaba.

“Ita da take tsananin tsoron haihuwa, tun yanzu yafara mata wani zancen unborn”   tafaɗi  haka acikin zuciyarta..

“Ya naga duk kin wani firgice ne haka, bakyason baby ne?” yatambayeta adai dai lokacin da yake tada motar.

“A’a”   kawai tafaɗa murya a sanyaye.  Baice da ita komaiba yaja motar suka fice daga cikin makarantar…

Direct wani hotel suka nufa don cin abinci, a cewarsa bazai iya haƙuri har sukoma gida batare da tasawa cikinta wani abuba.

Bata iya cin komai acikin hotel ɗin ba, sai pepper meat da kuma kunun aya kawai.. Koda suka koma gida tuni bacci ya cika idanunta, kwana biyunnan sosai take ebo gajiya amakaranta, da ta dawo kuma tayi wanka shikenan sai bacci.     Yaukam basu dawo da wuri ba sai gab da magriba, saboda haka bata ba bacci…    Wanka tayi da ruwan ɗumi take taji gajiyan yasauƙa daga jikinta..

“dogon wando na pencil jeans ta sanya ajikinta, sai kuma wata riga wacce tsayinta yakawo har gaba da guiwanta, gefe da gefen rigan atsage suke har wajen ciki, gaban rigar kuwa akwai aninaye masu kyau, rigace me kyau irin wacce ake ƙira da  shirt gown (my favorite)   sosai rigannan tayi mata kyau ajikinta yayinda hips ɗinta kuwa suka bayyana afili, kasan cewar rigar nada tsagu ta kowani ɓangare dama da hagu,  batayi ƙoƙarin kame dogon gashinta ba, tazura lufaya haɗe da hawa kan sallaya ta gabatar da sallan magriba.

Tana idar da sallan ta miƙe haɗe da fita zuwa falo.     Buɗe ƙofarta yayi daidai da shigowansa cikin falon, shima dawowarsa kenan daga masallaci.

“Waw!!!  Kinyi matuƙar yin kyau sosai fiye da kullum” yafaɗi haka  yana me ware mata duka hannayensa alamar tataho zuwa garesa..

Wani irin sanyin daɗi taji acikin zuciyarta lokacin da taji kalamansa, babu musu ta ƙarasa  garesa haɗe faɗawa cikin ƙirjinsa.

Kansa yaɗaura akan wuyanta haɗe da sanya harshensa yasoma yawo dashi yana lashe fatar wuyanta. Hanunsa ya ɗaura adai dai kan hips ɗinta,   cike da zolaya yace.
 
“Barin taɓa naji ko ciko akayi, anaso a yaudareni”

Dariya ne yakamata. Cewa tayi

“Allah ya sauwaƙe inyi cikon hips, taɓa da kyau kaji hips ɗina ne da Allah yaban bawai soso ba”

Shima dariya yayi haɗe da sake matseta acikin jikinsa.

“Nasani to ko kema kina ɗaya daga cikin mata masuyin cikon hips ɗin tunda ai naga mata sunayi sosai”

Da sauri ta ɗago ta kallesa lokaci guda ta ɓata fuska.

“Wato mata kake kallo sosai idan kafita ko? harkasan ana cikon hips, hmmm thank you”  tafaɗi haka tana me ƙoƙarin zare jikinta daga nashi..

Da sauri yasake matseta ajikinsa haɗe da tausasa muryarsa.

“Tuba nake madam, amma nisam mata basa gabana, inadake mezanyi da wata kuma daban, ke kaɗai ce kinkuma isheni,  amma kinsan ba abun mamaki bane dan nasan hakan, saboda  yanzu hakan ya yawaita sosai, wasu mata basa haƙuri da surar da Allah yayi musu, dole wai sai sunyi ciko, inakaranta labarai, ina kuma gani a Instagram,  amma kema kinsan baruwana da duk wata mace ina da me daɗina mezanyi da wata me ɗaci!”  yafaɗi haka cike dason shagwaɓata.

Aikuwa take ta hau dariya sosai taji daɗin kalamansa, amma kalman me ɗacin nan yabata dariya sosai, ko wace macece me ɗaci oho. 

(Please maza kuna faɗawa matayenku kalamai masu daɗi, koda ita ɗin bata da wani kyau, ka hure mata kunne kace ai ita kyakkyawace, wallahi zataji daɗi sosai, kai inda halima kadinga ƙiranta da sunan me daɗi????????wallahi yanzun sai gaka ranta yayi fari ƙal, kuma always zakaga tana cikin farinciki, wayyo wayaga anƙira su O’O da sunan me daɗi, ai nasan sai sunkusa sumewa saboda daɗi????????????)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button