SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Zama sukayi akan kujera haɗe da jawota ya ɗaurata akan cinyarsa, kansa yacusa acikin ƙirjinta, bayan ya ɓalle aninayen dake jere agaban rigarta, sosai ƙamshin dake fitowa acikin ƙirjinta yake yi masa daɗi, yanason ƙamshinta, domin kuwa yana sa masa nutsuwa sosai.
Lumshe idanunta tayi, tana mejin daɗin kissing ɗinta da yakeyi a ƙirjinta, hanunta ta sanya acikin gashin kansa tana yamutsawa a hankali. Ƙaran wayarsane yakaraɗe musu kunnuwansu, akasalance Dr.Sadeeq ya jawo wayartasa batare daya duba wanda ke ƙirannasa ba ya kara wayar akan kunnensa. Waro manyan manyan idanunsa waje yayi haɗe da cewa
“Dagaske kake?”
Banji me wanda yaƙirasa a wayar ya faɗa masa ba saiji nayi kawai yace
“Okay ganinan fitowa.”
Kallonsa Zahrah tayi, tanameson jin ƙarin bayani daga bakinsa.
“Lumshe mata idanunsa yayi haɗe da ɓuɗesu alokaci guda.
“Friends ɗinane sukamin surprise wai suna waje, banaje na shigo dasu, please mintina kisanja wannan kayan kinji, ina kishinki sosai banason kowa yakallemin ke!” yaƙare maganar yana wani lumshe idanu, domin kuwa cike yake da shauƙinta.
Murmushinta me kyau tayi masa haɗe da tashi daga kan cinyarsa tana cewa.
“Yanzu kuwa zan sanja kayan.”
Ɗaki ta wuce shikuma yayi waje don shigo da abokansa.
Zama tayi akan gado bayan ta sanja shigarta zuwa riga da sket na material marar nauyi takuma yane jikinta da mayafi, tanajin hayaniyansu acikin falon.
“Maza kenan wai nan su fa taɗi suke, amma kuma yawancin zancen nasu kama yake da musu” tafaɗi haka acikin zuciyarta. Bata ida zancen zucin da take ba, Dr.Sadeeq ya shigo cikin ɗakin.
Hanunta yakamo haɗe da kai mata sumbata a goshinta.
“Ko wani irin kaya kika sanya sai sunyi miki kyau, kyau ajininki yake ƴan mata na!” yafaɗi haka yana me ƙare mata kallo.
“Ƴan mata kuma?” ta tambayeshi tana ɗan murmushi.
“Eh mana ƴan matace ke a wajena ae har gobe, kuma ke sabuwace a wajena, tunda har yanzu bangama lashe zuma na ba” yafaɗi haka yana me kashe mata idanunsa ɗaya.
Kunyansane ya kamata, amma babu yanda ta iya shidai duk irin kalamansa kenan.
“Ki kawowa baƙinmu drinks kinji”
“To” Kawai tacemai.
A tare suka fita ita tayi hanyar kitchine shikuma yayi cikin falon..
Hanunta ɗauke da wani ɗan madaidaicin trey wanda ke ɗauke da kayan drinks da kuma ƴan madaidaitan glass cups tafito daga cikin kitchine ɗin, kanta aƙasa tanufo cikin falon saida takawo cikin falon kafun ta ɗago kanta fuskarta ɗauke da ɗan murmushi, wani irin bugawa taji zuciyarta tayi, lokaci guda idanunsu ya sauƙa acikin na juna, take ta saki trey ɗin dake hanunta yafaɗi ƙasa, ƙaran faɗuwarsa yajawo hankalin gaba ɗaya waƴanda suke cikin falon……
(????Waye Zahrah tagani????♀ badai Zaid bane yabiyota har cikin gida? kai ina ai Dr.Sadeeq yasan Zaid bazai barshi yashigomasa cikin gida ba, to waye ne wai??? ???? kutaimaka kufaɗamin waye, bazan iya jiran next page ba????????)
(Kuyi haƙuri dan Allah jiya banyi muku update ba????????)
Vote and Comment please my lovely fans????????
4/February/2020
Fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI!!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
CHAPTER 106
Da sauri Dr.Sadeeq yataso ya taho gareta, durƙusawa yayi yashiga tayata tattare wajen, saboda har wasu daga cikin cups ɗin dake kan tray ɗin sun face. Bisa tsautsayi ta zo ɗaukan wani fasashshen cup kwalba ya caketa a ƴar yatsar hanunta, take ta saki wani ɗan ƙaramin ƙara, cike da kulawa Dr.Sadeeq yace.
“I’am sorry kibi a hankali, muga hanun yayi jini ne?” yaƙare maganar yana me kama hanunta wanda kwalban yasoketa.
Murmushin ƙarfin hali tayi haɗe da cewa
“Yayi jini amma baso sai ba” hanunta Dr.Sadeeq yakama yashiga hura mata iskan bakinsa ahankali, yama manta da cewa basu kaɗai bane a cikin falon.
“Sannu amaryarmu, munsa kin yanke da ƙwalba ko, i’am really sorry” wani daga cikin abokan Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana ɗan murmushi.
Murmushi itama ta ƙaƙalo haɗe
da girgiza kanta, alamar
“bakomai”
“Tashi ki gaishesu sama sama ae duk sune silar jin ciwonki” Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me miƙar da ita tsaye.
Ɗan matsawa tayi wajen da suke zaune tashiga gaidasu cikin sassanyar murya, amma bata yarda ta kalli inda yake ba, shima kallo ɗaya yayi mata ya sadda kansa ƙasa, “Itaɗince dai duk da taƙara kyau hakan baihanasa ganeta ba” yafaɗi haka acikin zuciyarsa, zuciyarsa ne ke ingizasa daya ɗaga idanunsa ya kalleta, amma kuma yaƙi bin umarnin zuciyartasa saboda yasan hakan baidace ba.
Dr.Sadeeq dakansa yakawo musu wani drinks ɗin ita kuwa ta wuce ɗakinta..
Zama tayi akan gado haɗe da sauƙe wata irin ajiyar zuciya me ƙarfi, bazata taɓa manta wannan fuskarba, tabbas shine.
“To meya kawo JABEER gidanta kuma? kodai shima abokin doctor ɗin ne?”
tayi mawa kanta duka wa ƴannan tambayoyin, ganin da tayi cewa tunani bazai fishsheta bane, yasa ta miƙe ta ɗauko ɗan ƙaramin Al’Qur’ani’n ta tashiga karantawa a hankali…
Yanashigowa cikin ɗakin yajingina bayansa da jikin ƙofa haɗe da sauƙe ajiyar zuciya.
Kallonsa tayi haɗe da ɗan sakin murmushi.
“Yadai sai kace wanda yayi gudu?”
“laifine idan nayi gudu dan nazo naga matata?” shima yatambayeta yana me tsareta da idanunsa.
“A’a, amma ae abun bana gudu bane, tunda dai batashi sama zanyi ba inanan tare dakai” tafaɗi haka tana me gyara zamanta.
Takowa yayi yaƙaraso gareta, zama yayi gab da ita haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta.
“Ya hanun naki?” yatambaya yana me ƙoƙarin kamo hanun nata wanda taji ciwo dan ya duba.
“Da sauƙi bayama min zafi sosai”
Iskan bakinsa ya hura ahanun kafun yaɗago ya kalleta.
“Amma nayi mamaki ƙwarai da abun daya faru ɗazu, ko dai tuntuɓe kikaji ne?”
Da sauri ta shiga kaɗa kanta. “Bankula da gabana bane alokacin danake tafiya shine kawai na buge da kujera” batasan sanda ta mulmulo wannan ƙaryan ta rantaɓa masa ba.
Kansa ya jinjina haɗe da sanya hanunsa ya rungumota zuwa jikinsa.
“Nagodewa Allah ma dayasa bakece da kanki kika faɗi ba, tray ne kawai ya faɗi, da bansan inda zansa kaina ba” yafaɗi haka yana me shafa gashin kanta da hanunsa.
Ɗan shirune yashiga tsakaninsu kowannensu da abunda yake saƙawa acikin ransa, tabbas bazata iya haƙura ba sai ta tambayeshi waye Jabeer agareshi, to amma tace masa me? tace masa me ya haɗasa da Jabeer tsohon saurayinta ko kuma me? bari dai tayi masa wani wayon, tafaɗi haka acikin ranta…
Ɗan sake gyara zamanta tayi haɗe da cewa. “Amm wai duka waƴannan abokanka ne?”
Murmushi yayi batare daya ɗago ya kalleta ba yace “Eh”
Kanta ta jinjina haɗe da sake cewa “Dukansu fa nake nufi”